12&13

22 2 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira7531

        🅿️.......12&13

Ganin halin dana shiga zai iya saka aganoni, shiyasa nayi iyakar kokarina wajen ganin na dawo cikin natsuwata, ina nan kwance salma tashigo tana wani taunar cingam cikin yatsina fusma, mamaki nake yadda salma ta canza sosai daga dawowar su yah Aree zuwa yanzu, kokadan yanzu salma bata damu da damuwata ba, sai gari ya waye har rana ta koma ga ubangiji, salma ko kallon banza ban isheta ba, idan ma ni nayi mata magana baza ta kallan ba zata ban ansa, tabbas ina hasashen wani Abu dangane da ita,  salma ba haka take ba inson sanin dalilin canzawarta.

Wayarta ta ajiye ta shiga wanka ta fito tahau shirin bacci, Amman sai ka d'auka miji gareta sai kwalliya take yi, tana ta feshe jikinta da turaruka, kallon ta nake ina mamakinta.

Har ta gama bata cemun uffan ba, saida zata fita har takai kofa ta juyo cikin rainin hankali tace,

"Oh na manta fah kifito can babban falon Abbu ana nemanki."

Ta juya bin bayanta nayi da kallo kafin na yuk'ura na tashi, sake wanke fuskata nayi nafito, tabbas nasan wannan maganarce za,ai gaba na yana fad'uwa na isa kowa nanan har dadyn yah meenah, dasu Anni da yah jahid kowa dai yana nan banda yah shahid da sai karshen wata zaizo hutun karshen shekara.

Zama nayi can gefe bakin kofa, saboda irin kallon k'ask'ancin da yayi min muna had'a ido, bacin tsoronsa da yacika zuciyata ai dana rama.

Yah jahid ne ya bude mana taro da addua,kafin kowa ya shafa muka maida hankalinmu kan Abbu, gyaran murya yayi ya fara da cewa.

"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata,ala da yanuna mana wannan rana,  ya kuma nuna mana girmanku, Wanda da ba haka kuke ba, an wayi gari kowa ya mallaki hankalin kanshi, zuwa wannan lokacin nasan wasu daga cikinku kanku yatoshe, abisa wasu al, amurrah watau abunda kefaruwa shine, azahirin gaskiya Yayanku areef ba mune muka haifeshi ba, bamune mukashayar dashiba, saidai kuma mune iyayen rikonsa, konace ahalin yanzu dai Areef namune, watau Abunda ya kawo wanan magana shine babu batun b'oye b'oye, Areef kanwarka khairat tataso tun bata san kanta ba, take kaunarka Wanda data kara girma ta fahimci cewar babu aure tsakaninku, tayi kuka tashiga damuwa Wanda wannan damuwar itace ta ja har aka mata ripeting makaranta, karshe ta kasa rikewa ta sanar da Annin Ku, ganin wannan ba abunda za, a kyale bane yasa ta sanar dani, bata gaya ma mahaifiyarku ba saboda taji irin furucin da tayi wa yarinya k'arama, cewar inhar ta sake jin wani yanayi na soyayyarka aranta bata yafe mata ba, alokacin ta nuna cewar akwai alakar aura tayya tsakaninku, Amman ta haramta mata kai, saboda wani dalili.
Ban tab'a d'aukar hakan zai kawo ma khairat matsala ba, sai gashi lokacin da ta kwanta asibiti likita ya sanar dani tana da damuwa, idan da hali a San yadda akai akayi mata maganinta, saboda zuciyarta ba zata iya d'auka ba, ban d'auki wani mataki ba, saboda ina ganin abari zuwa sadda zaka kammala karatuka sannan itama tafara hada hadar shiga jamia,sai na sameka da maganar in ka amunce na aura maka ita."

Shiru falon yayi sai shashshekar kukana dake tashi cikin falon, duk na jike hijabita da majina da hawaye.

Cigaba yayi da cewa,

"Sanda kuka dawo nayi farinciki saboda ganin kamar abunda nake tunani zai tabbata,saidai kuma naga kamar ba haka ba, saboda kulawarka kaf akan salma kake yinta, sai kwatsa da kyara da kakewa khairat, har dalilin haka yaja zuciyarta hau hauwa, Wanda likita ya tabbatar mun da cewar wanan matakin shine na karshe data sake ta wuce shi babu makawa zata kamu da ciwon zuciya, shiyasa hankalina ya tashi na kasa natsuwa, gani nake duk sakacina ne,  Amman sai naga wannan damar ce kawai zata warware komi."

