Chapter 29

238 21 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you covered

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.

          *🅿️29*

Da Hanzari Ta Yaga Sikat din Atamfar Dake Jikinta Lokaci Daya Tana Yamutsa gashin Kanta Tana Dariya Tana Kuma Kuka Lokaci daya.
Tana Soshen Soshen Jiki Musamman ma Gabanta Take Fad'in"Baka isa ba Abdallah yadda bazan Haihuwa ba kaima ba Macen Da Zata Haihu dakai.."
Take Fad'a Tana Yaga Rigar Jikinta Cikin Mintina Ta Yaga Duka kayanta ya Rage Daga Ita sai Bra da Underwear, Shekowa Tayi Da Gudu TaNufi Hajiya Abdallah yayi Hanzarin Tare ta Ya Tsinke Wasila da Wani Wawan Mari Yana Fad'in"Baki da Hankali ne...? Dama Na dad'e da Sauwake Miki Wasila Tunda Na Fahimci ko ke Wacece, Lokaci Kawai Nake Jira Na sanar dake Kuma gashi Lokacin yayi Kina Duniyarnan Zaki ga Na Tara Zuru'a da Ma'u Kuma Asirinki bazai Kara min Tasiri ba Kije na Sakeki Saki Uku Wasila Daga Karshe kuma Allah ya Isa Tsakanina Dake."Yafad'a Idanuwansa Suna kad'awa Saboda Bacin Rai.
Wasila Dake Dafe Da Kunci Ta Wani Saki Dariya kafin Ta Zube Kasa Tana Fadin"Ka sakeni fa Kace...? Wlh karya kake Bazan Taba Rabuwa dakai ba, Nifa na Maka Asiri ka Haukace akaina Nida Momcy Mukaje gidan Boka Mukasa Aka Mallakeka Kuma Aka Rabaka da iyayenka..nina...nina..."Haka Wasila Ta Dinga Tonama kansu Asiri Duka Abubuwan da Suka Aikatama Abdallah sai da Tafad'a Kafin Ta Fara Fizge Fizge Tana Soshen shoshen Jiki Duk inda Ta Sosa Sai Jini ya Fito Ta Kuma lashe da Hannunta
Hajiya da Asma'u Suna Tsaye Suna Kallon Ikon Allah Ma'u Ko Tsoro ne ya kamata na Ganin Abubuwan da Wasila Keyi na Alamar Fitar Hayyaci, Kamkame Hannun Hajiya Tayi Tana Makyarkyata, Abdallah Yana Gefe Hannunshi Sarke a kirjinsa, yana Kallonta kamar ya samu Tibi.
Hajiya ko Kabbara Take Cikin Zuciyarta kafin Ta Furta Afili Tana Fadin"Allahu Akbar. Allah yayi gaskiya Dayace Kada Ku Had'ani Da wani Hallitana Wajen Tarayyah. Kunyi Iya Abunda Zakuyi gashi Lokaci Kankani kina Girban Abunda Kika Shuka..."Ina Wasila Bata Jinta banda Soshe Soshe Da Karta Naman Jikinta ba Abunda Take Tana Faman Mganganu Ita Kadai Tashi Tayi Tana Nuna Abdallah Tana Dariya Kafin Tayo Kanshi yaja baya Hajiya ta kama Hannun Ma'u Suka Matsa Gefe Tana Fadin"Kai Abdallah Tafa Haukace  Maza kakira Jami"an Tsaro Kafin Ta Mana Illah.
Abdallah baiyi Mgana ba Saboda Ganin Wasila Ta Nufoshi Da  gudu Tana Neman Rikeshi ya sanya Hannu ya Riketa yana Kwalama Emeka kira da Megadi da Gudu Sukazo Wasila ya Nuna Musu yana Fadin"plz Take her To dis Room.."Yafad'a yana Nuna Musu Dakin da Zasu sanyata Da Hannu Wanda Dakin da ada yake kiwon Zomo ne Mutuwa yayi Da Hanzari Suka Kamata Tana Fizge Fizge Tana Wasu Surutai Suka Shiga da Ita dakin Dakayar Suka Kulleta saboda yadda Take Kokarin Sai Ta Fito.
Ajiyar Zuciya Abdallah ya Sauke Kafin yayi Gaba yana Fadin"Mu Shiga Ciki Hajiya..."Kada Kai Tayi Kafin Tace"Allah ya kyauta..."Ma'u Ko Idanuwanta Har Sun Ciko da Kwallah Saboda  Tsausayin Rayuwa da Kuma Tsoron Allah Daya Kara Shigarta.
