chapter 50

732 83 5
                                    


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
    💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

*Tunda na fara rubutun wannan book ɗin ban taɓa shiga farin ciki da jin daɗi irin na jiya ba💃💃😇🥳 lallai na yarda masoyi alkhairi ne a rayuwar mutum duk yanda yake🤩 saƙonni daga ko ina sai tuttuɗowa kawai suke😃 dukda dai wasu na rashin jin daɗin haɗin da akayi ne😩 har bacci ɓarawo ma da ƙyar ya samu ya ɗauke ni🥰 yanda kuka saka ni farinciki kuma Allah ya saka ku kwatankwacin shi😍😘*

50🧝🏻‍♀️
Inaso in hana shi, amman zuciyata tana ingiza ni, ina so na dakatar dashi na tuna masa irin wurin da muke amman shine mai controlling ɗina a yanzu, ya tafiyar da tunani na gaɓa ɗaya babu abinda nake gani a gaba na sai shi ina amsan saƙonnin da yake tura ma duka ilahirin jiki na.
Ban gane halin da muke ciki ba har saida Zayyad ya kusan kaiwa ƙasa ƙafafuwan shi sun kasa ɗaukan shi, jikin shi na son tuna mishi har yanzu shi mara lafiya ne bai gama warwarewa ba tukunna.

Saurin saka hannu nayi na riƙo shi ta taimakon ƙarfen jikin gadon da ya kama be kai ƙasa ba, na saka dukkan ƙarfi na don na taimaka mishi ya tashi dai_dai lokacin da aka fara knocking ƙofa.
A hakan dai na taimaka mishi ya koma gadon ya kwanta na gyara mishi kwanciya na rufe shi da duvet sannan maida ɗankwali da gyalena na ƙarasa jikin ƙofar na buɗe.

Fa'iza da Ruma ne rike da niƙi_niƙin basket na abinci sai Sulaiman biye dasu a baya. Hanya na basu suka shige ina musu sannu, alhajin na kwance kaman patient din tsakani da Allah ya saka fiskan tausayi kaman bashi bane ya gama murje ni yanzun nan ba.

Karɓan baskets ɗin nayi na ajiyesu a wurin da ya dace suka miƙo min ƴar ƙaramar jaka wanda kayan da zan sauya yake ciki.
Me suke nufi? Kwana suke so nayi a nan?.
Ban gwada reaction din komai a fuskana ba muka gaisa dasu saidai tun bayan kallo ɗaya da nayi ma Sulaiman ɗazu ban sake yarda mun haɗa ido dashi ba, bansan ma da wani ido zan kalle shi ba tsananin kunyar shi ya gama kama ni.
Kaina a ƙasa na tambayi Fa'iza "aunty Fa'iza ina aunty?"

Murmushi mai sauti tayi tace "ai yanzu na tashi daga kujeran aunty kin hau kin zauna, aunty kuma babban yaya ya tura ta gida sai gobe da safe zata dawo duba ku insha Allah, ina dai babu wani abinda kike buƙata?"

Girgiza kai nayi tare da faɗin "babu"
Idanun Sulaiman na kan Zayyad amman kunnuwan shi suna jiyo mishi sautin muryata sai ƙoƙarin yaƙi da zuciyar shi yake yi, 'yanzu ita matar ƙaninka ce, don't feel anything for her please' shine abinda yake faɗa ma kanshi.
"Inaso zamuyi magana dashi, give us privacy please" ya faɗa ba tare da ya juyo ya dube mu ba.

Hannu na su Ruma suka ja muka fita daga ɗakin sai murna takeyi na yanzu burinta ya cika na dawo cikin su dindindin.
Muna fita Sulaiman ya juyo wurin Zayyad da lokaci ɗaya ƙwalla ya cika a idanunn shi ƙiris suke jira su zubo don har can ƙasan zuciyan shi yake jin guilt ɗin abinda ya faru, yasan yayi ma Sulaiman maƙura na rashin adalci da bai iya danne zuciyan shi ya haƙura ya barshi ya auri boɗɗi ba, ya kasa controlling zuciyan shi ne duk yanda yaso yayi ƙoƙarin cire ta farat ɗaya ya gagara a maimakon haka ma sai koma baya da ya samu saboda tursasawan da yake yi ma zuciyan shi.
Gashi babban yaya ba tare da wani tunani ba yayi mishi sadaukarwan da harga Allah idan da shine ba lallai ya iya mishi ba.

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now