(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*25🧝🏻♀️
22/Ramadan/1442
Yau da zazzafan ciwon kai na tashi domin tun jiya da Ruma ta kira tana kuka ta faɗa min jinnun Zayyad sun motsa na rasa sukuni don matsawa sukayi wai sai nazo,Da ƙyar muka shawo kan matsalar ta waya ina faɗa musu abinda zasuyi mishi, basu sani ba amman ni nasan nice sanadin hakan tunda ni na ɓata mishi rai,
Bazan so na shiga rayuwar bawan Allah bayan wahalan da yake ciki na ƙara mishi wani a kai ba,11:07am na fito da kwanukan da mukayi suhur dashi zan wanke dan tun a daren jiya na samu tsarki shiyasa dani akayi tahajjud, ban samu barci a daren jiya ba ko kaɗan shiyasa yau na makara,
A gaggauce na fara aiki na don na samu gamawa nayi wanka na tafi gidan mama kafin azahar tayi, kwankwasa ƙofar gate da akeyi ya jawo hankali na, na miƙe tare da shiga ciki na saka hijab akan pjamas ɗina sannan na fita duba mai knocking,
Tsananin mamaki na ya gaza ɓoyuwa yayin da idanuna sukayi tozali da aunty Amarya fuskar ta yayi fayauu kaman mara lafiya, kaman ko yaushe hannun ta ɗauke da casbi,
"Zan iya shigowa saudat?"
Tattaro nutsuwa na nayi, nayi saurin matsawa a hanyar don bata daman wucewa, murya na yana rawa nayi mata sannu da zuwa na shigar da ita parlor dan nasan tabbas a kan Zayyad tayi tattaki,
Gaisawa mukayi sannan na shiga na kira aunty Yusrah da yadiko suka fito suka gaisa sannan ta fara sanar damu abinda ya kawo ta,
"Ban sani ba ko kun samu labarin abinda yake faruwa da yarona daga wurin Saudat to shine abinda ya kawo ni nan nazo niman alfarman ki saudat....."
"babu wanda ya sani aunty, daga ni sai ku sai kuma Allah, ba zan faɗa ma kowa abinda na gani ba tare da izinin ku ba" nayi saurin katse ta kada ta sanar dasu,
Murmushin jin daɗi tayi tana ƙara yabawa da hankali na, bata yi tsammanin ba za'a samu matsala daga ɓangare na ba lokacin da na fahimci ciwon Zayyad amman gashi saima waraka da sauƙi da ake daɗa samu daga gareni, yarinya ƙarama amma akwai sanin yakamata, ta faɗa a zuciyar ta,
"Naji daɗi kuma na gode sosai saudat da kika mutunta mana sirrin mu kuma kika taya mu ɓoye shi, Allah yayi miki albarka" "ameen Aunty"
Ta maida dubanta wurin su yadiko da suke zaune "dan Allah idan ba zan takuraku ba, ina son ku ɗan bani aron Saudat in tafi da ita can gidan namu idan babu matsala, a halin yanzu wani ƙaramin matsala muke fuskanta a gidan, kuma saudat tana da daman magance mana wannan matsalar ko kuma ta sauƙaƙa shi, don Allah kui min wannan alfarmar ku ceci rayuwar wanda yake a halin gangara"
My words sounds like a puzzle to them, duk sun shiga ruɗani musamman yadiko, gwanda ita Yusrah ta san wani abu kaɗan akai, tana da yaƙinin maganar nan da akeyi a kan Zayyad ɗin nan ne dukda bata san komi gane da hakan ba, amman yadiko kam an saka kanta a baƙin laida,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficción General"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...