(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Mrs Naseer, mrs abdulwahab, mrs S hapsy, mrs usman, mrs bash, and all other MRS's😂 wannan shafin taku ce tare da*
*Ummu hafsat & Hussaina mai jama'a*
Inayin ku sosai dearies, thanks for the love ❤️💙18🧝🏻♀️
Nafi 5 minutes riƙe da takardan na ƙura mishi idanu kafin da ƙyar na haɗa letters ɗin na farko cikin rawar murya nace
"He'a_da_ca_he, (headache)"Saida nayi shiru tare da jan dogon numfashi na furzar sannan naci gaba da karantowa,
"ji_na'echa_o_masti'a(gynaecomastia) di_arrrr_he'a (diarrhea)
To dai na ƙarshen yayi min kama da nonses (nausea)"Da ƙarfin guiwana na ɗago bayan na gama karantawa sai ji nayi an kifa min ranƙwashi sau biyu a jere zafin su har ƙwaƙwalwa na, na dago naga wannan zazzaɓin, babban yaya tsaye a kaina yanayin fuskar shi kaɗai ya isa ya nuna maka ɓacin ranshi ni ban ma san lokacin da ya shigo ba dan banji sallamar shi ba,
Hajiya kam, al'ajabi, mamaki, firgici da takaici ne suka hana ta magana, she can't believe mai shekaru irin nawa ƴar birni wanda kuma tana da tabbacin ina zuwa makaranta amman ban iya karatu ba,
"Meye wannan kike yi? Baki da hankali ne ko kuma ance miki ilimi abun wasa ne ko kuma ita ɗin sa'ar wasan ki ne da zaki saka ta a gaba kina mata wannan shirmen?"
Kasa kallon sulaiman nayi na sunkuyar da kaina hawaye na taruwa a idanuwa na,
"Baki ji ina miki magana ne da ba zaki amsa ni ba? Do you think it's funny?""Haba babana kabi mata a hankali mana, meye na fushi a nan ta yuyu bata iya karatun bane, a wani class kike Saudat?" Ta tambaya tana kallo na,
Hawayen da suka gama taruwa min ne suka samu daman ɗigowa a kan hannu na da na ƙudundune shi a tsakanin cinyoyi na, kusan duk haɗuwa na da Sulaiman sai ya saka ni kuka, ina ƙoƙari sosai wajen ganin na kai zuciyata nesa kada na tsane shi amman abu na niman faskara,
Cikin tsawa ya sake tambaya ta sai a sannan na basu amsa da "primary 4"
Zaro idanu yayi cike da mamaki yace "mene? Babba dake kina primary 4!!? What's your problem? ke wace irin daƙiƙiya ce wanda bata gane karatu as big as you are amman ace karanta simple abu baki iya ba?"
Ban san dalili ba amman abu kaɗan yana sosa min zuciya sosai, maganar da ya faɗa min ba ƙaramin taɓa min zuciya yayi ba na saka tafin hannuna na rufe fuska na hawayen dake ambaliya a idanu na suka jiƙa su,
"A wani dalili yasa har yanzu kike primary 4 kuma a wani makaranta kik.."
"Tashi ka fita a ɗakin nan Sulaiman"
Yaya zaka saka yarinya a gaba kana tozarta ta? Haka aka ce maka ake yi?"
Tashi yayi ranshi a bace wai yau shine da girman shi za'a yi wa faɗa saboda wata har a kore shi a wuri dan yayi scolding ɗinta,
Cike da taƙama ya nufi hanyar fita ina jin mummunan kallon da yake bina dashi a jiki na saida yazo daidai fita ɗakin sannan yace "stupid girl" ya fice, ban san lokacin da na fashe da kuka mai sauti ba shima yayi mun babban zagin nan,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...