(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*11🧝🏻♀️
Na daɗe ina mafarkin sake sake ganin wannan abun sai yau Allah ya gwada min shi a zahiri kuma ina da yaƙinin wannan karon zan mallake shi insha Allah,Shiruu Sadiya tayi tana binshi da kallo haka kawai ta sami kalaman shi da ɗaure mata kai, don ta san Sulaiman is straight forward amman yau yana mata magana mai harshen damo lallai wannan al'amarin babba ne,
"Whaaatt?" Ya tambaye ta yana fitar da dariya mai sauti ganin yanda ta zurfafa kanta cikin tunani,
"Kinga ni bani son irin ɗaukan ɗumin nan naki kina shiga damuwa ba gaira ba dalili, ki kwantar da hankalinki ki koma kiyi barci wannan al'amarin bai shafe ki ba, Allah ya tashe mu lafiya" ya kashe lamp ɗin tare da juyar da ita ya lafe a jikin ta yana shafa bayan ta a hankali,Wannan sabon yanayi na Sulaiman ya ɗaure mata kai matuƙa, tana dai fatan ba wani abu yake shiryawa ba don haka kawai taji ranta bai aminta da shi ba,
*****
"Mtssww, ni zai kalla ya kira ni sitifid, wallahi duk ranar da na ganshi sai na rama wannan zagin, dama uwa na ko uba na ya zaga ba zan damu ba tunda wanda ya zagi iyayen wani iyayen shi ya zaga, amman tunda yace min sitifid babban zagin da yafi ko wanne a duniya to sai na rama"Ai kuwa ina kai aya abulkhairi ya callara ihu bayan ɗumbin kashedin da aunty Yusrah tayi mun na nabar ƙananun maganar da tun bayan magriba nake faman yi kada na tada mata yaro,
Tashi tayi ta zauna ta kunna Torchlight tare da kaimun duka a cinya daman already idanu na a buɗe suke tsugul na miƙe ina sosa wurin
"Muguwa! kina gani awa na biyu da yaron nan a hannu ina jijjiga shi kafin da ƙyar na samu yayi barci saboda nima na rintsa amman ko minti 30 baiyi ba kin daga min shi"Bance da ita komai ba don nasan nayi laifi, na zauna ina binta da ido ta ɗauki yaron ta fara feeding ɗinshi sannan taci gaba da cewa,
"Wai a dole muna kwana ɗaki ɗaya dan ki taimaka min da wasu abubuwa amman rana ta farko kin fara azabtar dani, haba da wanne ɗaya zanji?"Turo baki nayi ina ƙunƙuni, shiyasa ni banso kwanan ɗaki ɗaya tare da ita ba gwanda na kwana ni ɗaya yafi mun daɗi na faɗi abinda raina yake so a cikin barci ko a farke, amman ana niman takura min, kuma ma ai laifin Sitifid ɗin nan ne, yau nayi niyyan bazan ƙullaci kowa ba saboda kada nayi surutu cikin barci amman duk ya shiga ya ɓata min zuciya,
"Ke!!" Ta faɗa tare da taɓa ni, nayi saurin juyowa ina kallon ta tare da zare idanu na saboda yanda na ruɗa kaina bansan lokacin da nayi hakan ba,
"Boɗɗi lafiyan ki kuwa? Anya ke kaɗai ce? Maganganun me kike yi ne ke kuma ana miki magana hankalin ki yana wurin?"
"Babu komai aunty Yusrah me kika ce?"
Sauƙe numfashi tayi tace "ki zubo min ruwan zafi daga plask nasha"
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...