(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*52🧝🏻♀️ (GRAND FINALE)
"You are not serious" na faɗa cikin fitar da sautin dariya tare da juyawa zan bar wurin, da azama Zayyad ya riƙo waist ɗina ya dawo dani jikinshi yana bina da wani irin kallo mai nuna shauƙi da tsaftacacciyar ƙauna, " then let me show you how unserious I am"
saurin dakatar dashi nayi ganin yana matso da fiskan shi kusa da nawa nace "babylove bamuyi sallan la'asar ba fah! And it's 5 already"Furzar da numfashi yayi yace "zamu haɗu ai bayan sallan la'asar ɗin, ina nan tare dake babu inda zanje and our honeymoon is starting today!" Yaja hannu na muka shige bedroom ɗinshi wanda ke ɗauke da bathroom a ciki mukayi alwala sannan mukayi sallah a tare sai ya sake fita parlourn saboda alluran da nurse zatayi mishi a lokacin.
Wurin akwai sanyi kaɗan amman ganin ruwan zafi available a heater yasa banji kyuyan wanka ba, a gaggauce nayi na fito har lokacin Zayyad bai dawo ciki ba.
Jakan kayana wanda su Ruma suka haɗa mana na buɗe ina duba kayan da zan saka, yawanci gowns ne irin na jikina sai atamfofi da laces suma basu fi a ƙirga ba sai jibgin ƙananun kaya.Hannu na nakai kan wata ƴar ficikar riga armless pink color mai shegen kyau amman ina mamakin yanda za'ayi wannan ɗan abun ya shiga jikin mutum mai girma kama na, sai da na ɗaga naga saman nada faɗi tsayi ne kawai bata dashi sai wani da zaka ƙulle rigan ta ƙasa ya zamo yana showing cibiyan ka.
Saka rigan nayi a jikina na ƙarasa gaban madubi ina kallon yanda ya amshi fatata kaman don ni akayi shi, haka kawai naji ina son in zauna dashi a jikina, na ɗauko leggings golden brown kalan adon dake gaban rigan na saka.
"Woww" shine abinda na furta lokacin da nake kallon kaina sama da ƙasa a mirror, Black scarf nayi ɗauri mai kyau dashi saboda almuru gudun aljanu.
Turare kawai na bulbula na saka takalmi da confidence ɗina na isa bakin ƙofar da zai sada mu da parlour sai kuma naji ruwan ciki na yana kaɗawa na gagara fita.
Zayyad mijina ne, ya kamata ina ado mai ɗaukan hankali don na burge shi amman kuma ban saba ba, ban taɓa yi ba koda a gidan aurena na farko sai inajin wani iri a jiki na.Sake tattaro dukkan ƙwarin guiwa na nayi na fita parlourn a tunanina zan iya samun su har yanzu a wurin amman shiru babu labarin kowanne daga cikinsu, leƙa ɗakin nurse ɗin nayi itama bata nan sai kawai na koma na ɗauki medicated glasses ɗina da pencil da paper na fita ta ƙofar baya wurinda ke a kewaye babu wani daga waje da zai iya hango wanda ke cikin wurin.
Takalman ƙafana na cire na zauna ɗan nesa da bakin ruwan ina zanen waves, iskan wurin mai ɗan ƙarfi haɗi da niima yana kaɗani har kusan 30 minutes Zayyad bai dawo ba, komawa ciki nayi na ɗauki wayana na kira shi saiga wayan shi na ringing a kujeran parlour hankali na ya kai maƙura wurin tashi, na Farko bayi da lafiya gashi bai faɗa min inda zaije ba kuma magriba ta gabato har yanzu bai dawo ba, ji nayi tsoron gidan ya kama ni gashi yunwa nake ji annan bani da nutsuwan cin abinci haka na koma bakin ruwan naci gaba da zama.
Daga nesa na hangota zaune ta haɗa kai da guiwa da ɗan ficilar riganta da yabar rabin bayanta a buɗe,
Ƙarasawa wurin yayi ya mata sallama saboda bata san da zuwan shi ba kada ta firgitaBan amsa sallaman ba sai miƙewa nayi a dame ina dube_dube a jikin shi kaman mai son gano wani abu.
"Babylove where have you been? Hankali na ya tashi sosai, da ka sanar dani katin ka fita Pleease! I was really worried"
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficción General"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...