(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*41🧝🏻♀️
Bai ankara ba sai ganin hawaye yayi zirr a idanunta abin har yaso bashi mamaki dukda yasan za'a rina, gimtse dariyar shi yayi ya ɗan karkace wuya yana kallon yanda ta haɗa kai da guiwa tana matsar ƙolla yace"Haba baby sady, keda nayi miki albishir ina tsammanin naga murnan ki kuma mai ya kawo kuka? Ko na ɓata miki rai ba tare da sani na bane?"
Wani ƙululun baƙin ciki ne taji ya tsaya mata a rai, koda asiri tayi ma Sulaiman yazo ya karye iyakacin wulaƙancin da zai mata kenan amman tun kafin ya ƙaro auren ya fara cin mutucinta ina ga idan yarinyar ta shigo gidan?
"Yi shiru mana sady baby....ni ba niyya ta na saka ki kuka ba....please ki share hawayen ki"
Banza tayi mai taci gaba da kukanta ƙofar da zai sadaka dq kitchen daga ɗakin yaje ya rufe kada ta jawo masa abin kunya ƴan aikinta su jiwo kukanta ya dawo wurin da take zaune yana ƙoƙarin ɗaga ta tare da bata haƙuri,
"Ka sake ni sulaiman!! Ta faɗa a tsawace sai kuma muryarta yayi can ƙasa a raunane take kallon cikin idanun shi da nata wanda ya sauya kala zuwa jaa, a hankali ta zare ɗankwalin kanta ta jefa shi a tsakar ɗakin kana ta saka bayan hannunta ta goge fuskar ta da maroon janbakinta ya jawu har kan kumatun ta lokaci ɗaya kamanninta ya canza ta fito kaman wata partial mahaukaciya saidai har yanzu ko gizau baiyi ba yana duƙe a wurin ya zuba mata na mujiya,
"Shikkenan ko hankalin ka ya kwanta?..... A haka kake son ganina ko sulaiman? na dawo kamar mahaukaciya saboda damuwa ko? Nifa matarka ce! Uwar ƴaƴanka ba wata maƙiyiyarka ba I'm not your enemy my love... Me yasa azabtar dani ya zamo maka hanyar samun nishaɗi, tunda ka fara nimqn aure wallahi na rasa nutsuwa ta, harfa wani rama nayi baka lura ba?" Ta ƙarasa tana fitar da nishi,
Ji yayi jikinsa yayi sanyi dan ya sani ta wani ɓangaren bai kyauta mata ba, Yana son sadiya har a yanzu saidai kawai irin zaman da sukayi na rashin tattali da damuwa da juna ne ya jawo ma soyayyar naƙasu, a hankali ya ɗaura lips ɗinshi saman nata da nufin tsayar da kukan nata tayi saurin kawar da kanta tana hararar shi,
"I'm useful only when it comes to having pleasure....a lokacin kawai nake da muhimmanci a gareka amman idan girmawawa tausayawa da kuma sauran jindaɗin rayuwar aure Saudat keda su, why?"
fitar numfashinsa kaɗai ya sanya nutsuwa a zuciyan ta dukda kuwa har yanzu tana cikin tashin hankali, Bai saurareta ba saida ya tabbatar ya gama kashe mata jiki luƙus ya sanya mata kasala
"Ban fifita sashe ɗaya akan ɗaya sashen ba saidai kowa ina bashi abinda yake so ne, bani keda laifin abinda ke faruwa ba halima"
"To wayene??!!" Ta tambaya da ƙarfi lokacin da ya kusa ƙulewa ciki, ɗaga kafaɗan shi kawai yayi alamun oho ba tare da ya juyo ba yayi tafiyan shi bata san lokacin da ta sulale a ƙasa ba tahau birgima tana kuka da ihu cikin tafasan zuciya,
"Wallahi saudat ta shigo gidan nan sai na kasheta kaji na rantse sulaiman gwanda ka rufa ma kanka asiri kada kayi biyu babu....
******
"Ko wani dare daku nake kwanciya na sake farkawa daku a cikin raina, ina cikin ni'imar rayuwa amman kullum hankalina bayi kwaciya idan na tuna halin da na barku a ciki an zalincemu ya aminu kuma wallahi ba zamu yafe ba sai mun ɗauki fansar azabtarwan da akayi mana mu da iyayen mu"
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...