Chapter 5-6
Alhaji Mustapha kuwa zumudi baisashi ya fada ma hajiya kareema ba saida akayi wata bayan y a gama yan shirye shiryen shi inda ya gyara gefen part din amaryarsa, dama asama part uku ne, na tsakiya nasa ne sai kuma na gefen left side na hajiya kareema saikuma side din inda su abdulwahab ke sauka in suka dawo Nigeria part dinshi ya gyara tsaf sbd amaryar sa don Har kujeru saida ya chanza, Bayan wata cur Alhaji Mustapha ya shirya tsaf domin dauko amaryar sa labiba daga Niger, aranar da zai tafi ya shiga part din kareema anan ne ya sameta tana waya da abokanan kasuwancinta saida ya samu waje ya zauna tukunna ya fara Magana ''ki aje wayan nan kareema zamuyi Magana mai muhimmaci,'' aje wayar tayi sannan tace ''ina jinka oga'' murmusawa yayi sannan yace daman Magana ce zanyi akan aure na, jin haka yasa kareema miqewa tsaye, idonta wiki wiki ta fara Magana, ''wani irin maganar aure alhaji haba wasa kake ko? don Allah yanxu da girman ka tsofe tsofe dakai maganar aure kake yi, me kake nufi Kenan" ..kallonta yayi sannan yace '' ay ba maganar aure nake maki ba ay nayi auren ne nake so na fada maki ''gabanta ne ya bada daram, ay kuwa tana dagowa me zatayi banda ihu, masifa ihu zagi babu wanda bata gunduma mawa alhaji Mustapha ba daga karshe da yaga abin nata ya zama hauka kuma tanaso ta bata mashi lokaci anan take ya baza malun malun dinshi ya kara gaba, anan yabar kareema da ihu da masifa karshe dai ta koma daki tana bambami.Alhaji Mustapha kuwa saida ya isa har gidan alhaji rilwanu suka gaisa yaga amaryarshi tukunna ya wuce masaukinsa, kwanan sa biyu ah niger ya shirya dawowa shida amaryar sa, su labiba kuwa ansha kuka sosai sbd rabuwa da yan uwanta, anan mahaifinta rilwanu ya danqa mata sadakinta sisin gwal guda ashirin da alhaji Mustapha ya biya, daganan suka wuce airport tana maqale da mijinta, bayan isarsu kuwa gida direct ya wuce da amaryarsa koda suka isa ranar ya taradda kareema batanan tayi tapiya zuwa turkey domin saro wasu kayayyaki bata san wainar da ake toyawa ba saida suka kwashi sati uku suna soyewa tukunna kareema ta dawo kodata dawo ta tarar da labiba sai taga ay idan har tace zatayi kishi da ita raini ne ma, amma dai da mugunta da kirsa dai saita kuntata mata. Aykuwa anan haka labiba ta samu cikin danta na farko Abdul -kareem inda tana haihuwarsa allah ya amshi abinsa, labiba tayi kuka sosai sbd ta saka rai sosai da cikin nan daga baya kuma allah ya kara bata wani cikin inda ta haifi yarta ta farko kyakyawa Halima suna kiranta da halim, halim nada shekara biyar allah ya kara bata haihuwar da namiji inda aka sa mashi Khalil shima yanada shekara uku ta haifi wani dan nata inda ta saka mashi suna khamis auta.
Hajiya labiba irin matan nan ne masu kyau fara ce ga gashi ga kyau saidai itama fa ba a barta abaya ba wajen makirci, batada matsala da dan kowa amma idan ka shiga gonarta tofa zaka sha wahala sbd ita harda yan tsubbace tsubbace takeyi, tunda tazo gidan ashirye tazo saidai kuma ganin hajiya kareema bata shiga sabgarta ba saita aje makaman yaqi amma duk sanda kareema ta takaleta tofa bata barinta sannan kuma basa shiri kwata kwata da yayan salima musammam abdul wahab da Khadija, bata qaunarsu ko kadan suma kuwa basa sonta basa son yayanta,ayanxu yayanta uku halim 17yrs wadda take ss2, Khalil 10yrs jss2, khamis 7yrs nursery 3). Halim irin yarannan ne sangartattu, tanada son gayu sannan abu qalilan yake bata mata rai amma inka iya zama da ita zakaji dadi, shikuwa Khalil irin yarannan suma da Magana bata damesu ba sai khamis dan cutie sarkin dariya da wasa.
Wannan sune ahalin gidan alhaji Mustapha badaru gambo, to bari muji su wanene amra da kannenta salim da salima, ya akayi sukazo gidan,waye mahaifinsu, sannan su asalin yan ina ne sannan menene taqamaiman matsayinsu acikin gidan.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomantikAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...