Cigaban labari.......
Sallan asuba da aketa kirane ya farkar da amra wadda ke kwance a kasa miqewa tayi sannan ta tattare kayan shimfidar datayi ta ninke komai sannan ta wuce toilet koda ta fito kwance ta tarar da salima sai salim agefenta, ahankali ta tako ta fara tashin salim...,''salim salim tashi lokacin sallah yayi".,..tashi yayi ya zauna sannan ya fuskance ta, yace '' adda amra kin tashi ashe good morning bari na tashi salima'' dakatar dashi amra tayi sannan tace '' kyaleta zan tashe ta, ka wuce toilet kayi alwala saikazo muyi sallah ko",
mikewa yayi sannan ya bude kofar toilet, saidata jirashi ya fito tukunna ta shimfida masu sallaya sannan suka tada kabbara, koda suka idar addua sosai sukayi dashi da ita, kallon salima yayi wadda ke baje tana barci sannan yace adda maisa salima bazatayi salla bane ita,? Kallonshi amra tayi sannan tace ''salim I will explain to you why salima is not praying but please not now saika girma for now idan nayi maka bayani bazaka gane me nake nufi ba but idan har kaga nida salima bamuyi sallah ba we have our own reason kuma addini yasan da haka kaji ko'' nodding kanshi yayi sannan yace adda let be get back to sleep,'' tashi yayi ya kwanta gefen salima itakuwa amra tattare kayan sallan tayi sannan ta wuce wardrop din su ta aje, doguwar rigace ta barci har kasa ajikinta sai hula, fitowa tayi direct daga dakinsu fitilun ko'ina a kashe yake ahankali ta karasa wajen switch din wutan ta fara kunnawa saidata tabbatar ta kunna wanda zata buqata domin gyare gyaren da zatayi sannan ta wuce cikin kitchen, kodata shiga kitchen din yana nan yanda ta bari fess fess,karasawa har cikin kichen din tayi sannan ta wuce store ta fara dibo abinda zata buqata wajen yin breakfast, saidata fara fere irish da doya sannan ta dora shi akan gas, fita tayi backyard ganin gari har ya fara haske yasa ta kwaso tsintsiya da mopper, sannan ta wuce cikin parlor, duk girman parlor nan haka ta share shi tsaf duk da babu wani datti saidata tabbatar ta gama sannan ta fara mopping din ko'ina.Anaste ta kammala aikin ta sannan ta koma kitchen anan ta fara yan soye soye abubuwa data dafa sannan ta hada masu custard saboda tasan kananu yaran zasu buqata, sannan ta dafa ruwan tea. Wajen karfe 9 daidai suka fara sakko daya bayan daya, Khadija ce ta shugo kitchen jikinta sanye da kayan bacci riga da wanda kanta da ribbom kalar kayan jikinta ta daure yar jelar gashin nata, siririya ce batada haske sannan hancin ta yana nan anane kamar gutsirarren dankali😂, kodata shigo ko kallon amra batayi ba ta wuce wajen tabkeken fridge dinsu ganin haka yasa amra cewa good morning khadi, ko kallonta batayi ba ta bude fridge din ganin bataga abinda take nema ba yasata cewa, "ina avocado smoothie din danace ki dunga hada min duk safiya kina ajewa"??, kallonta amra tayi sannan tace, ''avocado dinne yakare shiyasa ban hada ba'' ..tsaki kawai khady tayi sannan ta dauki bottle water ta wuce dining, ita kuwa amra qannenta ta zubama akula sannan ta aje agefe, mugs din shan tea ta kwasa sannan ta wuce dashi dining room, duk kowa ya hallara amma banda iyayensu mata, daga kan khady, Muhammad, amina, ishaq, jabir,jalal sai khamis da Khalil, halim ce kawai babu acikinsu sai kuma manyan yayyi wahab da Ibrahim wanda basa kasar ma kwata kwata.
Ka'idar gidance duk yaran kowa sai ya sauko anyi breakfast dashi gudun samun misunderstanding kuwa iyayensu basa saukowa saidai ko wacce ta dafa a kitchen din part dinta asama.
kowannan su yana zaune haka amra tazo daya bayan daya tayi serving dinsu, ishaq ne kawai ya bude baki yace mata ''thank you sis amra,'' murmushi kawai tayi mashi sannan ta juya zata koma kitchen, tana gab da shiga kuwa tajiyo muryar halma tana sakkowa daga stair tana sanye da pink riga iya gwiwa,kallon amra tayi sannan tace '' zaki tafi baki bani nawa breakfast dinba kosai na kira mummy?"juyowa amra tayi sannan ta fara zuba mata, ishaq kuwa tsaki kawai yayi, amina kam ko kallon inda take batayi ba,dukda itace akusa da halma .Saidata sallamesu sannan ta wuce kitchen abunta aranta tana mamakin isa da suke nunawa, kamar basune suke wasa tare ba lokacin da iyayen su na raye lallai baka sanin mai sonka saika rasa gatanka aduniya, murmushi kawai amra tayi sannan ta wuce dakinsu,
Tana shiga ta tarar da su salim har sunyi wanka sun chanza kaya ita suke jira, aikuwa tana shugowa salim jikinshi har rawa yake wajen karban kulan data shugo dashi, waje ta samu ta zauna salima nayi mata sannu da aiki. Kallonta amra tayi sannan tace ''salima ku fara ci, ni yanxu agajiye nake zanje nayi wanka idan na fito sai inci nawa nima''...kallonta salima tayi sannan tace adda zamu jira ki kiyi wankan'', qwalalo ido salim yayi yace adda gaskia nikam bazan maki karya ba yunwa nake ji,'' dariya suka fara mashi saida suka tsagaita salima tace "kai salim akwai dan banzan ci", tura mashi kulan salima tayi sannan tace karba ka ci ka rage mana'' amra kuwa toilet ta wuce ta watso ruwa sannan ta fito ta bude wardrob dinsu, doguwar riga ta dauko baka mai yan duwatsu ajikinta sannanta ta koma toilet anan ta chanza kayan sbd salim yana cikin dakin sannan ta dawo ta wuce wajen dressing mirror dinsu, dan roll on kawai ta goga sannan ta wuce wajen yan uwanta anan sukayi zaman su daga bisani kuma suka fuce gaba dayansu zuwa kitchen din, nan suka taya ta daura lunch harta kammala sannan suka jera a dining, daki suka koma lokacin ana kiran sallar azhar, sallah sukayi koda suka idar anan suka dinga jin fitar motoci da alamu ko wacce cikin matan ta kwashi yayanta sun fice abunsu, sukuwa su amra da kanneneta da basuda gata sai aka barsu da gadin gida, ganin zaman bashida ammfani yasa suka fito suka wuce compound din gidan anan ne amra ta tsunko masu guava suka wanke sukaci sannan su salim suka fara wasansu shida salima yana gudu tana binshi abaya ita kuwa amra kallonsu kawai take tana jin dadi aranta daga bisani kuma ta shiga tunanin rayuwar su, harga allah tana son kannenta sosai har cikin xuciyar ta kuma batajin zata iya nesa dazu, suna nan har aka kira sallar magrib sannan suka koma cikin gida, daki kawai suka wuce sukayi sallah, amra bata mayi tunanin dora girki ba saboda basuci na rana ba sannan kuma daman yau Sunday ayaune kuma baba rabi zata dawo mai'aikin gidan gaba daya, daman tana zuwa gida friday da daddare sannan ta kwana biyu sunday ta dawo da yammata cigaba da aikinta.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomanceAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...