chapter 4

840 110 3
                                        


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

_(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

*kada kana yanke hukunci a kan mutanen da baka da masaniya a kan manufar su, hakan zai sanya ka maida masoyin ka maƙiyin ka, life is too short ka zauna da kowa da kyakkyawar zuciya*

04🧝🏻‍♀️
A wannan tafiyar ni ba Yusrah bace

Sunana Saudat Habib wanda akewa laƙani da boɗɗi, ƴar asalin jihar Adamawa muna rayuwa a ƙauyen wuroɓokki nida iyaye na, a halin Yanzu shekaru na 15,

Anyi mun aure tun ina da shekaru 11 da rabi da Yarima babban ɗan mai gari wanda yake da shekaru 20, a wancan lokacin na kasance yarinya mai gata gaba da baya kasancewa ta mace mai cikakken asali an sanmu tun kakani kuma mahaifina ya kasance Malami kuma mai baɗa magani, bangaren kyawu da tsari saidai nace alhamdulillah domin dukda a lokacin ban cika mace ba amman Allah yayi min kyawun fuska shiyasa ma ake kira na boɗɗi wato kyakkyawa,

Wannan kyawun shi yayi destroying rayuwata, wannan kyawun shi ya zamo silar lalacewar farin ciki na da na iyaye na, saboda shi ya jawo ra'ayin Yarima gare ni ya sanar ma iyayen shi na yake so, as you know no body can say no to a prince,

A ƙauyen mu inada ƙawaye da yawa wa'inda muke fita siyar da nono wasu ƙauyukan dake maƙwaftar mu da kuma kasuwannin dake hanyar birni amman tun da nake ban taɓa shiga garin yola ba, babban ƙawata kuma itace furera, muna amintaka sosai don har talle tare muke fita da an ganni to anga furere shiyasa har sirrikan juna mun sani, na riga na san furere tana bala'in son yarima, kai ba ita kaɗai ba ma duk wasu ƴammatan ƙauyen masu ji da kyau da yarinta sun gama haukacewa a kanshi burin su bai wuce su zamo matar magajin mai gari ba, well nima harda ni a ciki inada wannan mafarkin, ai babu wanda yaƙi daɗi ko?

Wannan haukan da mata keyi a kanshi yana Yarima ya zamo mai tsananin girman kai ga tinƙaho, bayi da abokai saidai masu take masa baya harta tafiya a ɓokare yake yi ya wani turo ƙirji gaba yana fankama wai gashi wanda zai zama mai gari nan gaba, duk da mai gari ba adalin shugaba bane amman iskancin yarima da zalunci duk ya take nashi kuma ko sau ɗaya bai taɓa kwaban shi ba,

Idan yarima yazo wucewa a hanya ba ga yara ba, ba ga tsofaffi ba haka zaka ga kowa yana zubewa yana kwasan gaisuwa idan bakayi ba yayi maka mummunan hukunci kuma yasha bulus, amman duk da haka bai hana kwaɗayayyun ƴammata kai mishi buƙatun su da ya aure su ba dukda kowa yayi ma matan fulani shaidan kunya, amman da yawan su indirectly suke zuwa mishi,

Lokacin da Mai gari yace ma Yarima ya fitar da matar aure, yace duk duniya babu wanda yake so sai ni, a ranar daɗi naji kaman ya kashe ni, daga anyi maganar aure ma yarinya zata fara jin kunya amman murnan zan auri Yarima ya kasa ɓoyuwa dukda naga kaman iyaye na basu so ba amman babu yanda suka iya ya zamo musu dole su amince su bada ni,

Tun daga ranar mukayi hannun riga da Furera tun daga lokacin ƙiyayya mai tsanani ta shiga tsakanin mu amman ni ko a jiki na, indai zan auri Yarima komai ma ya faru, idan naje dandali kuwa kada kuga yanda ake koɗa ni ana wasa ni, tun kafin na auri yariman ma sun saka na fara jin kaina a sama nima yanzu na zamo wata, kuma da ikon Allah nida abin ƙaunata Yarima zamu mulki wuroɓokki bayan mahaifin shi ya sauƙa, bayan wata guda akayi mana baiko,

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now