(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*🌹🌹🌹FEEENERH MATAR SOJA 🌹🌹🌹
💃ina masoyan feenah matar soja marubuciyar ✍️✍️✍️✍️
HARAMTACCIYAR SOYAYYA
AURAN SOJA
YAYAN GATA
KUSKURENA
BARIKI AURAN SOJA
WANAKE AURE
😍wannan karonma ta dawo muku da sabon littafinta mai suna 👉 ZANYI BIYAYYA😌 ina masoya hausa novels toga dama ta samu littafin ZANYI BIYAYYA 😌 yaxo muke da solo 💃💃 daban daban
domin san ku fadakantu ,waaxantu dakuma nishadi ku biyota awannan shahararran littafinta ZANYI BIYYAYYA😌 masu iya magana nacewa anayi dakai yafi ba,ayi dakai karku bari abaku labari koda kudinka akace sai da rabanka🤸♀️🤸♀️🤸♀️🤸♀️🤸♀️gamasu bukatar biya ku hanxarta karku bari abaku labari kubiya ku karanta cikin Aminci, katin Airtel 200 zaku turo normal VIP 500 kuturo katinku ta wannan number 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 NAFISA SANI fcmb yan niger🇳🇪 masu bukatar biya kunemi wannan number +225 48 15 39 03
36🧝🏻♀️
Na gaji da sadaukar maka da abubuwa masu daraja don na lura kai ɗin BUTULU ne mai saurin manta alkhairi, ga fili ga mai doki idan ka isa kada ka fasa karawa dani a yaƙin niman soyayyar saudat, ni kuma zan manta duk wata alaƙar dake tsakanin mu na gwada maka isa ta...ba don wai muhimmancin ta ya kai hakan ba A'a sai dan na ɗanɗana maka zafin yaudara ta da kuka yi,"Koda ita ɗin BAZAWARA CE zaka nemi soyayyar ta a haka kuma ka aure ta?"
A firgice sulaiman ya juyo tare da ƙanƙance idanun sa yana watsa ma zayyad kallon tambaya don yaji maganar tashi tayi mishi nauyi ainun,
"Indai ka aminta ka yarda zaka aureta a hakan ni kuma nayi maka alƙawarin zan haƙura da Saudat, zan yayyafa ma zuciya na ruwan sanyi na bar maka ita""Bazawara kuma? Are You serious??"
"Ƙwarai kuwa! Saudat bazawara ne kuma da bakinta ta faɗamin haka nasan ba zata min ƙarya ba, akwai faɗi tashi da ƙunci a rayuwarta wanda kai baka sanda shi ba, sannan ita ba ƴar garin nan bane har yanzu dangin ta da iyayen da suka haife ta da kuma dangin tsohon mijinta suna ƙauye, kuma ita ba jinin su khamis bane, ceton ta yayi daga mummunar ƙaddarar dake bibiyar rayuwar ta ya kawo ta cikin garin yola"
Istigfari yayi a zuciyar shi lallai ya shiga sahun maciya amana tunda ya buɗe sirrin da ɗaiɗaiku kuma amintattu ne Saudat ta sanar dasu amman yaya ya iya! Nima ma kanshi mafita yake yi don ya san tabbas babban yaya yaji maganar nan ba zai yarda da wata alaƙa dake tsakanin su ba ma ballantana aje ga batun aure,
Kuma hakan ne ta faru, yana gama ji daga bakin zayd ɗin cikin tashin hankali, juyayi, kullewar kai da ruɗani ya faɗa mota a ɗari suka bar gidan, zayyad najin wani tuƙuƙin baƙin ciki a ranshi har numfashin sa yana sama, hannun shi na dama ya ɗaga ya ɗaura a kanshi da yaji kaman ana sarawa da adda a take ya yanki jiki ya faɗi!!
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...