(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Wannan shafin naku ne my Wattpad buddies 🤩🥰 ur comments are killing me ahswear😂 sometimes i wonder inda ace true life story ne babu Abinda zai hana ku zuwa wurin nan ayita ta ƙare na lura baku ɗaukan nonesense😅 you are doing a great job and i love it😍, keep the good work dearies😘😘😘😘*
40🧝🏻♀️
"Amman...Yaya akayi ka san iyaye na da wurin da suke zaune? Ko hamma zayyad ne ya faɗa maka?" Na tambaya idanu na a kan sulaiman,Kafin ya bani amsa Nafi'u ya amshe da "Ohh! Wato mu bamu kai a faɗa mana wani sirri ba sai amininki zayd ko....?"
Annurin fuskar shi ne ya kau da jin kalamin shi, har alaƙan dake tsakanin zayyad da Saudat yayi ƙwarin da mutane suka fahimta? In amintakan ne me yasa ba'ace tana yi dashi ba dhi da yake ɓata lokacin shi a kanta sai da zayyad?.
Murmushi nayi nace "ba haka bane dadyn Husna, kasan abu irin haka babu amfanin faɗan shi already na ɗaura muku nauyi ba zan so ƙara wani a kai ba"
"Hakane amman tunda bamu muka ce miki mun gaji ba bai kamata ki hana mu samun lada ba, you have already became part of our family mun ɗauke ki kaman yanda muka ɗauki su Nana, muna maraba da duk matsalolin ki ko damuwan ki kuma zamuyi ƙoƙarin magance miki su matuƙar baifi ƙarfin mu ba, so feel free daga ni har zayyad har ya sulaiman duk ɗaya ne kinji ko?"
Gyda kai nayi fuska na cike da annuri na fara surfo musu godiya su baba suna taya ni, har aka kira sallan magriba muna ɗakin ana basu asalin labarin abinda ya faru ba wanda suka samu daga bakin mutanen gari wanda aka sirka shi da ƙarya ba, kowa ya tofa albarkacin bakin shi daga ƙarshe amman kalmomin da sulaiman ya ambata basu fi a ƙirga da yatsun hannu ba suka tashi zasu tafi,
"Yanzu baba za'a sama muku wurin zama saboda ba zai yiwu dukkan ku kwana a nan ba saidai mutum ɗaya ya zauna a jikin inna"
"Eh akwai mai ɗakina daizo ya kwana a nan ɗin sai yayi mishi duk abinda ake so" cewar jaɗe
"Toh hakan yayi, ku gama shiryawa zuwa anjima zan turo driver yazo ya ɗauke ku sai ya kaiku masauƙin naku"
Takowa kusa da inda yake tsaye khamis yyi cikin girmamawa ya duƙar da kai yace "amma boss da ka barshi kawai ɗawainiyan zaiyi maka yawa ni zan tafi dasu nawa gidan su zauna"
"A'a ba za'ayi haka ba....ai da nasan zan barsu su takura ko kai na takuraka ne da ban ɗauko su munzo nan ba, za'a kaisu wurin da zasu sake insha Allahu, kada ka damu kanka"
Godiya muka sake mishi a karo na babu adadi sannan suka kama hanya harda khamis amman yusrah ma ta zauna tace sai zuwa jimawa itama zata tafi,
Suna fita sulaiman ya cilla key ɗin motan shi ma khamis ya shiga na Nafi'u ya zauna sannan suka ɗau hanya,
Sunyi nisa da tafiya ya ɗan juyo yana duban shi hankalin shi gaba ɗaya ya tattara jikin takarda da ya gani saman dashboard yana karanta abinda ya ƙunsa,
"Babban yaya" ya kira shi a taƙaice, da "uhmmm" ya amsa ba tare da ya juyo ba,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...