Chapter 21

210 24 1
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you covered

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.

           *🅿️21*

Yusuf da Kamal ne Asahun gaba Wajen Isa Kusa da Inda Abdallah Ke Kwance Yana Shure Shure.
Yusuf ne ya Tallaboshi Cikin Wani Tashin Hankali Wanda ya Bayyana Daga Fuskarshi Zuwa Cikin jikinsa.
Cikin Muryan Fitan Hayyaci yake kiran Sunanshi."Abdallah...Abdallah ka Tashi meya Sameka...? Ammh Ina Abdallah sai Wani Kara Shure Shure  yake idanuwansa Suna Kulle Tamau,Hulan kanshi ya Ciremai kamal kuma ya Ciremai Babbar Rigar Jikinsa Yana Mishi Fifitata.
Nan da nan Mutanen Dake Wajen Hankalinsu Yafara Zuwa Wajen Abunda Ke Faruwa, kafin kace Kwabo An Zagaye Su Ana Kallon Ikon Allah,Ciki Harda Fahad Wanda Hankalinsa Ke Matukar Tashe, Mikewa Yayi yana Ciro Wayarsa Daga Aljihunsa da Hanzari ya Kira Mallam awaya yana Sanar Dashi Abunda Ke Faruwa Cikin Tashin Hankali,wanda Har Muryansa ta Canza Kwallah Sun Taru agefen Idanuwanshi.
Mallam da dasuke Tare Dasu Abba Acikin Masallaci Suna gaisawa Da Jama'a ya samu Kiran  Yusuf Cike da Tashin Hankali Mallam ke Salati. yana Sauke Wayar ya Sanar Dasu Abunda Yusuf ya gayamai Wai Abdallah ya Fadi Awaje.
Da Tashin Hankali Su Abba da Baban A'isha da Mallam D'abarani Suka Fito Daga Cikin Masallacin, Dakyar Suka Kutsa Cikin Jama'a Zuwa Wajen da Abdallah ke Kwance yana Shure Shure.
Lokacin da Mallam yayi Tozali Da Abdallah Sai da Jikinsa ya kama Rawa Durkusawa yayi gabanshi yana Girgizashi lokaci d'aya yana Kiran Sunanshi,Hakama Su Abba na Tsaye Suna Salati.
Mallam D'abarani ne ya Duko yana  kallon Abdallah kafin ya Sunkuya ya Tofamai Addu'a Sai yayi kamar  Yabar Zabure zaburen sai kuma ya Cigaba da yi, Yusuf ne yana Sharan hawaye yace"Mallam mu kaisa Asibiti kalli Abunda Abdallah yakeyi..? Yafad'a yana Kokarin Dagosa Mallam D'abarani ne ya Dakatar Dashi Da Hannu yana Fadin"lalurarshi bata Asibiti bace, Shawara Dayace Ku Sanya shi Amota Mu koma Gida Sai Munsan Abun yi.."Yafad'a yana Kara Kallon Abdallah.
Yusuf Zaiyi Mgana Kenan Mallam yace"Ku Daukesa Kusashi Amota.."Yafad:a cike Da Dattako,Da Kuma Kokarin Boye Tashin Hankalinsa ba Musu Yusuf da Kamal da Wasu yan'uwa Suka Taimaka sukama Abdallah Rikon Talala Har Cikin Mota.
Shi kuma Mallam yaja Abba gefe dashi da Baban A'isha Yayi mgana dasu na Tsawon Minti Goma kafin Naga Sun Sarke Hannu Sunyi Musabaha, Abun mamaki Babu Wanda yabi Takan Asma'u amarya Da'aka Tsara cewa bayan Daurin Aure Za'a Wuce Da Ita, Ammh Saboda Abunda Yafaru Cikin Tashin Hankali motocin Bauchi Da Tawagar Angon Suka bar Kofar Gidansu Asma'u
Kafin kace Kwabo mgana tafara Yad'a Gari Da Dangi,Domin da Yan Daurin Aure,da Wanda yaji Lbrin Duk inda Suka Zauna Sai Sun Bada Lbri, Lbrin ya isa Cikin Gidan Abba Inda mijin Anty Rukayyah yafara Kiranta yana Tsegunta mata wai Ana Daura Aure Abdallah ya yanke Jiki ya Fadi Harda Kari, Jini Ta Hanci Ta Baki,yana Ta Zabure Zabure Kamar mai Kamun Hauka, Harda Ce mata Dama Yasan cewa Aljaniin Daya Aure Asma'u bazai Taba Barinta Tayi Aure ba
Umma Dataji lbarin ita da ya'yanta Yadda Ku kasan su Zuba Ruwa akasa Susha Saboda Murna Umma Fad'i Take, Dama Za'arina na baya yi Nasara ba, na yanzu ma  Ai bazai kai Lbri ba Duk da ya juya kwanjinsa Harya Kafa Tarihin Dauramata Igiya ukun Da Na baya Suka Kasa,Hajiya iya kuwa Tana Ji Tafara Fad'an,wai dama Ta Fad'a Asma'u Bata da lafiya, gashinan Zata Kashe Dan Mutane.
Su Anty Amarya ne da Wasu Dangin Abba Suka Shiga Damuwa,Mama ma na Daki ita Da ya'yanta Suna Ta Maida Zencen yadda Mazajensu Suka Karanta musu.
Achan gidan Ammi kuwa Lokacin da Lbrin yazo a bakin Kawu, Asma'u na Uwar Dakin Ammi ne,Ammh Sai gata Ta bayyana Atsakar gida inda Kowa Ke Tsaye Cirko Cirko Ana salallami.
hannu Ta Ɗora Bisa Kai Idanuwanta na Zubar da Kwallah da gudu,ƙafafuwanta Suka Daina Daukanta Bata Da Wani Zabi Illah Zubewa kasa asume kamar Matacciya A'isha Dake Gefe Itama Tana Kuka Tayi kanta Ita da Sauran Kawayensu.
Ammi da Su Goggo Jummai Sai Sharan Hawaye suke Suna Tsananin Tsausayama Asma'u domin Hakika Taga Jarabawar Rayuwa..

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now