chapter 46

537 72 12
                                    


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
    💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: Polohttps://my.w.tt/4ZfEeBpVecbp
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

46🧝🏻‍♀️
Girgiza kai baba yayi da murmushi a kan fuskar shi, ba wanda yake nuna yana farinciki ba saidai mai nuna alama ta yana ganin mutuncin su dady amman ko kusa bai taɓa tsammanin mutane masu dattako irinsu zasu yi irin wannan tunanin har suzo su same shi a kan wannan maganar ba.
Haka iyaye suka zamo akan son zuciyan ƴaƴansu? Ba kunya ba tsoron Allah Kaman ba hausa Fulani ba!.

"Alhaji kiyi haƙuri amman gashkiya bazan amshi buƙatar ku ba badan wai na raina ku ko baku kai ku nemi wani abu a wuri na ba, amman Shaudatu yaro ne mai raunin gashke, a zahirin gaskiya ba zan iya washa da abinda ya shafi farincikin shi ba, don Allah ya bani irin wannan daman daga farko nayi wasa dashi wanda har hakan yayi sanadin zuwanta Wurin ku amman wancan ƙaddara ce, shaidai idan na kushkure na jawo abinda zai sake kawo mishi tsangwama da kyara a ƙarkarar nan to zai zamo sakaci"

"Na fahimce ka malam arɗo nima Saudat kama ƴa take a wuri na ba zanso ganinta ta shiga wani hali saboda wani na ƙyale ba ballantana kuma a sanadiyya na, amman dan Allah ka ƙara duba lamarin muma ba yana tafiya mana a yanda mukeso bane, ba zamu saka saudat yin Abinda bata so dole ba shiyasa suma na faɗa musu ra'ayinta za'a bi duk wanda tace tana so shi za'a bata si ɗaya ya janye"

Ƙara faɗaɗa murmushin shi malam arɗo yayi ya juya ya kalli khamis da yayi kicin_kicin ya haɗe rai don fin ƙarfi suka gwada mishi ƙarara amman da kafin azo nan duk ya gama cin ubansu an huta.

"Lalle kunyi min alkhairai da dama kuma zan kashance mai godiya a gareku har ƙarshen rayuwata, amman mutanen wannan ƙauyen bashu raina abinda zai jawo mutum ya zamo abun la'anta a wurin shu, shu gallaza ma rayuwar shi, boɗɗi shi shaida ne a kan hakan domin har rayuwan shi shuka sho ɗauka, bazan bari hakan ya shake faruwa da shi ba dan Allah kuyi haƙuri ku yafe min, amman wannan zancen a barta kawai"

With so much excitement khamis yayi tsugul yace "shikkenan ba za'a basu auren ba kenan? Dukkan su?"

"A'a khamishu, idan nayi haka ko ma kaina bayi adalci ba ballantana ma shaudatu ko su maneman nata, saidai zanso daƴa a cikin shu ta hakura tun yanzu, ko ita babban ta haƙura ta janye ko kuma ƙaramin ta haƙura".

Ya maida hankalin shi wurin dady sannan yaci gaba da cewa
"Alhaji da ace ba jini ɗaya suke ba koda sunfi biyu yawa zan basu duka ikon neman ta saboda bai saɓawa addini ba, amman yaya da ƙani ya saɓa ma al'adun mu, ban taɓa jin yanda akayi irin haka ba dan Allah kayi haƙuri kada a fara kafa tarihi damu, ni nayi alƙawarin wanda shaudatu ya gwada yana so a cikin su zan bashi ita ba tare da wani damuwa ba insha Allah"

Sam hakan baiyi ma khamis daɗi ba don har cikin zuciyansa baiso a bawa ko ɗaya daga cikin su Saudat ba don basu cancanta ba, amman tunda bashi keda hurumin nima mata miji ba zai bita da addu'a kawai yanzu dai ya riga da ya sauƙe nauyin amanar dake kanshi.

"In Allah ya yarda zanje na zaunar dasu mu yanke hukunci a tsakanin mu, nima na aminta da wannan shawaran da ka yanke don future'n Saudat ba abu ne da za'ayi wasa dashi ba, muna godiya da karamci da kuma dattako da kake nuna mana a ko wani lokaci, insha Allah zamu kama hanya yanzu kada dare yayi mana a hanya"

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now