chapter 39

443 77 7
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

39🧝🏻‍♀️
A kiɗime na juyo ina kallon shi don ban gane abinda suke nufi ba dukkan su, a dalilin me zaisa zayyad hana ni bin babban yaya? Kuma a kan waye sulaiman yake magana?

Sassauta murya nayi yanda sulaiman dake tsaye a jikin motar dake gaba na ba zai jiyo mu ba nace
"Hamma zayd bamu kaɗai zamu fita ba fah! Kuma baka san inane zamu je ba me yasa zaka ce kada na bishi?"

"Ok tun yanzu har zan fara jayayya dake?"

Irin tone ɗin da yayi amfani dashi wurin magana yafi kama da na babban yaya ba na zayd da na sani mai magana ko yaushe cikin sanyi da lallami ba, shiru nayi inajin wani iri na kasa komai ga sulaiman da ya tsare ni da idanuwa khamis yana jifa na da mugun kallo, ina taku ɗaya kaman a kunnen shi yace,

"Dan girman Allah boɗɗi kada ki bishi gani nan zuwa inda kuke, kada ki bari ya yaudare ki da kalaman shi ya sanya katanga a tsakan...."

"Mahaifiyarki zata gaji da jira Saudat, iyayen ki na tsumayen ganin ki kizo muje kiga halinda suke ciki"
Kalaman shi da naji dirin sauƙar su kenan cikin ƙwaƙwalwa da zuciyata,
A iya sanin da nayi wa babban yaya babu wasa ko ƙarya a tsakanin mu ko fuskar shi da mutanen da yake tare dasu kaɗai ya isa ya tabbatar min da gaskiyar zancen shi,

Wasu hawaye masu sanyi ne naji sun fara bin kunci na, ban gansu ba amman har naji sanyin ciwon dake cin zuciya ta tsawon shekaru sama da 5, disconnecting kiran nayi ba tare da na sani ba da gudu na nufi motar da naga aunty yusrah a ciki na shiga muka ɗau hanya,

Fakan idon ya Nafi'u wanda Jannat ta saka a gaba da surutu tayi ta Mintsile ni a cinya tana harara na,
"Kina son ku saka ƙafar wando ɗaya da abban jannat ko? Ana miki magana kin tsaya kina shiririta ma mutane sanin kanki ne bayi son rawan kai tun kafin ya saɓa miki ki shiga hankalin ki"

Maganar ta ya shiga kunne na amman banji abinda ta faɗa ba, my mind was absent ganin abunda ke faruwa yau ɗin nayi kaman a mafarki,
kwantar da kaina nayi a saman kafaɗar ta da hannu na zagaye kunkumin ta na rungume ta sannan na saki kuka mai zafi koda zanji sauƙin abinda yake taso min,

Bubbuga baya na takeyi a hankali cikin sigar lallashi ya Nafi'u ya miƙo mata kwalin tissue ɗungurungum tana share hawayen fuska na dashi, ni kuwa ji nakeyi kaman na ƙwace tuƙin motan daga wurin shi don gudun da muke surfawa a titi bayi min sauri babban buri na a yanzu kawai na ganni a gaban Inna ta da baba na,

A maimakon mu ɗauki hanyar wuroɓokki sai naga munyi parking a ƙofar asibiti, rasss naji ƙirjina ya buga ganin suna fita daga cikin motar babban yaya har ya nufi cikin asibitin, hakan kenan na nufin babu lafiya, wani nawa yana cikin matsala,

Ganin bani da niyyan motsawa yasa yusrah taja hannu na muka fita, a hankali take tafiya ina biye da ita a baya zuciyana yana bugun uku_uku baki na ɗauke da kalolin salati har muka isa room 6 ya saka kai ya buɗe sannan ya tsaya a jikin ƙofar yana kallo na,

Zaune take a saman gadon anyi mata matashi da pillow ta jingina bayan ta da jikin gadon, inna ta ƙara tsufa sosai a cikin shekaru 5 kacal saboda wahala da damuwa da har wrinkles sun fara bayyana saman fatar ta, ji nayi zuciyata ta karye lokacin da na saka idanu na cikin nata, kallo ɗaya zakayi mata kasan har yanzu tana jinjiki amman hakan bai hana ta sakin murmushin da na ɗauki tsawon lokaci ban ganshi ba cikin sassarfa na ƙarasa wurinta sannan na zuba a kan guiwa na tare da kifa kaina a kan cinyar ta na shiga rero kuka mai tsuma zuciya,

Babu wanda yayi ƙoƙarin rarrashina don a yanzu kukan shine mafi a'ala domin zai rage min wani abu daga ƙuncin dake zuciyata, munfi 4 minutes a haka wurin ya ɗauki shiru sai sautin kuka na kawai dake tashi, da ƙyar inna ta iya ɗaga hannun ta saboda nauyin da zuciyarta tayi ta ɗaura shi a kaina,

"Tashi boɗɗi am, innar ka tana lafiya ka daina kuka babu abinda ya same mu" shine kalaman da ta dinga maimaitawa har na rarrashi kaina na ɗago ina sake ƙare ma fuskarta kallo, she is my first love, mutum na farko da ta yarda dani sama da kowa dukda a lokacin bata nuna ba,

Hannayen ta na ɗago cikin nawa ina sumbatar su tare da sakin murmushi mai haɗe da kuka abun sai ya bata kunya ta juyar da kanta tana son ƙwace hannun ta amman naƙi bata daman hakan, ni yanzu ban damu ba zanyi ƙoƙarin nunawa iyayena soyayya domin a yanzu niba boɗɗin wuroɓokki matar Yarima bace, yanzu na waye a kan addini kawai nake tafiya babu ruwana da al'ada mai tsanani NO MORE GIDADANCI!

