49

122 4 0
                                    

Sai wuraren five na yamma amra ta fito daga school tunda ta shiga ride Takoma gida, kodata iso aje package dinta tayi ah sitting room  batabi ta kanshi ba,wanka kawai tayi sannan ta kwanta sbd agajiye ta dawo ko abinci bata nema ba sbd baccin da take ji. Sai around 8 ta farka ta fara neman abinci, tunawa da tanada leftover na kfc yasa tayi microwaving kawai taci tayi nak abinta tunawa da packaging din da akabata dazu yasa ta mike taje parlor ta dauko, kiciniyar budewa ta farayi, abin mamaki kuwa laptop ne aciki macbook air kalar rose gold sai wasu hadadden books da jorter na karatu da pack of pens hadaddu, abubuwan da bata taba tsammanin zata samu ba sai gashi Allah ya bata.

Next day shiri tayi na musamman saboda yau ne first day dinta, yauma sanye cikin abaya kalar sky blue sai flat shoe shima skyblue, tayi rolling mayafin ta saidan lip gloss data goga abakin ta, ba karamin kyau tayi ba dukda kayan nata ba masu tsada bane amma jikinta ya amshe kayan sai ta fito das abinta, laptop din kawai ta dauka da jorter sai wayanta, futowa tayi sannan ta wuce wajen ride din data requesting.

Yauma kamar jiya daburcewa tayi ta rasa ina zatayi, saida ta danyi tambaya tukunna ta kawo facaulty dinsu, daganan ta fara neman class din da zata shiga, saida ta duba portal daman yau ba wani dadewa zatayi ba sbd course biyu ne kawai zatayi, cikin ikon Allah wasu sukazo wucewa ta kusa da ita suna maganar class din da zata shiga nan take tabi bayan su, class ne babba sosai da wani smart board sai kujeru masu shegen kyau anatse ta samu waje ta zauna daga baya baya, lokacin har wata lecturer ta shugo mrs vee, tunda ta zauna babu wanda yako kalleta itama batayi gigin kula kowa ba, daman basufi su goma ba a class din. two hours lecture sukayi sannan suka fito suka shiga wani practical class, shima ana gamawa ta fito ta wuce café abinci ta nema taci wanda tayi mamaki da akace kyauta ne duk abinda kake so kaci, karfe hudu daidai ta iso gida agajiye, wanka kawai tayi sannan tayi sallah daman tun da asuba period din nata ya dauke, kwanciya kawai tayi abinta.

Bangarensu amar kuwa tunda suka tashi da asuba suka fara training, walk suka fara inda suka zagaye dajin wajen kap kusan awa hudu suka dauka sannan suka dawo camp dinsu, wanka kawai yayi sannan sukaci abinci wanda aka tanada masu professional chefs da zasu dinga dafa masu harsu bar camp din.

HAIFA's RES....
Kwance Haifa take akan katon gadonta cikin wani Turkish riga mai santsi ta shan iska, kunnenta maqale da airpod tana jin waka, hannu ta miqa gefen bedside dinta ta dauka glass of orange juice tana sipping, knocking dakinta akayi har sau uku, sannan aka shugo, wata farar mata sanye da abaya baka kanta babu mayafin sai gashinta dake asauke har gadon bayanta, fuskarta sak irin ta Haifa amma ita ta manyanta don Harda furfura ya futo mata, kana ganinta kaga mahaifiyar Haifa, takowa tayi har gaban gadon Haifa wanda yasha zanin gado da duvet mai kyau purple, wayan hannunta ta wafce, da sauri Haifa ta dago ashagwabe tace ''ummii.. aetini hatifi ummi (give me my phone ummi)'' kallonta wadda ta kira da ummi tayi sannan tace ''limadha anat hakadha Haifa? Why are you like this haifa''?.. maraice fuskatayi sannan tace ''ummi me nayi kuma, hutawa kawai nake yi'' cikin larabci matar ta cigaba da mata Magana wanda yake nuni da fada take mata sosai, chan kuma tace ''your abuh is calling you'' ..sannan ta ficewarta ba tare da ta bata wayanta ba,...tashi tayi sannan ta wuce hardakin abuh wato mahaifinta...fadar tsaruwar gidan su Haifa sai wanda ya gani, gidane da ake cema aljannar duniya, komai irin na larabawa,har cikin dakin abuh ta shiga bakinta dauke da sallama, kodata shiga yana zaune akasa gefen gadonshi yanacin kayan marmari,har gabanshi taje ta rusuna ta gaishesa,'' dagowa yayi ya kalleta yace '' Haifa menena matsalarki ne, da makaranta,? Kince bazakiyi karatu ah dubai ba na turaki London, shekaranki biyu achan kikace bakyaso zaki dawo nan, nanma kin dawo na turaki the most popular and high skilled educated university yanxu kin maida abin shiririta, Haifa yau almost a year Kenan bana gane progress dinki sbd haka nayi deciding yanxu duk school din da naga dama zan kaiki sannan wallah daga farko zaki fara, idan baki tsaya kinyi abinda ya kaiki ba kuwa aurar dake zanyi kuma duk wanda yayi min shi zan bamawa, karkiyi tunanin don ke kadai Allah ya bani ko zan kyale ki, no bazan kyaleki ba, idan baki nemi ilimi ba me zakiyi, sbd haka get ready gobe zaki fara makaranta kuma ni zan kaiki da kaina, and mind you duk course din dana zaba maki dolenki kiyi shi'' dagowa Haifa tayi idonta tap da hawaye tace ''abuu'' daga mata hannu kawai yayi sannan ya nuna mata kofa, ahankali ta mike ta futa, shima kanshi ya daure ne yayi hakan sbd yana son diyar tashi sosai amma kuma bazai tsaya rayuwarta ta salwanta ba,

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now