Bayan sunyi salla suka danyi hira anan ne amra ke tambayan salima ciwon cikinta kallonta salima tayi tana kakalo murmushi sbd batason yar uwarta tana saka damuwa aranta sbd ita, hakan yasa tace ''adda ai ya daina wallahi dama chan stress ne na school activities yayi min yawa yanxu kuwa da akayi hutu kinga na daina kwata kwata'' jinjina kai kawai amra tayi sannan ta hau kan gadon su ta lulluba sai barci.
Washe gari Thursday ta matsanancin ciwo amra ta tashi wanda ya janyo mata sumewa har sau biyu, dama yawanci haka period dinta ke azabtar da ita, idan azabar tayi yawa sumewa kawai takeyi, salima ne kawai ke kula da ita sai mama rabi mai aiki wadda ke lekowa dubata jefi jefi, haka tayi spending ranar akwance washe gari Friday tadan samu sauki wanda yasa ta fara prepation din competition dinsu na school, dukda tanajin ciwon marar nata amma haka ta daure ta fara practising, sai wajen sha biyu na dare ta gama komai ta rufe books dinta sannan ta kwanta gefen yan uwanta.
Washe gari karfe bakwai na safe daidai ta gama shiryawa tsaf cikin uniform dinta wanda salima ta wanke kuma ta goge mata, saida ta dan shafa powder tayi kyau fess fess sannan ta goga lip gloss kada, tadan fesa turaren ta mai sanyin kamshi sannan sukayi sallama da salima ta wuce wajen haladu wanda ke jiranta, gaishe sa tayi bayan ya amsa aranshi yana yaba kyawawan halayyarta da kannenta ba kamar sauran yaran gidan ba.
Karfe bakwai da rabi ta iso school wanda daga yan class dinsu duka sai malamai biyar da principal din school din, shiga cikin school bus dukkansu sukayi sannan suka kama hanyar makarantar NTIC, agaban parking space dake cikin compound din school din daga gefe sukayi parking inda sukaga hadaddun school buses suma suna sauke student din makarantu aciki, anatse su amra suka fara saukowa suka jeru waje daya gwanin burgewa, saida suka jira head of school dinsu hajiya abida da mijinta suka iso tukunna suka kutsa kai cikin school hall din inda ake event.
Tunda suka shiga school din suke ta faman kalle kalle, wato makarantar tayi mugun haduwa sosai, babu hayaniya kwata kwata sai sautin muryoyi da mic daga cikin hall din, anatse suka fara shiga ciki inda ake welcoming dinsu sannan aka basu sits da table wanda aka saka tag din school dinsu, zama sukayi na dan lokaci suna kora ruwa da juice da aka aje akan tables, karfe tara daidai kowa ya hallara, makarantu hudu cur, ko wacce school da garzo ko gwarzuwar su anan aka fara kiran sunayen participant, da yan NTIC aka fara, nan aka kira mutun uku sannan suka hau stage dinsu wanda shima da tag din school dinsu akai sai aka kira leader international school, bayan gabatarwa aka fara da first set of two schools din, tambayoyi akayi masu na wasa 'qwaqwalwa sosai guda uku, daga bisani aka basu two minute each suyi solving,lokaci nayi aka karbi result din su, bayan yan mintuna judges sukayi announcing winners, tashin farko aka watsar da leaders school, bayan Yan mintuna kadan aka kira next set of schools, saida aka fara kiran aero school sannan aka kira makarantar su amra wato ar-rahman, anatse suka fara fitowa aka basu nasu questions din, after two minutes kuwa aka karbi results dinsu sannan aka mikama jugdes, result din da judges suka fada ya matuqar bama mutane mamaki sbd duk cikin schools din an dauka sune zasuzo ah karshen baya wato Yan ar-rahman school sai gashi sun samu point da yawa, sauka sukayi sannan aka kira yan NTIC da kuma Yan Ar-rahman wato school dinsu amra, anan take kuwa suka tapi stage, saida suka tsaya tukunna aka fara masu questions, first attempt kuwa dukkansu suka samu same points, ganin haka yasa aka kara basu mai zafi sosai, ganin haka yan NTIC suka fara cije hakora, time yana clicking kuwa aka karba result, kallon mamamki kowa yake ma yan Ar-rahman school sbd jin cewa sune winners, amra kuwa dadi kamar zai kashe ta because tayi contributing sosai, bayan an salami yan NTIC sannan aka dawo kan yan Ar-rahman nan aka shaida masu ana buqatar gwarzuwa daya acikin school din, wato zasuyi competing against each other, nan aka shiga bawa kowacce question dinta sannan aka umarcesu dasu rubuta ajikin paper, abinda basu sani ba shine same question aka basu kuma answer question din yana da wuya sai idan mutun ya kasance mai qwazo sosai very smart sannan zai iya ansa question din, ahankali presenter ya fara karban ta farko wadda ake kira da fadila,anan ya fadi ansa data rubuta anan take kuwa judges sukace wrong ansa, next student kuwa mai suna hamida itama aka fado nata,anan take judges sukace wrong, ahankali presenter ya karasa wajen amra wadda itace last, kallon paper dinta yayi sannan ya kalleta, ahankali ya fada ansa dinta ay kuwa nan take judges din sukace correct, tafi aka fara yan school dinsu amraa me zasuyi banda ihu don murna, kowa murna yake and kowa is so proud of her, ahankali aka umarci sauran da su koma anan kuma akace amra ta tsaya, nan shugabanni suka fara congratulating dinta murna ma ya hanata dago