"Ayyo boɗɗi innar ka kawai ka gani ko?"

Zumɓul na miƙe ina dariya mai sauti yayin da idanuna suka sauƙa kan mahaifi na amman har yanzu basu daina zubar da hawaye ba, da gudu naje na shige jikin shi tare da ƙanƙame shi tsamm a jiki na har yanzu dai babu ma wanda nayi magana,

Tsilli_tsilli yake yi da idanu yana kallon dukka mutanen ɗakin tare da ƙoƙarin ɓanɓare ni daga jikin shi amman naƙiya, kunya yaji ya kama shi kaman ya nutse a ƙasa da ace a ƙauye ne hakan ya faru ai sai yayi sati bai haɗa idanu da mutan gari ba, saida na gaji dan kaina na sake shi juyawan da zanyi nayi tozali da ya Aminu tsaye a gefen Jaɗe, duk cikin su shi kaɗai ne sanye da kayan birni T shirt da wando,

Toshe baki na nayi cike da tsananin mamaki don a lokacin ji nayi kaman na kurma ihu saboda daɗi,
"Hamma Aminu kaine??"

Sassanyar murmushi yayi tare da gyada kai yace
"Nine boɗɗin baba kina lafiya ko?"

Ban iya bashi amsa ba na shiga jikin shi da gudu ina sake tambayar shi
"Ya aminu kaine?"

Khamis, yusrah da Nafi'u dai suna tsaye ne suna ƙare mana kallo cike da sha'awa ba'a batun babban yaya da bakin shi ya kusan taɓa kunne yana kwatatanta farincikin da nake ji a cikin zuciyan shi ko a yanzu buƙatar shi ya biya,

Bayan an gama gaishe_gaishe na sake komawa jikin babana lafe ina bin kowa da kallo cike da sha'awa, ɗan ture ni yayi yana karkaɗe min jiki na wai kada na shafe su jiki na ya ɗauki datti, rufe idanu na nayi ma kaman ban jishi ba domin idan da za'a tara duk arzikin duniyar nan a bani ba zasu kaisu cikin rayuwata ba,

"A gashkiya bani da abinda zan shaka miki dashi kamishu, kin riƙe mana amana sakani do Allah, mun gode Allah ya saka miki da mahihicin alkhairi ya saka ki gama da duniya lahiya"

Lumshe idanu yayi saboda jin daɗin addu'ar da kuma farincikin sauƙe nauyin da aka ɗaura mishi na shekaru yace
"Ameen baba, kun riga da kun gama biya na domin ba don kaiba da yanzu bani tare da iyalina ko bani cikin duniyar ma gaba ɗaya, saidai kuma rabin ɗawainiyar Saudat ga wanda ya ɗauke shi" ya ƙarasa yana nuna sulaiman,

"Duk wani canji da kuka gani a tattare da ita yana cikin wanda sukayi fafutukar kawo mata  shi, ya bada gudunmawa sosai a cikin rayuwar ta ba tare da an roƙe shi ko an saka shi dole ba"

Sulaiman dai yana tsaye kanshi a ƙasa yana yaƙe, haka kawai yake jin ransa fari tass shima gashi yau ya saka mutane farinciki yana jin sautin dariyan su a saboda shi,
Haɗe hannuwan shi baba yayi yana shirin sauƙa ƙasa sulaiman yayi saurin taro shi yana girgiza kai,

"A'a baba, dan Allah kada ka saka shaiɗan ya shigo cikin tarayyan mu na alkhairi, aci gaba dayi mana addu'a kawai"

Kallon shi kawai nake ina mamaki, sai yanzu na fahimci duk alkhairin da yake faruwa dani gaba ɗaya aikin babban yaya ne, wannan wani irin mutum ne? Wani irin zuciya sulaiman yake dashi da bata gajiya da aikata alkhairi da kyautatawa?

Babu wani kyakkyawan fahimta tsakani na dashi amman yana ta hidima dani babu gajiyawa, duk wasu buƙatuna na rayuwa ya biya min su ba tare da na faɗe su ba, dame zan biya shi???

_amman kuna ganin abubuwan da sulaiman yake yi ma saudat tsakani da Allah ne kuwa??_

*Ayi manage, kada dai a jini shiru ne yasa nayi wannan zuwa gobe zamuyi mai tsayi insha Allah*

Ummu Najma ce 😘

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now