Chapter 18

190 16 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KO DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI SAIWOWIN SANYI*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABARU*
*AKWAI SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI SAIWOWIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

          *🅿️18*

Hajiya ce tace "Bata ce mana tana sonka ba, mune muka ga dacewar hakan kuma muka zartar a matsayinmu na iyayenka.
wanda muke ganin muna da kima a idanuwanka muna da damar da zamu yanke duk wani hukunci akanka kuma ya zartu Abdallah, aure ne kuma dolenka ka karɓeshi bama buƙatar komai naka harta da muhalli mu zamu samar maka amincewarka kaɗai muke buƙata, in shima bazamu samu bane sai ka sanar damu." Ta ƙarishe cike da ɓacin rai.
Ido Abdallah ya kafa mata kafin ya sadda kanshi ƙasa, zuciyarsa ne tayi nauyi yama kasa magana ganin haka yasa Hajiya ta cigaba da faɗin "Nace zaka amince ne ko kuwa sai ka ƙara nuna mana iyakarmu a karo na biyu? Saboda kaga mun ɗaga maka ƙafa kana abunda kaga dama, wlhi Abdallah wannan karon indai ka bijirema umarninmu wlhi bazan taɓa yafe maka ba..." Ta faɗa tana tsiyayan ƙwallah.
Mallam ne yace "Ya isa Hajara, rabu dashi kinsan dai baki da lafiya don Allah ki bar tada wannan maganar.." Bata saurari Mallam ba, ta miƙe ta fice daga falon tana goge fuskarta da haban zaninta.
Ajiyar Abdallah ya sauke yana bin Hajiya da kallo jikinsa yana ƙara yin sanyi, cikin muryan kasala yace "Kuyi haƙuri Mallam na amince da zaɓinku Allah ya tabbatar da alheri.." Cike da murna Mallam ya washe baki yana faɗin "Masha Allah, naji daɗin maganarka Abdallah, Allah yayi maka albarka. tashi kaje kabama mahaifiyarka haƙuri tayi fushi da kai.." Miƙewa yayi jiki asanyaye ya fice zuwa shashen Hajiya.
Hajiya na zaune gefen gadonta tana tsiyayan hawaye Abdallah ya shigo ya daɗe a tsaye  yana kallonta hannunsa duka biyu suna zube acikin aljihun wandonsa, Hajiya taji shigowarsa amma saboda haushi ko ɗaga kanta batayi ta kalleshi ba.
Numfashi ya ijiye kafin ya ƙarisa gabanta ya durƙusa duka hanuwansa ya sanya ya riƙo hannuwan Hajiya yana kallonta kafin a hankali ya fara faɗin "Hajiya don Allah kiyi min aikin gafara ki daina kuka, na amince da abunda kuka zaɓa min.." Jin haka yasa Hajiya ta ɗago tana kallonsa haƙoranta duka awaje tace "Da gaske kake Abdallah..?" Kai ya ɗaga mata kafin ya samu zarafin magana Hajiya ta miƙe ta ɗagosa ta rungumesa tana saka mai albarka harda godiya kafin ta ɗagosa tana faɗin "Naji daɗin haka Baffa, na tabbatarma zaka ji daɗin zaɓin da muka yi maka, taso mu koma shashen Mallam mu cigaba da tattaunawa kasan abun yazo.."
Ta fada da murna tana yar dariya, tana riƙe da hanunshi har shashen Mallam ɗin, ganin Hajiya ta dawo tana dariya yasa Mallam ya fara tsokanarta da uwar Abdallah, itako tana dariya, nan Hajiya ta zauna ta tanƙwashe ƙafa tana ƙara zuzutama Abdallah kyawawan halayyar Asma'u, shiko yana zaune yana jinta sai dai yayi mata murmushin ƙarfin hali kawai, zuciyarsa bugawa take duk sanda ya tuna da Wasila, gaba ɗaya kanshi ya kulle bashi da yarda zaiyi ne, amma maganar gaskiya a tsarin rayuwarshi bayan Wasila wata mace bata burgeshi in ma auren zai ƙara toh sai dai ya ƙara da Polina don ko ba komai yanayin tsarinta yayi dai dai danashi, kuma sosai yarinyar take tafiya dashi.
Yana cikin wannan tunanin yaji muryan Hajiya na sanar da Mallam bata yarda Asma'u ta zauna a ko'ina ba sai cikin gidan nan, Mallam ne ya dakatar da ita da faɗin in akayi haka zasu shiga hakkinsu da yawa, kuma ko ba haka ba itama Asma'un baza ta sake ba duba da mahaifiyarta a gidan, hakama Abdallah sai dai cikin gidajensa dake GRA za'a duba ɗaya asaka Asma'un a ciki.
Duk da Hajiya bataso haka ba, amma maganar Mallam gaskiya ce, kuma tunda gari daya ne ana kusa, sai ta amince, shi dai Abdallah zuru kawai yayi musu bai ƙara saka musu baki ba, suma basa ambatonsa a ciki domin kamar yadda suka faɗa amincewarsa kaɗai suke buƙata, ko maganar lefe Hajiya da Mallam yaji suna maganar Safina da Hajiya zasu Kano su haɗo komai, saboda ko ance Maman Fati taje zatace bazata je ba.
Hirar bata tashi ba sai da aka kira sallar La'asar suka fita shida Mallam, koda suka dawo ɗaki ya shige ya kwanta saboda baya son hayaniya ga dagula mai lissafin dasu Hajiya sukayi.
Washegari nayi yabi jirgi ya koma bayan su Mallam sun jadadda mai yazo ɗaurin aure kuma yayi musu alkawarin zai zo, Hajiya kuwa kunnenshi taja akan kar ya kuskura ya sanarma Wasila komai sai daga baya, ya amsa mata da Toh, shima ai ba karan hauka ne ya cijeshi ba, don har yanzu asirin shakkar Wasila bai sakeshi ba, koda ya isa Portharcourt Office ya wuce sai dare ya koma gida bayan ya fara biyawa wajen Polina sun biya bashi kafin ya koma gida.
Wasila taji mamakin ganin Abdallah ya dawo kamar tayi ihu da tsalle saboda murna, tana ji a ranta ƙila aikin boka ne ya fara aiki domin dama gobe ne wa'adin boka zai cika, farin cikinta ya kasa ɓoyuwa ranar dai dole tasa Abdallah ya kusancenta domin tayi kewarshi sosai da sosai.

ZAMAN GIDANMU.Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum