Chapter 20

222 17 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KO DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI SAIWOWIN SANYI*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABARU*
*AKWAI SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI SAIWOWIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

          *🅿️20*

Hausawa sukace Rana bata karya sai dai Uwar D'iya Taji Kunya.
Yau dai itace Ranar da za'a Daura Auren Asma'ul Husna da Angonta Abadallah, Tun misalin 10am na Safe tawagar yan Daurin Aure Ta Mika Motoci goma Tsala Tsala na Alfarma cike da Kuma Mutanen kwarai Da Dattako kama Daga Yan'uwa da abokan Arzuka da abokai da makusatan Mallam aciki. Harda Mallam D'abarani atawagar Mallam, sun Tafi Su Hajiya nata Fatan Zuwa lafiya da Dawowa lafiya.
suma Daga Cikin Gida Hidima ta kacame,Maman Fati kuwa Tun Daren Jiya ta kwana sallar dare da Fatan Allah ya Tabbata da Wannan Aure, ba ita kadai ba Hatta su Hajiya basu Zauna haka ba, Suma addu'ar Suke Allah ya sa Adaura Auren Lafiya.
Abangaren Asma'u kuma Kun Riga Kunsani bata Wasa Da Gayama Allah Kukanta da Kuma Tsayuwar Dare, Kwana tayi Sallah Tare da addu'an Allah ya Tabbatarmata da alheri yasa Adaura wannan Auren Lafiya.
A'isha dake kwance Saboda tana Fashin Sallah Sai da Tama Asma'un Hawaye Itama Daga Kwancen Tana addu'a acikin Ranta Allah yasa iyakar wahalar kenan.
Suma tun Safe Anan Gidansu Asma'un Sunata Shiryen Shiryen zuwan yan Daurin Aure,Abangaren Asma'u Amarya kuwa Tun Safe Data tashi Taji Jikinta baya Mata Dadi.
gadai ta nan Tun Wajen 8am na safe Su A'isha suka Matsamata tayi Wanka ta Sanya Daya daga Cikin kayan Akwatuna Wani Leshi ne Ubansu,cbatayi Kwalliya ba Saboda A'isha tace Ummu Salma Kawarsu Wacce Sukayi Islamiyya tare Zatazo Tayi mata Kwalliya, Tana Cikin uwar Dakin Ammi ita da Amir yana Ta Mata Fira,Ammh Bajinsa take ba Kawai Wani Sashe  na Jikinta na bata Wani Abu zai Faru.
gabanta kuma na Yawaita Fad'uwa, Ammh sai Tayi ta addu'an  ko da Safe Dataje gaida Abba sai da Tayi kuka Da yake Mata Nasihan zaman Aure Haka kawai Takeji kamar fa Bazata bar Dutse Ayau ba.
Ammh bata Furtama Kowa ba,Duk da duk wanda ya Kalleta sai ya Fahimci bata da Walwala, A'isha ma Duk ta Damu Tana Ta Tambayan Asma'u ko lafiya sai tace Mata bakomai.
Ko kafin 12 na Rana tayi Har Asma'u ta Canza kaya Inda Ummu Tazo Tayimata kwalliya mai Tsari.
wannan karon Wata Atamfa ce ke Jikinta Super wax, Mai Uban Tsada da yarari,Abun da Zai baka Mamaki ana kamallama Asma'u kwalliya ta fara Kukan Da Batasan Dalili ba balle Dataji Lbrin yan Daurin Aure Sun Fara cika gidansu Ciki Harda su Kawu Daga Dutse Suma Mota Guda.
Su Anty Bilki duk gidansu Ammi suka Dawo Saboda Gulma, Asma'u tayi kyau Hartagaji da kyau,ga lallenta Baki da Ja,wanda yakara haskata,Su Sister Bahijja da Yan Wajen aikinsu da sukazo Tun dazu Suka Fara Rige Rigen Daukanta Hotuna.
Ammh Asma'u Taki Tsayawa Kuka Kadai Take yi ,A'isha ta Damu da Wannan Kukan na Asma'u Ammh sai Ammi tace ta Rabu da Ita kada ta Matsamata kukan Rabuwa da gidane,da Kuma Farincikin yau Allah Zai Cikamata Burinta.
Duk da A'isha bataso haka ba Ammh Haka Ta Rabu da Asma'u Ta Kira Fahad awaya yazo ya Dauketa Taje ta karbo abinci da suka Bada akayi musu,sai gashi Ta Dawo da Uban Kololin Shake da Shinkafa Fried rice ne da Alale sai Kunun Aya da Zobo, Lokacin da Tadawo Fahad ya Ijiyeta kenan ya Taimaka mata Sun Sauke Kololin kenan Motocin Angawaye da Iyayensa Suka Fara Fakawa Akofar gidan Su Asma'u lokacin karfe 12:30pm Lokacin Daurin Aure ya kusa,Ammh sai an isar da sallar Azahar za'a Daura Auren A masallacin Dake Kusa Dasu.
Liman Huzaifa dama Shike Dauramusu Aure,A'isha ta Shiga da Lbrin karisowar mutanen Bauchi.
Asma'u na Ciki na Ji,sai Taji kanta yayi Mata Nauyi Ammh sai Bata Nuna ba,Tunda Kawayensu Sun Fara Zuwa Suna Tare Da ita Suna Ta Mata Shakiyanci.
Koda su Mallam Suka Fiffito Daga Motoci gaiggaisawa Suka Farayi dasu Abba, kowa kagani yaci gayu ba Raini Ango kuwa Yana ta Kunci Da Komai ya Saka gezner nan da Yusuf ya Dinkamusu mai Babban Riga, Shima Sai da yace Sai Hadashi da Hajiya Kana ya Sanya kayan Ammh Tun Asali manyan kaya basa Burge Abdallah yafison yaga ya Tsuke Cikin kananan kaya.
Kuma Abunda baisani ba Manyan kayan Sunfi Amsar sa Sosai Kuma Sun Fi Fitomai da Zatinshi na Cikakken Namiji.
Ko Ayau din Ma Mutane Dadama sai Hamdala Suke tare Da Taya Asma'u Murnan Samun Gwarzo mijin irin Abdallah.
Wanda kaf ya'yan Ladan ba Wacce Ta samu Miji kamar na Asma'u Shikanshi Fahad Yaji Natsuwa ta Kamashi lokacin Da'aka Nunamai Mijin Asma'u Sai da Yaje suka gaisa, dashi da Yusuf, har Hotonshi ya Daukan ma A'isha,Suko mazajen Su Anty Rukayyah Tuni Suka Fara Raina kansu,Domin Susan Wannan ya Zarce  Tsara Sosai.
Fuskar Abdallah bata Saki Ba, Ammh kuma bai Mugun Daure Fuska ba,Kallo daya zai Maka kwarjininsa ya Dakeka Sosai,yana gefe shida Yusuf da Wani kamal abokinsu Tun Suna Mkrantan Abu Zaria,Yusuf ya yagayyatosa.
Mallam ne yace Suzo Suyi Alwala An kira sallah,cikin Lokaci kankanin Jama'a kowa ya Daura alwalansa kafin Manyan Mutane Da Kuma Waliyan Amarya Dana ango Suka Shiga Cikin masallacin Domin Baida Girma sosai, Sauran Jama'a ko Awaje akaja Sahu Ciki Harda su Abdallah,Tsawon Mintina Sha biyar kafin a isar da Sallar,lokacin 1pm ta Wuce Harda Minti goma,nan da nan aka Sanar da Za'a Daura Aure yanzu.
Liman Huzaifa ya Motsa kafin Mallam da Mallam D'abarani Su Matso kusa Inda Abba Da baban Aisha Suke Zaune yana Rike da Sadakin Asma'un.
Nan da nan Mallam ya umarci da Mallam D'abarani Yayima Abdallah Walicci,Shikuma Liman yama Asma'u cikin Abinda bai gaza Mintina Ashirin ba Aka Daura Auren *ABDALLAH MAHMUD ABDALLAH AZARE* Da Amaryarsa *ASMA'U LADAN SHERIFF* Kan Sadaki Naira Dubu Dari biyar Lakadan ba ajalan ba,Hakama Mai Shele ya dinga Sanarwa A lasifakan masallaci,
Daga gidan Ammi Ana ji, haka Daga cikin Gidan Abba, Asma'u na Zaune Tunda Taji Sanarwarn An Daura Auranta Zuciyarta ta Tsinke sai sabon Kuka Share Share.
A'isha ce Tazo Ta Rumgumeta Itama Tana Kukan Farinciki,chan Bauchi Yusuf ya kira Zainab awaya ya Sanar Da Ita Yanzu aka Daura Aure,ai sai gida ya Rude da Murna,Maman Fati ko Daki Ta Shige Takai goshinta gabas Tana Kwararoma Allah Kirari daya bata Ikon Ganin Auren Ma'u Wanda Da Dade Tana Fata Da Buri.
Abdallah ko Tunda aka sanar An Daura Aure yaji kansa yamasa Nauyi ko jama'ar dake mikamasa Hannu Suna mai Murna yake kawai yakeyi jinsa yake Kamar bashi ba.

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now