Chapter 15

196 28 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku zumar kiba zumar kiba zumace wadda zatasaka kiba cikin kwana 7 dayardar Allah zumar kiba zumace mai inganci wadda aka hadata da magun gunan gargajiya,Bugu da qari har nafdac ta amince da lafiyar zumarmu ta bamu BACH NO hjy indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kasha zuma saika chanza 08167453086

          *🅿️15*

Karfe 11:30am Ta yima Su Mallam Akofar get din gidansu Asma'u da yake Mallam yasan Gidan Tun Lokacin da yazo ya Dauki Asma'u ya Kaita School of Nursing Birnin Kudu.
Yusuf ne ya Fito Daga Motar ya Karisa Jikin Get din ya kwankwansa megadi ne yazo ya Bude Karamar Kofar ya Leko Yana Tambayan waye..? Ganin Yusuf bakuwar Fuska ne agareshi Shiyasa ya fiito ya Karbi Hannun da Yusuf ke bashi Suka Sarke Musabaha,Yusuf ne yace"Don Allah Megidanan na Ciki Kuwa..?

Megadi yace"Eh Alhaji na Ciki Bai Fita ba, Shi kuka Zo Gani..."?Yafad'a yana Leken Proff.daga Cikin Mota ganinsu ba wani Alamun Raini Cikin Kamala ,Yusuf ne yace"Eh Don Allah Ko Zaka Shiga Ciki ka mana Mgana Dashi..? megadi yace"Yanzu Kuwa.."Yajuya Da Hanzari Zuwa Cikin Gidan Koda Yayi Sallama a Babban Tsakar gidan Umma ce ta Amsa Daidai Lokacin Data Fito Daga Kitchen Hannunta Dauke Da Wani Katon Tire na Kayan Breakfast Din Abbane Dayake Baya karyawa Da Wuri ya Riga ya saba sai rana ta d'aga.
Amsawa Tayi Tana kallonshi. Rankwafa Yayi Yana Fadin"Ina Kwana Hajiya.."Kai Tsaye ta Amsa Tana gyara Zaman Farantin Hannunta, Cikin girmamawa yace"Hajiya Dama Alhaji ne Yayi Baki Suna waje sunce nayi Musu Mgana Dashi.."Umma Tace"Baki Kuma..? Daga ina Kuma Habu..?
Kansa na kasa yace"Wlh Bansani ba Hajiya ammh Dagani Manyan Mutane ne gaskiya.."Jin Haka yasa Umma Wucewa Zuwa Kofar Da Zai Sadata Da Shashen Abba Tana Fadin"Ok kace Gashinan Zuwa Bari na Sanar da shi yanzu.."Da Tom ya Amsa Kafin ya Fice Da Sauri Itama Ta Karisa Falon Abba Bakinta Dauke Da Sallama.
Abba Dake Kokarin Saka Hulan kansa Ya amsa Wanda Ke Tsaye  a tsakiyar Falon Yana Kara gyaran Zaman Hullan kube d'in Din Dake Kansa, Center Table Din Dake Tsakiyar Falon Taja ta Ijiye Tiren Dake Hannunta Tana Bin Abba Da Kallo Kafin Tace"A"a Alhaji Naga kana Sanya Hula badai Fita Zakayi ba..,? Gafa Breakfast Dinka Na Kawo maka.."
  Mirmishi Yayi Yana Gyara Zaman Babban Rigar shaddan Dake Jikinsa Lokaci Daya Yana Kallon agogon Fatan Dake Hannunsa yace"Bar Abun Karyawan nan Mandiya Ina da Haduwa da Alhaji Hadi a company Kuma ya Kirani Tun dazu Cewa ya Iso Ni yake Jira. Saboda haka Sai na Dawo Kawai.."Fuskarta ba Dad'i Tace"Shikenan.."Yana Kokarin Ficewa Daga Falon ne Umma Take"Au Alhaji."Tafad'a Tana Bin bayansa Waigowa Yayi Lokacin Yana Saka Wani Budadden Bakin Takalmi.
  Umma Tace"Kaga na Manta Yanzu Da Zan Shigo Na gamu da Habu Megadi ya Shigo Wai kayi Baki Ana Sallama Dakai.."Kallonta Yayi kafin yace"Haba Mandiya Kinsan da Haka Kuma Tunda Kika Shigo Baki Fadamin ba? ai sai Suce An shanyasu Fisabillah.."Umma take"Yi hakuri wlh na Sha"afa ne.."Kai ya Gyada kafin yace"Ok ya Wuce Bari Naje na Gani Kila Dagachan na Wuce  bani key din Motar Chan.."Ya Fada Yana Nuna Mata Key din Dake Kan Kujera Da Hanzari Ta Dauko Ta Mikamai ya Karba Ya Fita Tana Mai Adawo Lafiya.
D'akin Hajiya iya Ya leka sai ya Tarar Da Ita tana Ta Sharar Barci Bai Tashe ta ba kawai ya Fice Da Hanzari Saboda Bakin Da'a kace Suna Jiransa awaje.
Koda Abba ya Fito Haraban Killace Motocin Gidan Bai ga kowa ba Sai ya Dumfari Get Yana kwalama Habu Kira,Wanda ya Fito Da Gudu Daga karamin Dakinsa Dake Gefen Get din,ganin Alhaji yasa yaRankwafa Yana Gaisheshi Amsawa Yayi yana Fadin"Ina Bakin Da Suke Son Ganina.."?