da kai ta kallesu, daya bayan daya aka dunga zuwa ana congratulating dinta, maza suna bata hannu mata kuma suna rungumeta, jinta ajikin wata mata wadda kamshin turaren oreal ya cika duk wajen sannan kuma wani connection me sanyi ya ratsa sakaninsu yasa amra dagowa ta kalleta, tana sanye da wani tsaddaden lace wanda akalla zaikai 300k anyi mata dinkin bubu, fuskarta fara sol tasha dan cute lipstick fuskarta dauke da murmushi, ''congratulation beautiful you're re such a genius, I'm impressed, infact I am so surprised because this question is the hardest question that only a certified phd holder can answer it, weldone my dear Allah ya maki albarka,'... wanni irin nutsuwa da sanyi dadi ya sanya amra kasa daina kallonta, saitaji kamar ammin ta ce ta rugumeta, ahankali ta fara Magana ''Thank you so much ma,''murmushi matar tayi mata.Wucewa matar tayi sannan ta zauna a high chair domin tana daya daga cikin manyan guests, kiran presenter tasa akayi, bayan yazo da girmamawa ta mashi magana cikin sirri san nan ya wuce stage, anatse matar ta tashi ta futa daga hall din fuskarta dauke da murmushi, bayan futarta presenter ya fara bayani kamar haka ''muna farinciki zuwan kowa da makarantun da suka halarci wannan grand competition din sannan yanxu zamu fadi kyautar da makarantar da taci wannan competition zata samu hade da gwarzuwar data zo itace ta farko, each participant na school din ar-rahman yana da kyautar dubu dari biyu sannan school management din ar-rahman ta samu kyautar miliyan biyar domin bunqasa ilimi acikin makarantar daga karshe kuma mss amra ta samu kyautar scholarship a UAE (united arab emirates) sannan anyi sponsoring karatunta kona shekara nawa harta gama tare da accommodation, sannan tanada damar zabar duk makarantar da takeso ah uae, daga karshe kuma ta samu kyautar waya da check na miliyan biyu daga anonymous guest, mungode da zuwanku duka".
Tunda amra taji wannan batu suman tsaye ne kawai tayi, she can't believe it, wai ita aka yima wannan kyauta, hawaye ne suka gangaro afuskarta, daga bisani ta fuskaci alqibla tayi sujjada tare da godiya ga Allah, saida aka bama kowa kyautar sa sannan suka wuce school, anan ta samu haladu yazo yana jiran isowarta, ganin irin farin cikin da take yasashi tambayarta, murna ma kadai ta hanata fada mashi, saida suka iso gida kuma hankalinta ya tashi tunawa da yan uwanta, daga karshe dai ta kawar da baqin cikin ta karasa cikin dakinsu, koda ta isa ciki akwance ta samu salima tana barci abinta salim kuwa yana gefenta yana wasa da yar nokia amra wadda take bari agida, ganinta yasashi tasowa har gabanta yace '' sannu da dawowa adda'' kitchen ya nufa ya kawo mata ruwa lokacin ta shiga wanka saida ta fito ta nemi abinci tukunna ta tashi salima, ''albishirinki yar kanwata?" zumbur salima ta zauna sannan tace adda kicemin kinci kawai nama sani'' girgiza mata kai amra tayi, ay kuwa aguje salima ta tashi tana rawar murna farinciki duk ya lullubeta, dakatawa tayi sannan tace adda fadamin kyautar da suka baku, aykuwa nan take fuskar amra ta chanza, tagumi tayi sannan tace scholarship aka bani, ganin abun farin ciki amma kuma amra ta bata rai yasata zama kusa da ita sannan tace ''adda scholarship fah kika samu kai alhamdulillah but why do you look so sad?'' shuru amra tayi idonta na kawo ruwa, kollon salima tayi tace ''salima scholarship amma ba'a nan ba'' jin haka yasa salima dariya sannan tace ''to sai me adda,inace idan kinje zaki dawo hutu ko and besides mu na tare mana tunda ba kasar zaki bari ba'' kallonta amra tayi sannan tace ''ah Dubai ne fah salima'' ...zaro ido salima tayi sannan daga bisani kuma ta daka tsallen murna sannan tace wayyo allah na dadi kasheni, adda na dubai fa kikace wayyo Allah alhamdullih''.. mamaki ya hana amra rufe baki ganin qanwarta na farin ciki, farin cikin abunda zai raba su wanda bazata taba yarda haka ta kasance ba, kallonta amra tay sannan tace ''salima kina tunanin zan karba schorlaship dinnan ne?, inaaa..ay bazan karba ba, bazan iya rabuwa dake da salim ba, zandai karbi wayarda aka bani sai cash din 200k din da aka bama kowa each sannan sai check din 2m din amma gaskia bazan karba schorlaship dinba,'' tashi tayi kawai ta fuce salima kuwa dadi kamar ya kashe ta.
Washe gari Sunday amra bata cikin walwala kwata kwata salima kuwa sai tausasa ta take yi akan babu komi ta karba schorlaship din watakila shine zai zame masu alkhairi don idan ta gama karatun kamar sun tsallake baqar ukubar da suke ciki ne ayanxu, zama tayi kawai tana sauraron salima amma bata jin zata iya amincewa. Bangaren Yan gida kuwa babu wanda yasan maganar scholarship din sai daddy wanda yana kallon news da safe yaga program din da akayi na grand Competition din NTIC kuma ya ganta lokacin da ake bata grand kyaututuka daga karshe dai dariya yayi aranshi yana cewa ''this is the beginning''.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomansaAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...