*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT
08066726866Gentle EXFOLIATING Gel
💃💃💃Kuna Ina masu fama da kurajen fuska
Dark sport
Masu gishirin fuska
Masu oily skin
To kufuto wannan naku ne DILKAR TURAWA 😉💃💃💃Yar uwa kina fama da wadannan Abubuwan sun sa fuskar ki taki smoothie
To futo GHT ta kawomiki abunda zai share miiki hawaye 💃💃💃💃
Gel ne
Zaki shafa a fuskar ki bayan mintuna sai ki wanke da ruwa Mai Dan dumi wato warm water 🌊🌊🌊🌊Idan kika shafa afuskar ki ,kiyi massage nashi na Yan mintuna sai awanke 💃💃💃habawa Yar uwa Zaki Sha mamakin skin naki 💃💃idan kina da wannan prob din sai biyu Zaki Ke amfani d shi a sati .
Idan Kuma bbu kawai kina son skin naki ne yyi glowing kiyi looking matar oga 💃😀😀😀to sau daya a sati 💃💃💃
Mmn MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866
*🅿️05*
Sai da Suka Shekara Daya Cur da Aure kana Wasila tace yakamata Suzo Bauchi. Tunda kuma tace Shikenan mgana ta zauna, Zuwan da sukayi sai da kowa yayi Nadama mussaman Hajiya Don Zuciyarta ta kusa bugawa na ganin yadda Rayuwar Baffa Ta koma Bita zaizai. sai Abunda Wasila tace shi yakeyi Wani karin Abun takaichin ma ko gaida iyayen nasa ma Sai da Wasila tace ya gaida su kana Baffa ya Gaida Mallam da Hajiya.
Tunda ga Zuwan nan bai kara taka kafarshi Bauchi ba. Su kuma basu Daina addu'a ba, Al'amarin akwai ban Tsoro aciki koda Abun yaso ya lalace Da Zarar Wasila Taji lbrin Baffa yana kiran Bauchi abakinshi Zata kira Hajiya Kudirat su koma Wajen Boka su Zube kudi asake sabon aiki. shikenan kuma sai Abu yakara komawa baya, Wasila ta zama itace Uwarshi da ubanshi sai Abunda tace Shi Baffa keyi. Ta mallakeshi dashi da Dukiyarsa gabad'aya daga ita sai Yan:uwanta ke fantamawa da arzikinshi.
iyayenshi ko ya ma manta dasu kwata kwata mganar ibada ko Wasila duk ta kara Susutar dashi dama itama ba gwana ba. Wani lokacin baya sallah akan Lokaci Addu'a ma Baya samun yi balle har yayi ma kanshi ko wani mtsalan Nashi ya ragu.
Saboda Samun waje Har Kannenta Tace su dawo gidan da Zama su Jamila suna tsoma biyar suna Fito da goma. babu Abunda Sukeyi sai dai Su ci su kwanta Suyi chart ko suyi wanka Direba ya Fita dasu yawo, mganar gyaran gida da girki kuma Tun kafin Aurensa da Wasila yana da kuku Josepen,shine ke kula mai da gidan,ko yanzu kuma Da ya Auri Wasilan Babu Abunda ya Chanza Zani.
Tun Bayan Aurensu likitoci Suka tabbatarma da Wasila baza tataba haihuwa ba Har abada sakamakon Tun lokacin Datake kan ganiyar Watsewarta Tayi ta amfani da kwayoyin hana Daukan Ciki su sukayi Sanadiyar lalata mata mahaifa. shiyasa bazata iya Daukan ciki ba, Wasila bata wani damu ba ta bar Abun Aranta tana ganin sai dai ita da Abdallah su Mutu basu ga Dan kansu ba. ammh Bazata taba bari Abdallah yaji wannan lbrin ba balle har ya kara aure Wata tazo ta Haihu dashi.
Rayuwar Wasila ta chanza Fiye da Tunanin mai karatu, takara Fari da kiba da kyau Abdallah ya Siya mata Motar Kirar Vibe2019 sabuwal dal Ga Kudin daya ke Bata tana yarda taga Dama Babu Abunda ya Shafeta, Illah Soyayyar Abdallah Wanda takejin ko Uwar data Haifeshi bata Fita Son Shi ba shiyasa take bala'in kishinsa ko kallon Banza wata mace bata isa tayima Abdallah ba yanzu Wasila zata Fara hauka. shiyasa yake kiyayewa kirarin Da wasila take ma kanta itace kwara d'aya jallin tal matar Abdallah da ita zai Rayu kuma da ita zai Mutu.
Abunda bata sani ba Bayan Auresu Da Wata goma Tafiya ta kama Abdallah Zuwa Lagos wajen Saminar daga wajen aikinsu yaso Ya taho da Wasila ammh sai taki. tace mai ya Tafi kawai ashe lokacin tana son taje Bidda zasu koma wajen Boka, akan mganar iyayen Abdallah Tana so ayi musu Farraqu har abada atsakaninshi da wannan Shegen mijin Kanwar nashi Yusuf.
Wannan Zuwan Shine Sanadiyar Had'uwarshi da POLINA Wacce ta kasance Ba musulma ba kuma Karuwa ce Sosai wacce tasan Duniya sosai.
A Hotel d'in da Abdallah ya Sauka anan ya kyallah ido yaga polina kawai yaji ta burgeshi Don shi akwai Son mace Doguwa Fara mai jikin Mata,ammh Duk da haka bai mgana ba. Saboda ajinsa,sai itane data hangeshi sanda yake kallonta ta kariso gareshi tana mai kwakwarsa, Da farko tashi yayi ya bata waje,Ya nufi dakin daya sauka ganin haka yasa tatashi ta bishi,yadda taga ya bar mata dakin Abude yasa ta tabbatar da yana Ra'ayinta.