 Cike Da Ladabi Habu Megadi yace"Suna Waje Alhaji.."Kallonsa Yayi kafin yace"Haba habu meyasa Kabarsu awaje, ai Daka Bude Musu get din Sun Shigo.."Kan Habu Megadi na kasa Yace"Ayi Hakuri Alhaji.."Ya Wuce Yana Fadin"Bakomai.."Da kansa ya Bude Karamar Kofar ya Fice Kafin ma Habu ya Kariso.
 Shiko Yusuf habu na Shiga Cikin Gidan ya Koma Cikin Mota yana Gayama Mallam Gashinan Zuwa, Wayar Yusuf aka Kira Sai ya Fito Daga Motar ya Jingina da motar Yana amsa Kiran,Bai Dade ba Sai ga Abba ya Fito ganin Yusuf Jingine Jikin Mota yasa yagane Sune ke Nemansa Cikin Natsuwa ya Karisa Ga Yusuf din Wanda Tunda Yaga Fitowarta Abba yayi Saurin yanke Kiran.
Cikin Fara'a Suka Tarbi Juna Bayan Sunyi Musabaha, Abba na Kallon Yusuf yace"Bawan Allah Ban Shaideka ba,kuma Ance Kana Sallama Dani.."Yusuf ya kalli Abba Zaiyi Mgana Kenan Mallam ya Bude Murfin Motar Ya Fito yana gyara Zaman Gilashin Idonsa.
Hannu ya Mikama Abba Sukayi Musabaha kafin Mallam yace"Alhaji nine ke son ganinka Indan ba Damuwa  Ni Sunana Proff.Mahmud Abdallah Azare Nine Mijin Tsohuwar Matarka Habiba.."Jin Haka yasa Abba ya Kalli Mallam Yana Yar Dariya yace'Oh Allah Sarki Sannunku Da Zuwa,Masha Allah Ku Shigo Daga Ciki ai bakwa Tsaya Daga waje ba."
Mallam yace"Toh ba Damuwa"
Abba yayi Gaba Suka Rufamai Baya Har Zasu Shiga Gidan Abba ya Waigo Yana Kallon Yusuf yace"Bawan Allah Daka Shigo Da Motar Ciki daga ciki ko? Yusuf ya Juya yana Fadin"Toh Abba.."Motar ya Shiga Suko Su Abba Suka Karisa Ciki Ta Kofar Wajen Haraban Gidan Abba ya bude Kofar Falonsa Suka Shiga.
Shikuma Yusuf habu Megadi ya Wangalemai Get ya sulala Da Motarshi Ciki ya fakata Kusa Da Ta Abba,Fitowa Yayi ya Kulle Motar Shima Yayi Sallama Cikin Falon Yayin da Mallam da Abba Suka amsa Yusuf ya Shiga yasamu Gefe ya Zauna Yana Gaida Abba,Amsawa Yayi Cikin Sakin Fuska kafin ya Mike Yana Fadin"Ina Zuwa.."
Mallam yace"Ba laifi.." Da Sauri Abba ya Fita ta Kofar Cikin Gida Yana Kwalama Umma Kira, wacce Ke Daki Ta Fito Da Sauri,Hajiya iya ma data farka daga barci yanzu  Sai Da Ta Fito, Anty amaryace Dama Tana Tsakar gidan,Cikin Mamaki Umma Ke Fadin"Gani Alhaji Lafiya Naga k Dawo..? Yana Gyara Zaman Haban Babban Rigansa yace"Kedai Bari Ban Tafi ba Daman Bakin nan ne na Shigo Dasu Daga nesa Suke Maza Ahad'a Abinci Da Abun Sha Don Allah akawo Musu Falona.."Hajiya iya ce Tace"Ladan Wasu Baki ne Wanna Naga kana Ta Rawan jiki..?
Ya Juya Zai Koma Ciki yana fad'in"Iya masu Muhimmanci ne, Don Allah Halima ko Mandiya ku Hanzarta.."Yafada Yana Wucewa Shashen Nashi,Anty Amarya ce Ta Mike Zata Shiga Kichen Hajiya Iya ta katseta Da Fadin"Ke Halima Dawo, Ke Mandiya hada Musu Komai ki Mika Falon Ladan.."Tafada Kai Tsaye tana Wani Hade Rai.
Anty Amarya Takalli Hajiya iya ta Danyi Mirmishi Duk Da Tagane Manufarta sai Ta Dawo da Baya Tana Fadin"Toh ai Bakomai Nida Ita Din Duk Daya ne, Dama ganin yace ayi Sauri ne Shiyasa na Mike.."Tana Gama Fadin Haka ta Shige Dakinta Umma Da Hajiya Suka Bita Da Harara Kafin Hajiya Iya Tace"Hanzarta Mandiya Kinga yace Bakin masu Muhimmanci ne, kila ma Manyan Mutane."Umma Tace"Toh.."Ta Nufi Kichen.
Dama Already Da Safe Su Baba lami Sun Dafa Ferfesun Kayan Ciki,sai Soyayyen kwai Da Kuma plantains, harda Soyayyen Buredi sai Ruwan Zafi da Kayan Tea,Shi Ta Hada awani Babban Faranti Shima Mai Kyau Da Tsari Daki TaKoma Ta Sanyo Mayafi, ta Mai Kyau Ta Dauki Tiren Ta Nufi Shashen Abba.
Suko Su Abba Suna Kara gaisawa Da Mallam Kenan Sai ga Umma Tayi Sallama Suka amsa Ta Shigo Taja center Tablen din Dake Wajen Bayan Ta Sauke Farantin Kayan karyawan Abba Ta Dora Wanda Ta Shigo Dasu, Dan Rankwafa Tayi Tana Gaishe Da Mallam ya Amsa Kansa na Gefe Ita ko Kallonsa Take Duk da ba Sosai Ta ganshi ba Ammh Tabbas Dattakonsa Da haibansa Sun Daketa Kuma ga Dukkan alamu Hutu Da Naira Sun Zauna Mishi.

ZAMAN GIDANMU.Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