Chapter 7

211 32 2
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866

CONSTIFREE* *(BARI IN BAKU WANI SIRRI NA WANNAN HADADDEN TEA DIN NAMU)*

*GASHI HADIN ITATUWA NE DA GANYENYAKI, GWANIN DADI IN KUNA SHA, ABUNDA DADIN* *SHINE BAYA TADA ULCER💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾*

*CONSTIFREE na abubuwa da dama kamar Haka....* 👇

🌹💃🏾 *Yana maganin Ciwon mara na al'ada ( menstrual pain)*

🌹💃🏾 *Yana wanko mara yayi maganin infection, natural detox ne*

🌹💃 *Yana maganin basir Mai tsoro*

🌹💃 *Yana magance constipation (kaje yin toilet ka kasa kayita fama bayan gida na damunka a ciki)*

🌹💃  *Yana taimakawa sosai wajen rage kiba da tumbi...💃💃💃*

💃🌹 *Yana taimakawa wajen magance duk wata matsala ta hanji cikin yardar Allah...*

💃🌹 *Constfree na magance duk wani datti na cikin ciki Koh mahaifa*
*(Misali wasu zakuga ance sunada blookage a ovaries nasu Wanda yake hanasu daukar ciki)*

💃🌹 *Constfree nasa kyan fata ta zama gwanin burgewa....*

✔️ *Constifree ..na magance prob na Fabriod*

*Maza ku garzayoo domin mallakar naku💃🏻💃🏻💃🏻 Price 12k Muna Bada Rabi*

Mmn MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866

                *🅿️07*
      
Bikin Aisha da Fahad ya rage Saura Wata Hud'u aka sanyama Fa'iza Rana wata bakwai Wanda lokacin yayi Daidai da tagama Candy Dinta.
wannan karon Ban hana kaina kuka ba, Domin inaji ina gani agidanmu sai karewa ake ana barina.
Dama mu uku ne muke kwana ad'aki daya ni da Fa'iza da Rabi'a. Su Maryam d'akin Mama Suke kwana don daga ita har ya'yanta basu Cika shiga Shirgin yan gidanmu ba yadda kasan Suma ba ya'yan gidan ba ne.
Ba laifi Fahad yana da Rufin ASirin Domin ma'akaicine A Hukumar Nepa. shiyasa akayi komai Cikin Wadata a ka yi sa. Lokacin da bikin ya kariso Duk sai Aisha ta zabge ta rame kamar ba ita ba,haka itama Asma'u Suna jimanin Rabuwa da juna Saboda sanin yadda Suka Shaku. ammh babu yarda zasuyi Tunda haka Allah ya kaddara.
Tun ana Saura Sati d'aya biki Na nesa dana kusa suka Fara Cika gida. Mamana Tazo Ana gobe biki tazo da Tsohon cikinta Haihuwa ko yau ko Gobe, Murna wajen Asma'u ba'a mgana ganin yadda Mamana tayi kyau Sosai dagani ta samu kwanciyar Hankali ita kuma ganin yarta ta Sai Tsausayin ta yakamata sosai. na ganin yadda zatasha kewa in Aisha Tatafi ta barta.
Ranar biki komai Tare Suka sanya Aisha da Asma'u Domin hatta ita Sai Da Fahad yama kaya kamar wacce zai aura saboda sanyayama Aisha Zuciya, Tun da Suka ga yammah tayi suka Fara kuka kar Aisha taji lbri koda motocin Daukan amarya Suka zo Aisha bata yarda hannunta ya Rabu Dana Asma'u ba har aka kaita Dan madaidaicin gidanta dake GRA.
Kuka da Tashin hankali bai Faru ba sai da  Asma'u zata bi yan kawo amarya Aisha ta kamkameta tana kuka,duk yadda Asma'u taso Daurewa Abun ya gagara itama kukan Ta Fashe dashi. Ganin Sunki rabuwa da juna yasa aka bar Asma'un anan Sai da angwaye suka zo suka Siya baki kana Suka Wuce da Asma'u Suka Sauketa agida.
shi kanshi Sai da Asma'un ta ma Aishan Dubaran Zata Shiga Bayi ne ta Fito sai dai  ta waiga taga batanan, Ranar Fahad yaga kuka,kuma yakara Jadadda kaunar dake Tsakanin kawayen Biyu.
Auren Aisha shi yakarama Asma'u  zaman kad'aici da kuma zaman gidansu Tunda yanzu bata zuwa mkranta. kullun Cikin yad'a mata Habaici Umma keyi ita da Hajiya Iya ba wajen wanda take samun mgana mai Dadi sai Wajen Anty Amarya, sai Baba lami da hassatu sabbin masu aikinsu. dayake Suna da kirki Sosai,mama ko dama ban da gaisuwa babu Abunda ke Shiga Tsakaninsu daga ita har ya'yanta.
Tun bayan Abunda ya faru ni Asma'u Nayi alqawarin bazan kara kula kowani  Namiji ba,ammh kuma ya zan yi domin Zaman gidanmu na neman ya Fita kaina. Kwatsam sai ga Ishaq ya Shigo cikin Rayuwata wanda kai Tsaye wajen Abbana yafara Zuwa Neman izini Shi Abban da kanshi ya kirani yana Fad'amin. ban yi gardama na karbi ishaq tare da addu'ar Allah ya sanya Shine mijina,Shima yana da Abun hannunshi Domin ma'aikacin banki ne,haka nake Duka jinin samarina masu dashi ne. Aisha dataji lbri kamar ta Zuba Ruwa kasa tasha saboda Murna har gida na Kai musu Ishaq suka gaisa da Fahad.

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now