preview

3K 155 32
                                    

"Na riga da na gama magana kuma kin san idan nayi niyyan abu bani fasawa, SAUDAT zata dawo wurin Hajiyan mu ta zauna kuma ni zan dinga daukan gaba ɗaya ɗawainiyar ta, kada kiyi musu dani Sadiya domin matsawar ki a kan lamarin nan zai saka na ɗauki matakin da ba zaki ji daɗin shi ba kwata_kwata,

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Dago kanshi yayi yana kuka kaman ƙaramin yaro fuskan shi yayi caɓa_caɓa da hawaye yana ji a ranshi da ace ana canza gangar jiki da ruhi da kuwa ya canza nashi, ya kalli sulaiman dake zaune a kujera ya haɗe fuska domin yau NANA tayi matuƙar ɓata mishi rai har ya kasa tantance wani irin hukunci zaiyi mata,

Shirun da yaji yayi ne yasa yaci gaba da cewa
"Daman nasan tunda matsalar nan ya wuce tsakanin mu har ya fara bazuwa cikin dangi ƙarshe dole na tozarta, yanzu bayan Nana da Sulthana Allah kaɗai yasan yawan wanda suka san da wannan al'amarin"

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

"Sulaiman haka aka ce maka ake aure a yanzu ba zaka shawarci yarinya kaji ko tana son ka ko bata son ka ba kawai zaka tura a nema maka auren ta?"

Fuskar nan dai a haɗe kaman ko yaushe ko uwar tashi ma ba sararawa, cikin maganar shi da yafi kama da na umarni yace

"Hajiya a gani na hakan shine dai_dai saboda wannan yarinyar bata yi hankalin da har za'a nemi yardan ta ba kafin a yanke hukunci a kanta, ni naji ina son auren ta zan iya zama da ita saboda tana da nutsuwa sosai ba zan samu matsala wurin shawo kanta ba"

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Dariya ya sake yi wanda ya saka dimples dinshi lotsawa yace "ya nafi'u itace fa maganin matsala ta, itace maganin matsalar da nafi shekaru 25 ina fama dashi lokaci ɗaya tazo duk wasu damuwa ta ta yaye min su me zai saka na damu don ita BAZAWARA CE? abinda na sani kawai shine ZAYYAD yana son SAUDAT kuma ZAYYAD shi zai auri SAUDAT

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

"Haba abban Jannat, ka tsaya muyi magana mana don Allah baka ji ƙarshen bayani ba kawai ka ɗau zafi?

"Babu abinda zanji YUSRAH ai wannan ma maganar banza ce in dauko yarinya amana a maida ita kaman zanin sayarwa a kasuwa saboda rashin mutunci? Dan K.....🙊 Ubansu daga Sulaiman boss ɗin har Zayyad ɗin babu mai auren ta a cikin su idan sunga dama sai su kore ni a aiki mutanen banza kawai

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

"Baka isa ba wallahi, kayi kaɗan ka jawo mana tozarci da abin kunya Zayyad, kana saurayi sabo fill a laida ka rasa wanda zaka auro sai bazawara? Ai matsalar taka yanzu tayi maka maganin shi ko? To Allah ya bata lada amman ba zan lamunci wannan shashancin ba ko kusa"

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

"A duk lokacin da kazo da wani matsala naka nakan yi ƙoƙarin maida shi first priority na, ba zan huta ba har sai naga nayi maka maganin shi to yanzu lokaci ne da zaka biya ni wa'innan alkhairan da nayi maka, ka haƙura da boɗɗi ka fita daga rayuwar ta gaba ɗaya dan Allah Zayyad,

Waye zai zamo abokin rayuwar SAUDAT a cikin su?? Zabin ranta ko kuma wanda ya cancanta?

Ummu Najma ce 😘

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now