(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*15🧝🏻♀️
Ji nayi kaman na nutse cikin ƙasa saboda kunya, na miƙe tsaye tare da fito da naman baki na da ban samu daman taunawa ba na zuba a cikin ƙaramin dustbin dake kitchen ɗin, yanayin fuska na yasa Zayyad yaji ba daɗi dukda photo na da ya ɗauka ba wai da nufin bazawa a duniya bane, haka kawai zuciyar shi ta raya mishi ya sake tsokana ta dan ya lura ni ɗin kaman ƴar rigima ce amman yaga alaman ba haka bane,Bani da saurin zuciya, idan nace zanyi wani abu ma na san ba iya karawa zanyi da Sitifid ba don tun jiya ya gwada min shi ɗin yafi ƙarfi na,
"Me kike yi a nan?"
Ya tambaya cikin sanyin murya da naji ya ratsa har ɓargo na, ban ɗago ba da yatsana na nuna mishi plate ɗin cake ɗin da nake ci,
Idon shi a kaina yace "baki magana ne? Ko Allah ya isana na jiya ne ya cinye miki bakin?"
Still ban tanka shi ba na ɗago idanuwa na na zuba su a cikin nashi ina ƙare masa cikakken kallo for the first time, for about 2 minutes muna kallon juna,
"Ba zaki faɗa min ba?"Ya faɗa ba tare da ya san maganar ta fito ba saboda wani yanayi da ya tsinci kansa lokaci ɗaya, ni na fara ɗauke idanu na sannan na sunkuyar da kaina ƙasa kafin nace
"Abinci nazo ci,
"Abinci da wannan lokacin?" Ya tambaya"Eh, yunwa nake ji"
Taɓe baki yayi tare da faɗin "ok" ya juya zai fita da sauri nasha gaban shi dan idan nace sunan shi zan kira bansan wanne ɗaya a ciki zan kira ba Zayyad ɗin ne ko Stipid,
"Dan Allah ka goge hoton nan filis"
Yatsina fuska yayi kaman bai gane abinda nake nufi ba yace "Wani hoto?"
Saida gaba na ya faɗi ganin yanda lokaci ɗaya yasha mur dukda basu kama da babban yaya ɗin nan amman a haka yayi kama dashi sosai, kallo ɗaya mutum zaiyi musu ya shiga taitayin sa, tattaro ƙarfin guiwa na nayi sannan na kalle shi cikin ido
"Na san ɗazun nan hoto na ka ɗauka amman dan Allah ka goge harda na jiya ma ba zan sake maka wani abu mara kyau ba"
"Oh ashe kin san babu kyau ɗin kika yi? Ke baki san rashin kunya ma babba laifi bane da kika saka ni a gaba kaman sa'an ki kina murguɗa min baki? Ai na riga na ɗauka dan haka babu gogewa wannan shine punishment ɗinki duk ranar da kika sake abu makamancin haka kuma sai na gwada ma yaran gidan nan kowa ya gani ke harda su hajiya ma sai na nuna musu"
Da faɗan haka ya raɓa ta gefe na zai wuce ai nayi saurin sake tare shi idanu na suna shirin zubda hawaye dan gani nake kaman yanzu ma idan ya fita da gaske nuna musun zaiyi, ai kuwa da na shiga uku musamman idan Nana taga hoton da ya ɗauka yanzu inaga kora na zasuyi da zagi daga gidan tunda abinda na ɗauka nake ci ma ban tambaya ba,
"Dan Allah kayi haƙuri ka goge wallahi bazan sake ba kaji na rantse maka"
Naɗe hannayen sa yayi saman ƙirjin sa yana bina da kallon ƙurilla sannan yace "Shikkenan naji zan goge amman bisa sharaɗin duk tambayar da nayi miki zaki bani amsan ta kin yarda?"
Da sauri na gyada mishi kai na zuba kunnuwa don sauraron wasu tambayoyi ne wannan,
"Menene sunan ki?"
"Saudat""Shekarun ki nawa?"
