53

123 3 0
                                    

Kwanan ta hudu a kunshe tun bayan last paper rabonta da fita gida, yamma nayi ta shirya cikin shigarta ta zuwa gyming, kamar kullum saidata killace al'aurarta sannan ta fuce, koda isa basit ta tarar shida wasu friends dinshi, yana ganin ta shigo yace ''guys ga sabuwar hit dina chan, saina kwashi rabona'' ya fada da larabci, dariya sukayi sannan yaje wajenta, gaisawa sukayi kamar kullum sannan sukayi exercise tare don kwana biyu tana dan sake mashi sakamakon farko farko da take kaffa kaffa da kowa, saida suka gama sannan tayi shirin tafiya gida, daman akafa take zuwa kuma da dan nisa, basit ne ya soma Magana ''amra let me give you a ride naga duk kin gaji'' farko taso kin yarda chan kuma da taga sauqi ne yazo mata yasa ta bishi, motonshi kirar benz fara suka shiga, suna fara tafiya yayi locking kofofin motar ,ta ankare da hakan amma ta basar, tafiya suke kamar bazasu kaiba, ganin haka yasata tambayan maysa tafiyan baya sauri, gefen titi ya gangara sannan ya juyo ya kalleta har yana matsowa dab ta ita, ganin haka yasa ta bata rai ta fara Magana ''basit what's the meaning of this?" baiko saurareta ba ya fara lalubar hannunta, ganin sabon abu yasata daka mashi tsawa, aykuwa ko gizau baiyi ba saima kokarin taba boobs dinta da yake, da sauri ta kabe hannunshi sannan ta daddage ta Waska mashi mari idanunta sunyi jaa sosai ta fara magana''who the hell do you think you are, kai kasan ni wacece, da alamu bakasan halin matan Nigeria ba, to bari kaji wallahi kana tabani wannan hannun naka ya gama amfani, don mu hausawa ah Nigeria mun yi nisa ah black magic saboda haka ka budemin kofa na futa'' jin tace black magic yasa basit shiga taitayinshi da sauri ya bude mata kofar da gudu ta fuce, batama tsaya ta waiwaye shi ba ta fara gudu, kamar zata tashi sama, bata tsaya ba saida ta ganta gaban apartment dinsu, aikuwa tana tsaya wa ta kyakyace da dariya ta furta ''karamin dan iska yalolon banzan, ashe wasu mazan suna da tsoron asiri'' ciki ta wuce koda ta shiga wanka tayi sannan tayi sallah ta danci abinci sannan ta kira Haifa domin ta bata labara, sunsha dariya kuwa daga karshe sukayi sallama, dannan number su salima tayi yau wata guda Kenan baya shiga, ganin haka ta kira ishaq shi kuma ta shiga amma ba ayi picking ba ganin haka yasa tayi mashi message don lokacin kamar dare ne a nigeria.

Asuba nayi bayan tayi sallah taga reply dinshi na cewa yana bacci ta kira kuma kowa yana lpy sannan zai tura mata hotunan su salima ta gansu sbd ta daina damuwa.

Amar...
Karar wayanshi ne ya tada shi wanda an kira yafi sau goma, tsaki Kawai yayi sannan ya jawo wayan ya kara akunnenshi, jin muryar hammam yasashi ware idonshi ''congratulations General Amar yunus taura of united arab emirates armed forces, and happy birthday'' mumushi amar yayi sannan ya gyara zaman wayan akunnenshi yace, ''thanks dude''... murmushi Hammam yyi yace "now get up nasan baka tashi ba, za ah fara program by 10 so be ready because you're one of the heroes today to be promoted'' ..dariya yadanyi sannan yace ''I will hammam thanks once again'' sannan ya kashe wayan.

Toilet din apartment dinshi ya shiga sannan ya fito ya bude wardrop ya dauko 'ka'kin shi ya sanya, ya fesa turare ya sanya booth dinshi sannan ya jawo rank dinshi ya manna gaban rigar yana murmushi yace ''goodbye to rank 5''...murmushi kawai yakeyi don yasan shi kanshi yayi kyau sosai ba kadan ba, fucewa yayi inda ya tarar da m-5, saida shima yayi congratulating din ogan shi sannan suka shiga motor suka wuce headquater, suna isa gate aka barsu suka shiga dukda yau security din is very tight sbd event din da akeyi yi ayau na promoting officers,direct hall suka wuce, wanda ya cika dam da mutane,manya manyan kasar da manyan sojoji na kasashe daban daban, ciki ya shiga inda kallo ya koma kansa, inda aka tanada ma senior officers yaje ya zauna bayan sun gaggaisa da kowa, jin ana announcing sarkin garin da president zasu shugo ya sanya su mikewa gaba dayansu, saida president din suka zauna sannan suma suka zauna aka fara gabatarwa, mutane da yawa akayi promoting daga freshers to juniors daga juniors to seniors sai seniors to general wanda mutun daya ne tarr za ah dauka cikin senior officers koda akazo kan amar, babu wanda yayi mamaki da sugaji shine akayi promoting to the only general of (uaeaf) kowa tafi ya fara sosai, ahankali zakin ya tako har stage, fuskarshi yau ba laifi dauke da murmushi, anan aka cire tsohon rank dinshi aka saka mashi sabo, bayan an gama ya sara ma kowa sannan aka dunga tafi ana ihun our hero our hero!!! Saukowa yayi daga stage nan idonshi ya fada kan daddy wato baban aman Kanin mahaifinshi Alh Kabiru, da mamaki yake kallonsa sanna ya wuce ya zauna, event akayi na manya anci ansha daga nan aka fara watsewa, tsayawa amar yayi awaje don jiran daddy ya fito don ya lura yana dan gaisawa da mutane, ganinshi da dadyn hammam yasa kanshi daurewa yana tunani yaushe sukasan juna bayan yasan bai taba hadasu ba shima hammam din sau daya ya taba ganin daddy din lokacin ya zo mashi wani zuwan bazata. Sannin Halin dady da kutsa kai cikin manya yasa ya kece Duk wani tunani aranshi.

