(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Alhamdulillah, bayan tsawon jira gashi na sake dawowa a karo na biyu😃 ina bawa masu karatu haqurin rashin jina kwana biyu da sukayi sakamakon ƙaddara data faɗo min har yayi sanadin rasa sim card ɗina sai kuma na ɗan jinkirta dawowa saboda azumin Ramadan. Amman yanzu zamu kammala littafin nan idan Allah yaso*
43🧝🏻♀️
Buge hannun ta nayi ina ƙara sautin kuka na, ta yaya za'a dake ni a hana ni kuka? Ni lokacin da yarima yake cin ubana a gidan ba suna gani suke kyalewa ba? Ko a cikin su akwai wanda ta taɓa yunqurin dakatar dashi? Saidai idan ya gama cin zalina goggo ta rarrashe ni amman duk yawansun nan taron yuyuyu ne babu wanda ya taɓa wani abun azo a gani akan komai dake faruwa a cikin gidan sai yanzu ne da suka ga babu sarki sai Allah wai zasu rusuna su fara roqona gafara?
To ba za'a yi haqurin ba!!Sake rarrafowa yadikon yarima tayi tana kuka kaman anyi ma kafiri mutuwa, ta ƙara danƙo kafana daga inda nake zaune tace
"Dan girman Allah boɗɗi kayi mana aikin gafara ka roƙi kaɗɗon nan ta rabu mana da mai gari ƙarami don ya Rashulullahi"Fisge ƙafana nayi daga riƙon ta na ɗaura daya kan ɗaya ina kuka tana kuka sauran mutan gidan ma suna tsaye suna kallon mu suna taryo duk abubuwan da ya faru dani a baya cikin kwaƙwalen su,
Kwanakin da nayi su mafiya wahala a cikin rayuwana ana treating ɗina kaman wata dabban jeji da bata da uban gida,
Babu wanda ya damu da kuka na, babu wanda ya damu da cina ko shana, azaban da yarima ya bani ko a gidan kaso ba za'ayi min shi ba, he and his family abuses me both physically and mentally.Zumɓur na miƙe kaman wanda aka razana sannan na dube su dukan su nace
"Yanzu dukkan ku kunyi ma kanku adalci? Bayan cusguna min da kukayi kuka maida ni abu marar ƴanci a baya, yanzu ma kuna son sake rabani da wani ɓari na farin cikin rayuwata?.
Kun manta lokacin da ake hankaɗo ni daga wancan ɗakin.." na faɗa ina nuna dakin da ya kasance nawa da yarima a da."... lokacin da ake duka na da sanda kaman jaka, haka zan wuni a kwance a ƙofar ɗakin can cikin jini bayan goggo dakan tallafe ni da abinci ko kallon banza babu wanda wani ko wata daga cikin ku yake jifa na dashi,
Dan Allah bakuji kunyar sake kallon cikin idanuna ba!!! Bakuji kunyar roƙona alfarma ba!!" Na ƙarasa cikin daga murya.Shiru ne ya ratsa wurin babu wanda yake da bakin ce min komai don fiye ma da abin da na faɗa ya faru, Ruma na ganin ba zata iya jurewa ba ta fice daga gidan gaba ɗaya tana kuka don ita a zaton ta abinda ya faru dani be kai haka ba,
fa'iza ne ta karaso kusa da inda nake zaune ta daura hannun ta saman kafada na tana lallashi na, cikin tausayawa ta riko hannu na ta dunkule cikin nata tace
"Ba halinki bane Saudat ke ɗin mai hakuri ce mai yafiya idan kina tuna baya rayuwar ki ta gaba ba zata yi inganci ba, learn to forgive... please..""Aunty fa'iza ganin dangin yarima sun wulakanta kaman yanda suka wulakanta nawa dangin shine kaɗai farinciki na, burina kenan guda ɗaya naga na kawo su ƙasa"
"Amman ba haka kuka yi da yaa Zayyad ba, ba wannan halin da mugun nufin kika gwada mishi ba, idan har kin ɗauke mu da daraja ki bar abinda ya wuce ya wuce, kema zaki samu Allah ya yafe miki laifukan da kikayi na rayuwan ki harma da wanda baki sani ba"
![](https://img.wattpad.com/cover/247603990-288-k80421.jpg)
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficção Geral"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...