Haka Suka Shiga Ciki ita dai Bedroom dinta ta Wuce Ta Shiga Wanka Hajiya ko Tana Falo Ita da Abdallah Suna Kara Jinjina lamarin Haka ma Ma'u Abun yaki Barinta Ranta, Koda Ta Fito Wanka Zuru Tayi Duk Jikinta yayi Sanyi,sai da Hajiya ta Shigo ganin Halin Data Shiga Ta Zaunar da Ita Tana lallashita Har Ta saki Ranta Tea hajiya Ta Had'amata Shikuma Abdallah ya Fita ya Siyo Abinci Koda ya kawo Hajiya ce Kad'ai Taci ma'u Har Tayi Barci sallama ya yi maata ya Shiga Dayan Bedroom Din yayi Wanka da sallah ya Kwanta yana Tunanin Rayuwa Da Irin Abubuwaa da Wasila Ta furta da Bakinta ta Aikata gashi yau Tana Girban Abunda Ta Shuka.
Washegarin Abun na Wasila ya Huce Tunani Domin Ko kafin Gari ya Waye Tagama Tsige gashin Kanta Tsab Ta Koma Kuma Tana Tsige Na gabanta Wa'iyazu billah, Abun sai Wanda ya gani Dole Imani ya kamaka Haka Take Buga Kofar Dakin Tana Iface Iface da Fizge Fizge Daman Kofar Tana da Kwari  Ammh da Bata Dashi Da Tuni Ta ballata Ta Fito.
Akwana na Biyu Ne Hajiya Tace Ya Kira Mahaifin Wasilan ya sanar Dashi Halin Da'ake Ciki Baiyi Gardama ba Ya Kirashi ya sanar dashi Ammh sai yace yayi Kyau a saketa Tabi Duniya dama Shi ya dace Da Ita.
Jin Haka yasa Hajiya Ta karbi Wayar Tamai Nasihan Hannunka baya Taba Rubewa ka Yanke ka yar,Dole da yayi Hakuri Wasila yarsa ce naHar Abada, Hakuri ya bata yace Zai Zo da kanshi,Da mganar Kwana Daya sai gashi yazo Shida Kaninshi Halin da Suka Tarar da Wasila yayi Muni Sosai. mahaifinta yayi Kuka Sosai nan yace zasu Tafi da Ita Ammh Sai da garada Wajen Goma Suka Taru kana aka iya Daureta Suka sakata amota Suka Tafi Ita da bidda. Chan ma Din Wani Daki na Mussaman aka sata aka Kulle Duk Wanda yazo yaga Halin da Wasila Ke ciki sai ya Kara Tsorata da Duniya Jamila Data Ganta ta Razana Nadama Ta kara Shiganta Wacce Cikinta ya Tsufa Har Bata iya Barci ba Neman Gafaran Allah kawai Tana Gode mishi Da Batayi Mutuwar Wulakanci Irin Wanda Momcy Tayi da Hafsat Ba, Kuma bata Tozarta Irin yarda Allah ya Tozarta Wasila ba Wacce Duk Ta Cire Komai na Jikinta Tsirara Haihuwa Uwarta Take Duk Tajima Kanta Rauni bayan Ta Gama Illata Farjinta Abun ba Kyan gani Wannan Abun ya zama Izina ga Mata masu Bin bokaye Wlh Kisani Karshenki bazai Kyau ba
Hajiya Sati Daya Tayi Shirin Komawa Wanda Ma'u bataso ba Harda Kukan Zata Bita Abdallah ya Hana,Dole Ta Hakura Itama Hajiyar Bata Matsa ba, Su suka Rakata Har Filin Jirgi sai da Suka ga Tashinta kana Suka Komo Gidan Daga Ma'un Har Abdallh Abunda ya Faru da Wasila ya Dakesu Kuma Sun gane Cewa arayuwar nan In baka Bi Allah ba Wlh Kana Tare Da Ganin Masifu Kala kala, Hajiya ko Mamman yazo ya Dauketa daga Filin Jirgin Abubakar Tafawa balewa Bauchi Itama Haka Ta Koma Wannan Lbrin Mara Dadin Ji da Sauraro Mallam ya Jinjina lamarin Kowa Jikinsa yayi Sanyi Tun Balle yadda Hajiya Take basu Lbrin yadda Wasila Ta Dinga Tonama Kanta Asiri dasu Anty Nafi Sukaji ko ajikinsu Allah ya kara ma suka ce Alhakin Yaya Abdallah bazai Barta ba dama.
Wasila fa Abunta yana kara gabane Domin yanzu Tafara Saka Hannu tana Cizgo Naman Gabanta Tana ci Wayyo Rayuwa Wlh mu aikata mai kyau Mu Guji Shirka da Sabama Allah,Dakin Datake Ciiki banda Wari Babu Abunda yakeyi Babu Mai matsowa Kusa da Wajen sai dai  Daga Nesa Anan Cikin Wannan Halin Watarana Da Daddare Ta Balla Kofar Ta Fita da Gudu ba Wanda ya sani sai da gari ya Waye aka Farga An bita ammh Shuru ba'a Ganta ba Ta Nausa Cikin Gari ba Wanda ya sani,Jamila ce Mai Kukan Nadama da Dansani Wanda bai Da Ranar Karewa

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now