chapter 2

1.2K 121 11
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

_no matter how smart you are, if you don't know how to work with people your dreams will only be dreams_💡

02🧝🏻‍♀️
"21,22...." "Kayan nan basuyi miki yawa ba Yusrah? Da wani nauyi ɗaya zaki ji, na cikin ki ko na uban zannuwan da kike ta loda?"

"Abban Jannat na faɗa maka na tura yaro ya tsaro mun napep ya kawo shi ƙofar gida sai ka ɗauka min ka saka min a ciki, 23,24,2..."

"To idan kika isa wurin da zaki je waye zai sauƙe miki?

"Shi mai keken mai yake yi? Zai sauƙe min mana ai har cikin gidan zamu shiga da shi, 25, 26, 27,28..."

"Yanzu idan kika kai musu zasu baki kuɗin ki duka, ko kuma a bashi zai ƙare?"

Shiru Yusrah tayi bata kula shi ba yaci gaba da cewa,
"Kuɗaɗen da yawa fah! Hajiya Sadiya matar Sulaiman boss ta baki sauran kuɗin ki na jiya?"

"Twenty nine, twenty ten..."

Dariya Khamis ya saka yana ci gaba da taya ta irgen shirmen da ta fara saboda yanda yake distracting ɗinta "twenty eleven, twenty twelve...

Ɗaya daga cikin zannuwan dake gabanta ta ɗaga ta jife shi dashi, ya caɓe yana dariya,
"Haba abban Jannat sau uku kenan kana ɓatar dani sai lokaci ya gama ƙurewa ban kai musu kayan nan ba idan kana wuri mutum ba zai taɓa ayyana abun arziƙi ba kenan?"

Dariya ya sake yi cikin nishaɗi yace "to ai baki gama bani amsa ta bane kin gwada fifiko ma kasuwancin ki a kaina"

Gyara zama tayi a kan kujerar da take ga cikin ta da ya fito zuƙeƙe aihuwa yau ko gobe tace "tambayi ina jinka"

Saida ya murmusa yace "yauwa nace idan kika kai ma masu wannan zannuwan kayan su zasu baki kuɗin ki a hannu ne ko kuma bashin ku na ƙarshen watan nan zasu ɗiba"

"Wannan ashobe ne ai sun riga da sun haɗa min kuɗin shi, kayan da na kai musu jiya ne sai watan azumi zan samu kuɗin su"

"Ok to balance ɗinki na wurin hajiya sadiya fa? Ta baki?"

"Tun da safe ta tura min dubu ɗari na cus a account jiyan ma wai ayyuka ne sukayi mata yawa bata da lokacin tsayawa tayi min transfer, kaima ka san wannan mutanen basu san karban bashi ba yanda suke da wannan ƙazamin dukiyar idan sukayi sai a tambaye su"

"Nice! To cikin 100k ɗinnan nawa ne naki a ciki?"

Kallon shi tayi a kaikaice tace "ban gane ba? Na taɓa tambayar ka nawa ne salaryn ka?"

"Idan ma baki taɓa tambaya na ba, ba a nan wurin nake zuwa dashi ayi budget ba? Kinsan komai ai"

"Wayo kake son min ko? Idan aka haɗa da wanda ta bani jiya ya zamo 150k riba na 35k"

"Wow! ga kuɗin da zaki karba idan kin kai wannan ga wanda zasu baki ƙarshen wata, idan aka tara gaba ɗaya ko wani month kina da kusan 70k fa kenan, baby kin kusa fina arziƙi ai" ya ƙarasa tare da taɓe baki yana jinjina kai indicating that he is impressed,

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now