11&12

20 2 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira7531

      🅿️.......10&11

Har na isa b'angaren Anni tunani ya cushe Mani k'walwa, ni banga abun fushi anan ba, to mema nayi masa har haka koko don na tafi wani waje bayan nasan zai dawo, to in nasan zai dawo goyashi zanyi, koko mezan masa.

Tsaki naja sanda nake ajiye mayafi na, kallona yah meenah tayi tace.

"Lafiya dai, ya kuka k'are dashi."

Raina 6ace na wurgar da jikkata nace,

"Wai yah meenah ni za,a dizga kiga fa yadda yake ta shan k'amshi, kodai ubana in yaje unguwa ya dawo iyakar abunda zan mar kenan, to d'aukarsa zanyi don murna shine zai banza dani, to gidan ya tarar bazan lamunci wulakanci ba, idan wancan karon anyi nashanye yarinta Ce yanzu kuwa da girmana bazan jura ba wallahi."

Mai yah meenah take shafawa tace mun,
"Ban son wanan zafin ran naki khairat,  ki ringa bin komi ahankali."

"Haba yah meenah kina ganin yadda yayi Mani halin ko in kula,  ita kuma salma kowa yana magana Amman ita uffan ta kasa cewa."

"Nadai ce maki kiyi hakuri ki sama kowa ido, karki nuna b'acin ranki afili, ki share inkikai hakan wallahi zakisha mamaki, oya shiga kiyi wanka kizo kiyi sallah ko mangaruba bakiyi ba ga isha,i anata kira."

Haka na d'auki maganar yah meenah saboda koba komi ita kad'ai ke kulawa da lamarina.

Yadda tace nayi haka nayi,  sai gashi cikin ikon Allah nasamu yar natsuwa, wanka nayi nazo nashirya cikin kayan baccina masu shegen kyau, ummin Dubai ta aiko mana dasu kala uku uku mu uku, ba k'arya ummi naji damu, more exspicialy ni bama yini guda bata kirani bah, haka d'anta yah imran jininmu y had'u da juna, don sosai yake ji dani don duk dare idan bana komi, shima yagama duk abunda zai zaikirani video call,  nan zamu d'au lokaci muna hira har wani zubin yah meenah ta zo ayi da ita,  har sun saba dashi itama.

Sallah nayi na gama na jawo system dina ina cireta daga caji, yah meenah tashigo.

"Khairat kifito muci Abinci inji yah mujahid."

"Wallahi da kwanciya zan, inyaso inci abincin anan d'aki, Amman tunda yah mujahid ne muje."

Abaya doguwa har k'asa nasa mukafito, ina cigaba da danna system din, muna hira har cikin falon maah.

Salma ta tusa shi gaba yana cin abinci, ga uban juice da ta had'a mashi, itace keta zuba mashi surutu kamar kanyar da babu dadi.

Bama tasan mun shigo ba, mu kad'aine falon maah na wajen Abbu nasani, don baka ganinta irin wannan lokacin, idan ba tazo duba muba, don duk dare zata zo taduba idan munyi baci, in bamuyi ba tace komi muke a ajiye akwanta.

Zama nayi kusada yah mujahid k'asa nida yah meenah.

Murmushi yayi mana yace,
"Kun zama y'anmata khairat, nan bada jima wa ba zamu badaku ko."

Dariya nayi ina danna laptop dina nace,
"Haba yah janmu kake kaima, duka nawa muke ai mun samu muma muyi yar bokon nan da ake mana yanga kanta.

Har ga Allah ni ban fad'a da wata manufa ba Amman Ashe na jawo ma kaina fitina, jinai ya ajiye spoon dinsa yace mun,

" ke!"
Cikin wata tsawa da ta firgitani bama ni kadai ba, har yah meenah ta tsorata.

Juyawa nayi ina kallonsa gabana kamar zai fito waje.

Cikin kakkausar murya yace Mani,
"Da ubanwa kike wannan maganar, watau kinga na kyaleki shiyasa zaki gaya mun magana ko."

Yah mujahid yace,
"Look Areef, ya daga dawowarka zaka fara halinka don Allah Ka daina, ba dakai take ba, karka tada mata hankali."

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now