Bayan tafiyar su jabir da jalal kuwa sama suka wuce wajen part din su, suna shiga sitting room maman su suka tarar azaune hajiya kareema tana waya..,itace uwar gida yayanta bakwai maza biyar mata biyu (Abdulwahab 27yr Ibrahim 25yrs Muhammad 22yrs Khadija 20yr Amina 18yrs ishaq 15yrs sai jabir 10yrs jalal 7yrs) Abdulwahab shine babba acikin yayan babansu wato Alhaji Mustapha badaru gambo, abdulwahab yayi karatunshi ah England inda ya karatan mass com yanxu haka baya nigeria yana aiki da babban gidan talabijin na channels tv company dake England,abdulwahab shine wanda ya gado halin babansu, bashida hakuri ko kadan ga fada sannan yanada son nashi baya qaunar bare, Ibrahim kuwa yana da sauqin kai ba laifi amma kuma shi nashi halin baka taba sanin ina ya fuskanta, shima ya kammala karatunshi ah London inda ya karanta international relations ayanxu haka baya nigeria amma yana gab da dawowa, daga shi sai Muhammad wanda ya kammala secondary school dinshi amma shi yace baya buqatar komawa makaranta sbd shi kasuwanci yake son yi sai Khadija wadda suke kusan class mate da amra, ita kuma tana ss3 yanxu haka suna second term sun kusa fara exams din second term, tana karanta art, Khadija irin yarannan ne masu ji dakai da dagawa bata ragawa kowa sannan itama halin uwarsu tayo ta iya kirsa da kisisna da baqar mugunta itama bata qaunar bare,sai amina wadda take ah ss 2 itama tana karanta art itama dai ba a barta abaya ba saidai ita miskila ce sai ishaq wanda yake sa'a da salima, ishaq mutunne mai son mutane babu ruwanshi bashida rowa sannan bashida zafi ko kadan, sai kananun jabir wanda yake sa'anni da salim yana jss 2 sai jalal wanda yake primary 2.
Hajiya kareema ita kadaice awajen iyayenta hajiya tabawa da alhaji sammani, mahaifinta mai kudine sosai lokacin zamaninsu, ita kadai Allah ya mallaka mashi shiyasa ya dora mata son duniya ita da yayanta. Shekarun hajiya kareema 40 chip aduniya hajiya kareema irin matannan ne da karatu yabi jikinsu, tana da business dinta ahannu inda take sayarda manya manyan sutura ta mata, atampopi laces wanda take importing daga kasashe daban daban, dalilin arzikin babanta dana mijinta shine ya bunqasa mata market dinta.
Hajiya kareem macece mai zafin kishi babu wanda ta sani sai nata, bata qaunar dan riko ko kadan sannan kwata kwata tanayima talaka kallon kaskantacce.sunyi auren soyayya itada alhaji Mustapha tun auren saurayi da budurwa, shekarun aurensu da alhaji Mustapha talatin cirr daga baya kuma ya auro mata kishiya, ba karamin hauka hajiya kareema tayi ba lokacin daya sanar da ita ya kara aure wanda auren nashi kwata kwata bai wuce wata daya ba da haduwar shi da amaryar tasa hajiya labiba,
Alhaji Mustapha ya hadu da labiba lokacin da kasuwanci ya kaishi niger inda yake saro wasu treasure gems masu shegen tsada wanda da kyar ake samun su ah Nigeria,inda yaje sarowa, anan ne ya hadu da mahifin labiba wanda shine babba ah manufactory gem din, ciniki ya barke tsakanin alhaji Mustapha da alhaji rilwanu mahaifin labiba inda mutunci har ya kullu tsakaninsu shida alhaji Mustapha anan ne ya gayyace shi gidansa domin yaci abinci kafin yabar kasar, bayan zuwansa kuwa iyalan alhaji rilwanu sukaje gaishesa masha allah dukkansu kuwa bade kyau ba yayanshi hudu mata haka suka jeru suka tsugunna har kasa suka gaishe sa, daga bisani kuma ya dora idonshi akan labiba alokacin ne yaji kawaii ita yake so, washe gari kuwa dakyar alhaji mustpha ya wayi gari babu jira ya nemi ganin alhaji rilwanu, anan ya mashi bayanin cewa shifa ya gani kuma yanaso,daga bisani alhaji rilwanu ya mashi alkawarin idan har da gaske yake zai tambayi itama yarinyar idan taji ta gani tanaso zai daura masu aure sbd ya yaba da halin alhaji Mustapha dukda bai tsaya yayi wani dogon bincike akansa ba. Bayan rabuwarsu alhaji rilwanu ya nemi ganin yarsa labiba domin ya tambayeta idan har itama tana ciki ay kuwa ta nuna tana so, murna kamar ta kashe alhaji Mustapha lokacin da yaji labiba tayi naám dashi kuma zata aure shi anan ya buqaci alhaji rilwanu ya daura masu aure shida labibarsa sannan idan ya koma gida bayan sati biyu idan ya kammala inda zai ajeta sai ya dawo ya dauka amaryarsa. Aykuwa bayan kiran sallar dhuhur aka daura auren labiba da alhaji Mustapha.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...