Da farko tasha Wahalanshi don yayi mata jin kanshi ammh sai ta nunamai ita yar Duniya ce tayi amfani da barikinta ta hillace Suka kwana aikata masha'a.
Abdallah yasha mamakin yadda yaji ya Fita daga hankalinshi akan polina Duk da tun dayake bayan Wasila bai taba kusanta Wata mace ma. ammh yaji polina tasha bambam da Wasila nesa ba kusa,ta tafiyar dashi yadda ya kamata,sai gashi Wasa wasa Shakuwa ta Shiga tsakaninsu Suna tare har yayi kwana hud'un da zaiyi yayi Shirin komawa nan f hankalin Polina yatashi Domin ita ta kamu da Son Abdallah gaye ga kyau ga kudi ga iya Sarrafa mace.
Dakyar ya lallasheta akan zai dawo ya bata kudi masu yawa bayan sun karbi Nombar wayar Juna.
Baisan Wasila Lami ce ba sai da ya Dawo Suka Kebance da Juna. Daganan ya tabbatar da bambamci mai yawa tsakaninta da Polina, ai A daddafe yayi Sati biyu ya koma lagos aboye yayi kwana biyu daya tashi dawowa sai ya Dawo Tare da polina Farko guess hause Dinshi yafara ijeta sai daga baya ya Siya mata gida a Elelewo.
ta koma chan bayan ya Siya mata mota yana kuma Dauke da Nauyinta,Duk sanda ya Fita da niyyar Zuwa wajen aiki sai ya biya gidan polina sun Sheke ayarsu da ita kafin ya Wuce ya Riga ya saba da ita bazai iya Rabuwa da ita. ammh fa yana takatsan takatsan kada Watarana Wasila ta ritsashi Shiyasa aduka Nombobin polina ya sanyamata pol1 pol2 Saboda Gudun Wata rana,kuma akwai amana Tsakaninshi da Emeka Direbanshi Duk Abunda ya gani Nuna yake Baiga Komai ba.
balle ma Kowa Haushin Wasila yake ji Saboda tana Abunda ko yallabai baya yinshi.
Farida tazo Haihuwa aka samu mtsala Jini ya yanke mata Ta haihu Yaron data Haifa bai Fito da Rai ba,ko awa daya ba'ayi ba itama Farida Tace ga garinku nan.
Mutuwar Data girgiza Mijinta da iyayenta da yan'uwanta Lokacin da Mallam ya kira yusuf yana gayamai lbrin Rasuwar Farida daya samu yanzu abakin Mijinta Baffa ya fara kira ya sanar mawa.
Kuma ya tabbatarmai da gobe zai Hau Jirgi yazo ammh sai me,har Farida tayi bakwai da Rasuwa ba Baffa ba dalilinshi da Yusuf ya kara kiranshi Wasila ce Ta dauka ta zageshi tas tace Kuma Abdallah su dashi har Abada wannan kalaman nata ya bashi Tsoro har ya sanar ma Hajiya ita kuma jin haka ga Rasuwar Farida sai jininta ya hau har ta kara komawa Asibiti nan ma Yusuf bai Dandara ba ya kara kiran Abdallah yana Sanar mai yazo yaga Hajiya hakikanin gaskiya Lokacin Abun yafara sakinshi yaso yazo Bauchi ammh sai Wasila ta ki bada damar haka Ta kira Momcy tace ta koma wajen Boka.
koda taje wannan karon ya mata gargadi na karshen kan Duk Abunda zasuyi Toh Su Tsaya kan Abdallah Sudaina kokarin Son Taba iyayenshi Da kuma rab'arsu.
Abdallah dai zata sameshi ammh har abada iyayensa da yan'uwanshi suna tsaye kanshi kuma bazai taba Rabuwa dasu ba Har abada ko an Rabasu na d'an lokaci ne.
Abun zai sakeshi karshe Reshe ya juye da Mujiya,jin haka yasa Suka Dakata da sun yunkuri yi musu Farraku na har Abada suka koma bangaren Maida Abdallah tamkar bawansu kuma Sun samu.
domin Tunda ga Ranar Abdallah bai kara mganar Zuwa bauchi ba balle Ya Tuna da Wata Hajiya..
Mallam ya Umarci kowa da ya Daina damuwa akoma ga Allah,shiyasa Duka yan'uwanshi kowacce ta daina barcin Dare. suka dage da ma dan"
'uwansu, addu'a kan Allah ya kwatoshi. hakama Yusuf bai zauna ba, Shima yanayi kuma yana sakawa ana ma Abdallah saukan Qur'ani, shiyasa lamarin yafara lalacewa gashi yana son yaje ammh kuma Abun yana so yafi karfinshi,Kuma ya rasa ya zaiyi baida Tunanin yayi addu'a sam da kila Abun yazo mai da Sauki.
Tun Bayan Haka sai Yusuf ya daukema Dukkan Su Hajiya Wani Nauyi inda zai zo wajensu zai zo da kayan abinci Niki Niki,kuma in Zai tafi ya basu Kudi Tun suna kin karb'a yana matsa musu har suka koma Suna karba tare da sakamai albarka. Ko bakomai yana Goge Wani kewar Baffan agaresu.

YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU.
AdventureLabarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.