(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Masu iya magana sunce "don't judge a book by it's cover!" Ta yuyu ta sigar da ka fahimci abu bashi bane zahirin shi*💡
10🧝🏻♀️
Amman shekara ɗaya kawai kalli yanda ta ƙara girma tayi kyau? Naso na nimi wurin da take koda sau ɗaya ne na sake kallon ta amman ban san ta ina zan fara ba saboda bansan daga ina tazo ba, yau dai ba zan bari wannan daman ya wuce ni ba dole na san daga wani gida take kuma ita ƴar waye,Duk wannan saƙe_saƙe da yake yi cikin zuciyan shi yana tsaye ne wuri guda bai motsa ba, har ya juya zai koma cikin gida wani mutum ya ƙaraso gaban shi tare da durƙusawa kaɗan ya miƙa mishi wayan shi da ya manta cikin mota lokacin da yazo,
lokaci ɗaya annurin fudkar shi ta ɓace batt ya haɗe fuska ya fito a asalin babban yaya ɗinshi, sannan ya ƙara wayan a kunne tare da yin sallama, "i will be there in 10 minutes" kawai ya faɗa ya juya ya kama hanyar tafiya waje ranshi ba daɗi, amman idan yayi sauri maybe zai dawo ya same ta, ya faɗa tare da shiga mota suka bar haraban gidan,
Hmmm eviritim (everything) a gidan nan is fasfet (perfect), hankali na ya tafi kallon fasfet ban san har munzo jikin main door na part ɗin ba, hankalin aunty Nasreen bayi wuri na ita ta saka kanta a gaba a tunanin ta ina abin da ya kamata ne sai jina nayi dimm, na bugu da jikin mutum,
for a moment na tsaya ina tunanin anya wannan mace ce? A maimakon na kauce a hanyar ko na bada haƙuri amman ina tsaye ina tunani saida wani dogon tsakin da ya ja ya dawo dani cikin hayyaci na na ɗaga idanuna na zuba mishi,
Ya ƙanƙance idanu cikin masifa ga jiki na manne da nashi dan har yanzu ban tabbatar ko karo mukayi ba ballantana na san me zanyi gaba,
"Sh***t, who is this stupid girl? Ya tambaya a tsawace, ni dai banga kowa a wurin ba, bansan da wa yake magana ba, amman duk inda aka ambaci sitifid (stupid) na san zagi ne, wato zagi na yayi don kawai na bangaje shi ba tare da sani na ba? Dan cin mutunci ma zagin da turanci??
Saurin matsawa nayi daga jikin shi, yayi saurin wucewa tare da sake jan wani tsakin sannan ya juya ya tafi har ya shiga part ɗin dake gefen wanda zamu shiga ina kallon bayan shi, wannan wani irin zafin rai ne? Na tambayi kaina, shi wannan wani irin mutum ne mai tsanani sai kace wani mala'ika?
"Haba Saudat! Ina hankalin ki yake ne zaki jawo mana magana? Yanzu da ya dake ki fa yanda ranshi yake a bacen nan kuma baki iya bada haƙuri ba?"
"Tabɗijam, sitifid fa yace mun babban zagin da yafi ko wanne a duniya kuma kice na bashi haƙuri? Wallahi da saidai ya dake ni amman duk wanda yace min sitifid ba zan bashi haƙuri ba"
Girgiza kai kawai tayi muka sake kinkiman jakan kayan mu mukayi ciki dashi, babu kowa a parlorn bayan su biyu, sun lunƙuma cikin kujera ɗaya da laptop a cinyar ta tana nuna ma mai waya a hannu wani abu,
Sallamar da mukayi tare da niman wurin zama ne ya jawo hankalin ruma dake riƙe da laptop tana zaune kusa da zaytoon, da fara'a a fuskar su suka tarbe mu muka gaisa sannan Ruma ta nufi ɗakin Hajiya da niyan kira mana ita, Zaytoon kuma ta saka maids kawo mana abun sha,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficción General"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...