Sake kallon shi nayi da mamaki ina tambayan kaina wani irin tambaya ne wannan? Amfanin me sanin shekaru na zaiyi masa? Amman kuma ganin fuskan shi babu wasa yasa na bashi amsa da "15"
Haka yaci gaba da mun tambayoyi ina amsawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwata, ina ne unguwan ku...a wani makaranta kike....ajin ki nawa....ina ne ƙasar ki na aihuwa....iyayen ki suna raye... A taƙaice dai Zayyad yayi mun tambayoyi sunfi ashirin wanda ban san dalilin su ba,
yana gamawa ya ciro wayan shi daga aljihu ya goge a kan idona ina gani ya danna delete photon ya ɓace, but little did i know akwai foldern dake ajiye recently deleted messages a wayan shi wanda sai pic yayi 29 days idan bayi restoring ba sai yayi deleting permanently,
dan haka ya saka ma ranshi da ya bar nan zai maido da abinshi yaci gaba da kallo don yana da buƙata,
Juyawan da zaiyi ya hango ruma tsaye a bakin ƙofa tana faman zabga murmushi, shima baisan lokacin da murmushin ya suɓuce masa ba dan yana da tabbacin Ruma ta daɗe a tsaye daga yanayin tsayuwar da tayi,Ƙarasawa yayi yaja cheeks ɗinta sannan ya fita tana binshi da kallon tuhuma dan tana hango wani al'amari a cikin wannan murmushin da ya fita yana yi, ta ƙaraso wuri na ta ɗauka min plate ɗin cake ɗina sannan ta jani zuwa part ɗinsu dukda ban so shiga ba dan bani son sake haɗuwa da Sitifid,
Zama nayi a kan cushion seat na ɗakin ina jiranta ta shigo da glass cup da kwalin chivita ta ajiye mun a gaba na tare da jingina tana kallo na cike da sha'awa,
"Finally Allah ya kawo ma ya Zayyad matar aure, yau gani ga budurwan ya Zayd"
Duk da na lura a sigar wasa ta faɗa mun amman kuma kalmar BUDURWA da ta faɗa ya daga min hankali, wannan laƙani bani cikin masu mallakan shi, wannan suna yayi min nisa da HAR ABADA ba zai dawo mata ba, Yarima ya riga ya tarwatsa wannan ƙimar yayi mata tabo a zuciya wanda ba zai taɓa iya goguwa ba,
"Ke!!"
Ruma ta katse mata tunani tare da tafa hannunwan ta saman fuska ta don ta dawo da ni hayyaci na,Dagowa nayi a firgice ina ƙoƙarin sakin murmushin yaƙe bani son arin Ruma ta gane ina da wani damuwa har ta tambaye ni, don wannan sirri tawa ce da zuciya ta,
"Tunanin me kike yi ne ina ta magana baki ji?"
"Babu komai Rumaisa, me kike faɗa?"
"Cewa nayi yanzu sai mu san yanda za'ayi ki daidaita da ya Zayyad kinga sai ayi abun na wuri ba sai an ɓata lokaci ba tunda kema kamar na gida ne"
"Lallai fa Rumaisa, wa yace miki soyayya muke da kike maganar wani daidaitawa, daga kinga muna magana tare Shikkenan sai ki ɗauki wani tunani ki saka a ranki?"
"Look madam, idan ma baku yi ni zan saka ku fara because i want the two of you to be together, na san ba zan taɓa samun sister in law da zata kai ki ba wanda zata kula da yaya na tsakani da Allah kuma ta kula da matsalar shi"
Juyowa nayi ina kallon ta hannu na riƙe da handle ɗin ƙofar toilet da zan shiga,
"Wani matsala kuma Rumaisa? Ya Zayyad ɗin yana da wani matsala ne???*****
Me yasa yayi ma kanshi haka ne? Ya samu dama amman yayi wasa da damar shi, da ace ya saurara yaji address ɗin da ruma zata bashi da safe da a yau ɗin nan zai je ya fara fafutukar niman auren Saudat,Shi bai damu da yarintar ta ba, indai zata zamo mishi mata ta gari buƙatar shi ya biya, kuma yana da yaƙinin hakan don yarinyar akwai nutsuwa da kamun kai don duk haɗuwan da ya taɓa yi da ita cikin yanayi mai kyau take,....
Tunanin shi ne ya katse saboda ringing da wayar dake saman table ɗin shi yake yi,
Ganin sunan aunty amarya yasa yayi saurin picking tare da sallama,"Sulaiman kazo dan Allah, ZAYYAD!!.........🤦🏻♀️
Battery low😫
Sai yanzu na samu caji kuyi min afuwa😣*Ummu Najma ce 😘*
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...