Koda daddy ya karaso gaban sa, kawar dakai amar yayi sannan kuma ya juyo yana mashi kallon tuhuma, nunfasawa daddy yayi sannan yace''har yanxu baka dauke ni matsayin uba ba da ko gaisuwa ban chanchanta ba dukda ina matsayin qanin ubanka kuma miji awajen uwarka ayanxu'' ran amar inyayi dubu yabaci sbd yanda yake mashi Magana da gatsali..daurewa kawai suka gaisa sannan yace ''bakacemin zakazo ba infact nasan ban gaya ma mummy cewa za ayi min promotion baya ya akayi ka sani '' dariya kawai daddy yayi sannan yace ''kaifa dana ne ya za ayi bazan san duk wani movement dinkaba eh amar?" bai tsaya ya saurari amsar amar ba ya shige mota ya wuce airport..da mamaki karara amar yake kallon moton daddy data wuce sannan ya furzar da zazzafar iska ya shige tashi motor baima jira m-5 ya tukashi ba... direct wani bar ya wuce, don shan iska dukda ba shaye shaye yake ba wajen is decent yakanzo ya zauna yasha non alcoholic dirink ah private louge sannan ya koma gida, yauma chan ya wuce direct ya zauna, saida yadan natsu,mintuna kadan saiga knocking, ''come in yace don duk atunanin shi bar attendant ne wanda zai kawo mashi order, jin sautin takalmi yasashi dagowa, macece kyaudai akwai shi tana sanye da wasu kaya irin na larabawa kamar belly dancers na larabawa kanta babu ko komai ta yarfo gashinta, cikin larabci ta karaso gabanshi tace ''kana buqatar wani abunne'' baiko kalleta ba tun kallon farko da yayi mata kai tsaye yace ''get the hell out of here if you don't want to lose your job and the entire bar now!!!.. jin haka yasa a sukwane ta fice, daman daya shigo ta dauka dan hannu ne waenda ke zuwa private ana biyosu shiyasa ta buyosa, shikuwa damuwar dake damunshi bai sashi jin komai game da ganinta half naked ba, tsaki kawai yayi sannan ya fuce ko shan drink dinma baiyi ba..

Amra's apartment
Tun baya abinda basit yamata bata kara komawa gym dinba tayi zamanta agida, saidai ta danyi workout agida sbd gudun sake afkawa irin wannan masifar, azaune take taji karar door bell dinta, anatse ta je bakin kofar tana tambayan waye, jin muryar Haifa yasa tayi saurin budewa, da sauri Haifa ta rungumeta tace "I miss you amra", itama rungumeta tayi sannan tace "miss you too hammam's baby", ciki suka shiga nan Haifa ke ce mata abuh ya barta ta kwana, hira suka bude har dare yayi amra ta dafa masu pasta sukaci, Haifa na wanke wanke taji karar amra, arude ta dawo parlor tana kallon amra dake rike da waya fuskanta dauke da murmushi tace ''haifa I just received my internship letter, it's the army hospital alhamdlh'' murna sosai suka fara inda Haifa ta zauna jiran nata itama, sai wajen karfe 12am nata ya shugo, saidai kuma ba army hospital aka bataba, taji zafin abin sosai sbd sunso su shiga tare, daga baya Haifa tace zatayi Magana da abu yayi mata hanya a maidata.

Washe gari Haifa ta shirya ta koma gidan, tayi ma abu maganar shima yafisonta kusa da amra nan take yayi waya da head of school, bayan sun gama ya kira Haifa ya shaida mata zata samu amma ance yanxu wajen is full sai an sallami student na wasu school din kuma bazai wuce 2 months ba so zata iya jira daga baya saitayi joining amra, taji dadin hakan kuwa.

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now