(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY*
*UMMU NAJMA**DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الَْأرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
(Bismillaahil-lazee laa yadurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem)
×3 da safe/×3 da yamma
(Three times)(Whoever recites it in the morning will not be afflicted by any calamity before evening, and whoever recites it in the evening will not be overtaken by any calamity before morning.)
07🧝🏻♀️Yana so na sosai bayi son ganin faɗuwa na, dukda nasan ko samin kason nawa nayi ba amfani zaiyi min ba saboda wannan matsalar amman zan jajirce naga na samu ko dan babban yaya yaji daɗi"
Sauƙe nannauyan ajiyar zuciya tayi cike da tausayin ɗanta tace
"Shikkenan Zayd, Allah ya kawo mana ƙarshen wannan al'amarin nan kusa, bari naje ko tea ne na kawo maka naga abincin da Ruma ta kawo maka da safe baka ci ba aka fita dashi"Tana faɗin haka ta ajiye waya da casbin ta a seat ɗin da ta tashi ta fice daga dakin,
Sunkuyar da kanshi yayi a yanda yake zaune an tokare bayan shi da filo ya haɗa kai da guiwa yana jin zafi sosai a zuciyar shi, rayuwar shi ɗaya take da mara amfani tunda bayi amfanan kowa da komai kullum wahala kawai ake yi dashi, harta hankalin wanda suke tare dashi ba a kwance bane kullum suna cikin fargaban ya shiga matsala, basu son ganin kukan shi amman shi ba zai iya hana su kuka ba,"Ya Allah kaine mai iko a kan kowa da komai ya Allah ka raba ni da matsalar da nake fama dashi, ya Allah ka yafe min kura kurai na ka sanya ni jin daɗin lahira idan duniya ba rabo na bace, ya Allah kaine mai iko akan dukkan komai, kai kake yin yanda kaso da kowa, ya Allah idan wannan matsalar itace jarabawata ka sauƙaƙamin kuma kasa na tsallake ta ya zul jalalu wal ikram" ya faɗa hawaye suna sauƙa daga idanun shi,
******
Da sallama ya shigo parlorn tare da wata mata a gefen shi tana ɗauke da yarinya a hannun ta da ba zata wuce shekara 2 ba, Ruma na hango su da sauri ta ajiye fork din hannun ta taje da gudu ta rungume matar kaman zata kaisu ƙasa,Da ƙyar ta samu tayi balancing kanta tana dariyan ƙarfin hali yarinya zata ɓarar da ita a gaban surakanan ta,
"Rumaisa wai yaushe zaki yi hankali ne? Baki ganin yarinya a hannun ta ne ba zaki ɗauka mata ita ba sai ki ƙara mata da nauyin ki?"
Lakutan hancin yarinyan tayi tace "wannan mai ƙyuyan ko nace zan ɗauke ta ba yarda zatayi ba ya Nafi'u, sannun ku da zuwa"Cikin girmamawa ta gaida su da kyar ta samu yarinyar hannun matar shi taje wurinta, suka ƙarasa gaban dining ɗin sukai squatting a ƙasa suna gaida Baba da Hajiya, ɗaya bayan ɗaya yaran dake zaune tare dasu suka fara gaida su yana amsawa tare da tsokanar su,
"Lafiya ƙlau aunty rasai" ya faɗa yana kallon Fa'iza da take faman ture turen baki don tasan wannan zuwan da suka kwaso zuga na tarban Zaytoon ne ita bata san wani dalili bane yasa kowa yake sonta ba kuma hakan na ɓata mata rai sosai, tafi so taga ko ina ana rashin mutunci ko kuma tsakanin mutane babu jituwa yanda zata samu ta caccaki kowa son ranta,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficción General"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...