(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Team sulaiman how market😝 sunfa dage suna caccakar babban yaya fah daga kawai an tambaye su ra'ayin su😒*
*naga sis Zaheera ma tace ita ma khamis taso a bada boɗɗi saboda Yusrah ta ɗanɗana kuɗan ta don ta gane namiji ba ɗan goyo bane har yanzu abun da tayi a matar kulle yana bata haushi🙄*
*Amman khamis ɗinmu ɗan goyo ne harma da zani😌 koya kuka ce😎*37🧝🏻♀️
Cikin abinda bai wuce sati biyu ba komai ya canza a tsakanin su idan kaga yanda suke mu'amalantar juna kaman ba ƴan uwa ba, babu jituwa sam yanzu a tsakanin su wanda har iyayen su suka shiga cikin maganar, anyi_anyi da ɗayan su ya faɗi abinda ya shiga tsakanin su haka amman kowa yaƙi faɗan komai daga ƙarshe nasiha kawai dady yayi musu ya ƙara nuna musu muhimmancin alaƙar dake tsakanin kada su yarda su bari wani abu ya shiga tsakani ya ruguza shi,Godiya sukayi, a gaban su sukayi sallama ma juna kowa fuskar shi ɗauke da fara'a kaman da gaske, dukda shi zayyad bai ɗauki abun can da zafi ba amman saboda zaɓin da ya bawa sulaiman na idan ya amince zai aure ta a matsayin bazawara zai bar mishi ita bai yarje mishi akan hakan ba yasa shima ya tirje kan koda ya yarda daga baya ba zai bar mishi ita ba,
Suna fita daga parlorn dady sulaiman ya zari tissue ya goge hannun sa saboda musabahan da sukayi a gaban iyayensu su, har yanzu yana ji a ranshi yaudaran shi zayyad yayi har yanzu yana danasanin alkawarin da yayi musu wanda yake ganin sakayyar sharri da yake masa a halin yanzu,
Kamfanin da suke tun da har zuwa yanzu suke samun duk wani rufin asiri daga gareshi ba nasu su kaɗai bane companyn haɗin guiwa ne amman mahaifin su alhj. Muhammad jibril yana da babban kaso a ciki, kusan 42% na abinda kamfanin ta ƙunsa duk nashi ne, saboda yafi kowa saka hannun jari lokacin da ake constructing ɗinshi,
Lokacin da girma ya kama shi a lokacin yaransa sun taso sun fara kawo ƙarfi hakan yasa suka haɗa meeting da share holders na kamfanin cewa yana son a kakkasa nashi kason ma ƴaƴan sa kuma suka yarda saboda nagarta da suka ga yaran suna dashi ta ɓangaren karatunsu da sauran al'amura na rayuwa amman sun ƙayyade cewa ba zasu bawa ko wani ɗaya daga cikin su ya wuce kaso goma ba saboda ba zasu yarda a karya alƙadarin kamfanin ba saboda sunyi imani cewa yaran basu san darajar shi ba don a sama suka same shi basu sha wahalar nima ba kuma har sai kowannen su ya kai shekaru 30 a lokacin ne suka san ciwon kansu da har zasu iya kula da wasu a ƙarƙashin su,
A kan wannan hukuncin aka tsaya, daga fari aka fara mallakawa sulaiman nashi Nafi'u ya biyo baya amman shi zayyad yana da matsalar makarai wanda suka shiga jikin shi tun yana shekaru 3 a duniya a cikin garden ɗin gidan su yana ƙwallo a lokacin almuru ana sallan magriba ya buge aljanu,
(a irin lokacin da ake so iyaye su killace ƴaƴayen su cikin ɗakunan su har zuwa lokacin da za'a kira sallan isha, harta jaririn da yake barci ba'a son barin shi a kwance saboda sheɗanu da suke sauƙowa a lokacin ana son uwa ta kasance tana karanta adduoi ma yaranta wanda suke da wayau kuma a koya musu sunayi don kariya daga sharrin sheɗanu da aljanu kada su shafe su,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...