(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*22🧝🏻♀️
Tunda Sulaiman ya faɗa ma Sadiya wa'innan kalaman hankalin ta ya kasa kwaciya ta rasa gane abinda yake nufi da Saudat zata dawo zama a gidan su har sai ta gaji da ganin ta kenan auro wannan yarinyar zaiyi??Tafi hour 1 tana tufka da warwara ta rasa wani hukunci ne ɗaya ya dace da abinda ya faɗa tunda a kaikaice yayi mata maganar ko dai ya faɗa ne don ya kawar da maganar da take mishi da kuma wanda take son isar mishi cikin hikima wato neman wasu kuɗaɗe daga gareshi a lokacin? Idan kuma da gaske yake fa yake?
Ganin ba zata samu amsan hakan ta hanyar tambayar kanta ba yasa ta ɗauki wayarta tana jin yanda ƴarta take zunduma ihu amma a yanzu bata da nutsuwan kulata, ƙarshe kiran nanny ɗinta tayi tazo ta ɗauke ta ita kuma taci gaba da trying numbern Sulaiman,
********
I was Shocked!! For a moment zuciyata ta kasa gaskata abinda idanuwa na suke gani har saida naga Zayyad yana buga jikin shi a jikin ƙafar Centre table wanda ko shi ba ƙaramin girgiza yake yi ba, jikin shi ya ƙame kaman mai farfaɗiya sai ihu yake yi abun gwanin tausayi,
Babban mutum magidanci, that kind and sweet Zayyad, my heart desire wanda a ko yaushe nake mafarkin kasancewa tare dashi shine a cikin wannan yanayin da ko ƙaramin yaro ba za'a so mishi ita ba?
"Rumaisa ina containern maganin shi da yake wurin ki? Ban samu nawa ba!" Shine maganar da ya fargar dani amman na kasa ayyana komai jiki na ya mutu ina tsaye a wurin Ruma ta koma ɗakin ta da gudu da nufin ɗaukowa Sulaiman kuma yana ƙoƙarin riƙe shi da duk wani ƙarfin shi amman ya kasa sai ji ma kanshi rauni yake yi a garin haka shima yaji masa ciwo a ƙafa, da kuma guiwan hannun shi,
Amman haka ya riƙe ɗan uwanshi ba tare da ya damu da halin da yake ciki na cutarwa ba dan basu iya controlling ɗinshi idan ba su uku shi da dady da Nafi'u ba, a hakan ma da ƙyar,
Fitowa riƙe da wannan dai farin ƙaramin containern Ruma tayi ta miƙa wa Aunty Amarya ita kuma ta buɗe ta mika ma sulaiman da nufin ya shafa mishi amman abin yayi mishi yawa ba zai iya ba, yana karba Zayyad yayi ball dashi wanda su kansu basu san ina ya shiga ba,
Zan iya taimakon shi, ina da sani a kan hakan amman ta yaya? Ta wani hanya zan taimake shi ba tare da mun aikata zunubi ba? Iyakacin ruƙiyya da na taɓa yi a rayuwata ma mata ne zallah, ta yaya zan iya haɗa jiki na da namiji da sunan nema mishi sauƙi daga wurin Allah?
Amman ganin idan na bar Zayyad a haka ba tare da nayi wani abu ba zai cutu yasa nayi shahadar ƙarasawa kusa dashi dukda tsoron shi ya kama ni amman a hakan na durƙusa na fara rero ƙira'a, saidai fa matsatstsakun kan bawan allan nan sai toshe kunne naga yana yi yana ƙoƙarin kawo min gwabza,
A taƙaice dai ruƙiyyan nan bai kammalu a haka ba saida babban Yaya ya riƙe min shi, na manna baki na a saitin kunnen shi ina karatu ina kuka irin wanda mahaifiyar shi take yi tana mishi addu'a,
Munji jiki kam babu ƙarya dan kunsan hidima da namiji kuma majiyin ƙarfi ga ƙarin wani ƙarfin na mutanen ɓoye dake jikin sa,
Allah ya yafe min ko dan tsarkakuwan niyya ta amman lokacin da yayi wani yunƙuri ya birkito ni ina jin yanda ƙirjin shi yake gogan nawa wasu sakwanni na tsohuwar ƴar hannu yana isa cikin jikina dukda shi baima san yayi hakan ba taimakon da Allah yayi min ɗaya bani azumi a ranar da shima ya kama hanyar garin su,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficción General"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...