"Na samu saudah da maganar hadaku aure Amman Kalmar farko data furta mun itace cewa ta haramta maku juna kaida ita,saboda alkawarin da tayiwa ummin Dubai cewa cikin yaranta babu mai auren wani, ma,ana khairat ko shahida bazasu aureka ba, kai matsayin wansu kake uwa daya uba daya,  alakar aure bazata tab'a shiga tsakanin kuba, don haka khairat saidai tayi hakuri Allah ya bata wani Amman ba kaiba."

"Nikuma nace muddin ka amunce da tayin da nayi maka akan khairat, to kuwa wanan auren babu fashi saidai idan mahaifiyarka ta Dubai ce tace aa ko mahaifinka, kokuma kai da bakinka kace bazaka aureta bah."

Shiru ya k'ara yawaita cikin falon zuwa yanzu kukana ya karu, don sonjin ansar da zai bayar, har ga Allah duk irin abunda yah Areef yake mun banji zan iya hakura dashi ba ina jinsa shine ABIN CIKIN RUHINA Amman ya na iya da hukuncin ubangiji, muddin yace zai auran, inkuma har naji sab'anin haka nayi alkawarin yafeshi har iyakar karshen rayuwata, haka zalika bazan sake tada hankalina akanshi ba zan d'auke shi matsayin yayana uwa d'aya uba d'aya.

Tsawon lokaci baice komi ba Wanda kowa sonjin ta bakinsa yake,  har saida dady yace masa.
"Areef dakai ake kayi shiru."

Ajiyar xuciya yayi yace,
"Abbu meye dalilin da yasa maah ta furta hakan."

Baidamu da tambayar da yayi ba yashiga bashi ansa.

"Watau Areef bari nayi maku dalla dallah."

Shekarun baya tun da mukai aure da sauda saida muka shekara goma ko b'ari bayi ba, nan yashiga sanar dasu halin da suka shiga, da irin takurawar da dangin Abbun suka mata, har sadda suka bar kasar..........

"Ranar da muka sauka kasar gidan ummin Dubai muka sauka, Wanda aranar aka haifeka Areef, tun da aka sallamoku asibiti nida saudah muka nuna sha,awar abamu kai, to sanin cewar suma kaikad'ai garesu yasa bamu rok'aba, to Ashe da saudah suka kebe da hafsat, ta sanar da ita halin da take ciki na rashin haihuwa, har gashi ance na k'ara aure saboda bata haihuwa.
Saboda son juna da tausayin halin da saudah keciki yasa umminku ta nemi iznin mahaifinka, akan zata barma saudah kai, koda yaji halin da muke ciki baiyyi jaa ba, yace har duniya tatashi Arref na mune halak makal, wannan yasa bamu dawo ba saida aka gama shayar dakai, ta dalilinka komi ya canza
Duk da saida kaddarar haihuwar salma tasa na sake wani auren, da marigayiya lantana uwa gareki salma, ranar da aka haifeki ranar mahaifiyarki ta koma ga Allah, saudah ta had'aki da khairat ta shayar daku batare da banbanci ba, kaji tushe mafari komi yanzu INA son ji daga gareka, shin zaka auri kanwar ka khairat kokuwa."

Idona akansa hawaye kawai kefita, yayinda kirjina yake wata irin duka, gyara zamanshi yayi yace.

*"Abbu kamar yadda maah tace nima ina ganin hakan din ne,  kayi hakuri ni nadauki khairat kanwata ta jini ban tab'a jin sonta ba, koda na minty gudane idan nace zan amunce da auren zan iya kwararta, saboda bana son ta,  gaskiyar magana ma SALMA NAKE SO BA KHAIRAT BA."*

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU, UN HAZBUNALLAHU WANI IMAL WAKIL.............kala man da nake ta nanata wa kenan cikin zuciya da kan bakina, duk iyayen AC din dake cikin d'akin sunkai shidda Amman zuface nakeyi ta fitar sharia, jikina har karkarwa yake gaba d'ayan falon yayi tsit bakajin motsin komi.

Abbu ne yayi karfin hali yace,
"Salma kina son yayanku."

Kallonta nayi naga ta sadda kai tana wasa da yatsun hannunta, kafin Anni tace,
"Ansarta kenan Abbun khairat alamun ta amunce kenan."

Jinjina kai yayi duk yana yinsa ya canza sosai, daka kalli fuskarshi zaka gane ranshi ab'ace yake.

"Kowa na iya tashi zan nemeku idan bukatar hakan tatashi."

Daya bayan daya haka kowa kefita jiki babu kwari, maah duk jikinta yayi mugun sanyi,  ta kasa yiwa Abbun magana.

Tashi nayi zan fita don har wata juwa ke kwasata, jinai Abbun yace,

"Yaki nan ta alkairi, kisameni da safe kafin nafita aiki, kinjiko."

Ban iya bashi ansa ba kawai jinjina kai nayi nafita................






Mom muhsen

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now