55

476 11 1
                                    

Washe gari Monday da wuri amra ta shirya cikin manyan kaya irin namu, atamfa riga da skirt, wanda ta taho dashi daga gida, sun dameta sosai, kayan alatun jikinta kamar zasu farka kayan su fito lol... mamaki ne ya lulubeta sbd agida kayan kamarma yawa sukayi mata, amma yanxu skirt dinma da kyar yake shiga sbd ass dinta daya karu sosai, feshe jiknta tayi da turaren ta mai sanyin kamshi wanda suka taba saya itada Haifa, mayafin ta dauka ta yafa shi gefen kafadarta, ganin jikinta is too exposed yasa ta lullube bayan ta sai tabar gaban, flat shoes ta dauka na zara baki wanda ya fidda kyawun yatsunta wanda tadan goga masu henna kadan wanda ta sayo, chain bag dinta ta dauka ta sanya sannan ta zari wayanta da lap coat dinta da laptop ta fito, ahankali ta sakko ta shiga motorn da tayi requesting sannan suka fara tayi, adaidai gate din shiga head quarter wayanta yayi ringing, ganin number Haifa yasa tayi saurin picking, nan ta shaida mata ta iso already kuma tana cikin asibitin, ciki suka shiga kamar kullum sannan ta bada payment din ride dinta ta wuce direct cikin bulding dinsu, ahankali ta ke takawa harta isa reception, Haifa na ganinta ta taho da sauri ta rungumeta, saida suka gama rungume rungumensu sannan suka wuce office din su amra, babu kowa aciki da alamu hafiza bata karasoba, zama sukayi kafin amra ta fara shirinta, lapcoat kawai ta daura akan kayanta sannan tayi rolling veil din ajikin ta, morning round ta fara wajen sojojin da aka kwantar, saida ta duba daya bayan dayansu daman basuda wani yawa sosai sannan suka wuce wajen head of team office, basu kaiga karasawa ba sukaji hafiza na kiran amra, koda suka juyo suka gaisheta nan amra ta shaida mata zasuje wajen head ne, nan hafiza ta shaida masu cewa itace zatayi dealing da aikin head temporary, juyawa sukayi harda hafiza suka wuce office dinsu anan hafiza tayi ma Haifa komai sannan ta shirya mata nata office din wanda yake gefen nasu office din.
Haifa kam taso ahada su waje daya da amra amma ganin wajen nasu babu nisa Tsakani yasa ta hakura.

Lokacin sallah nayi suka wuce masjid na mata, salla sukayi sannan suka fito ajere ko wacce da lapcoat din ta ahannun gwanin burgewa, fitowa sukayi daga bulding din dama masjid din shine bulding next to headquater bulding, tafiya suka dan yi kafin daya bisani suka jiyo hayaniya, dagowa sukayi ganin waenda akema wannan salute din, wajen duk ya karade, general ne da na hannun damanshi m-5 sai kuma hammam sun fito daga masjid, kallon kallo amra sukayi itada Haifa, kan kowa adaure, jawota gefe amra tayi sbd adaidai hanyar wucewar su suka tsaya, ganin Haifa ta qi motsawa yasa ta kura mata ido tace ''haifa lets go karki samu acikin matsala'' itako Haifa mamaki ne ya cikata, hammam ne ya ganta har sunyi ido biyu amma ya kawar da kai kamar bai santa ba, mamakin hakan da yayi ne ya sata kasa motsawa, ganin sunzo dab dasu yasa cikin amra kullewa, hankali atashe ta duqar da kanta, tsinkayar muryar hammam sukayi wanda ke cewa ''get out of the way ladies''... amar da baima san dasu awajen ba ya dago yayi masu kallo daya sannan ya wucewar shi.. da karfi amra ta janyo ta gefe tace ''haifa wai meke damunki, kinaso akoremu ne ko asamu tsallen kwadon da bamu shirya ba''...asanyaye Haifa ta kalleta, fuskarta tap da qalla tace ''amra bakiga abinda ya faru bane? Hammam ne fa yayi kamar bai san da tsayuwana awajen nan ba, what is the meaning of that''...sai yanxu amra ta dago zancen, wanda yayi masu Magana akan su kauce ahanya wato hammam ne...

Janta tayi suka wuce cikin asibiti, zama sukayi ah office din amra, saida amra ta bata ruwa mai sanyi tasha, har lokacin mamaki ne kwance ah fuskar Haifa, saida amra ta tabbatar ta 'dan sauko tukunna ta fara mata Magana cikin nutsuwa ''Haifa bai kamata don hammam bai maki Magana ba kodan ya kau dakai don ya ganki kiji zafi ba, uzuri zaki mashi, kinga dai babban ne ah headquater kuma kinga wanda yake tare dashi general ne gaba daya na headquater, kuma kinsan yanda aiki yake anan, komai professional ne, ni ina tunanin yayi haka ne sbd kinga bayason asan cewa yana relationship da intern, yanxu haka ma qila bai kula dake ba, ke kuma duk kin wani damu, please karki damu kanki nasan cewa zai maki Magana, ki bari ku fara Magana ke dashi tukunna kinji kafin kiyi judging dinshi".

Sai alaokacin Haifa ta dan ji daidai, don duk abinda amra ta fada haka ne, maybe ma she's just over doing things, kuma dole wajen aiki kowa ya zama strictly professional babu wani nuna kusanci da juna.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now