Chapter 24

182 24 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

 Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you covered

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price. 

 
           *🅿️24*

Bata fi Minti Goma Sha Biyar Da Tsayuwa ba, Sai ga Motar Abdallah ke ciki Bakar pradonsa Tana Slow Daga Wajen get din Asibitin Sakamakon Gabadaya Tinted ne shiyasa Bata Iya gane Su waye Aciki ba.
a gabanta Suka Faka Motar Lokacin Da Abdallah ya Tsura mata ido Ta Cikin Motan yana Kare Mata kallo Kamar Wani Tsahon maye. Kallon farko ya ganeta Saboda yadda Komai Nata ya Zauna akwakwalwarsa Shi ya Umarci  Emeka da ya Tsaya agaban Asma'u batare Da Ita Ta Fahimci Shine Ba.
Tana Faman Waige Waige Taji Wayarta Na Ringing ganin Nombar Dazu ne Da Abdallah ya Kirata Dashi ya sanya Ta Daga kafin Takai ga Mgana yace"Muna kallonki Ki Shigo bakar Motar Data Faka agabanki yanzu.." Haka Kurum ya Fad'a ya yanke Kiran, sai a Lokacin ta Lura Da Bakar pradon Dake Fake agabanta, Gabanta ya Buga Ras shiko yana Ta Ciki yana Kare Mata kallo Tunda ga Sama Har Kasa zuwa bakin Combos din Dake Kafarta ba'a ganin Farin Hijabin Dake Jikinta sakamakon Ta Sanya Wani Purple din Hijabin Gida Wanda ya Sauko Mata Har Zuwa gwiwa
 Jikinta asanyaye Tafara Takawa Kusa da Motar, Emeka Dake Ciki yayi Saurin Fitowa Daga Mazaunin Direba Ya Washe Baki Rankwafa yayi yana Fadin"Gud mrning Madam.."Kallonsa Tayi Cike Da Mamaki Bata Samu Zarafin Mgana ya Bude Mata Gidan Baya Inda Abdallah ke Zaune, Batayi gardama ba Ta Daga kafa Ta Shiga Motar Shi Kuma ya Maida kofa ya Rufe kafin ya Bude Kofar Mazaunin Direba Ko kafin ya Daidaita Zamanshi yaji Muryan Abdallah na Fadin"Emeka Wait me Outside ..."Bai yi gardama ba Emeka ya Bude murfin mota ya Fice yana Fadin'Ok Sir."
Fita yayi ya gangara Gefen Asibitin Ammh Acikin Ransa yana Tunanin Kodai Itace Matar Nashi da Sukayi Ta Mganarta da Madam polina Wacce Tace Da Zarar Abdallah ya Dawo ya Sanar Da Ita Bayan Ta bashi Phone Number Dinta, Emeka baiyi Sanya ba Ya Fito da Wayarsa ya Kira polina bayan Ta Daga kiran Suka gaisa nan ya Labarta mata Komai Game da Dawowar Abdallah da Inda ya Sa su Suka Taho Wajen Wata yarinya.
Farinciki ya Cika polina Ko Bata sani ba Itace Matar Tashi Asma'i kuma ga Duk Alamun Sunyi Nasara Abdallah Zai Kusanci Matarshi, Saboda Murna Polina Tace Emeka ya turo mata account Nombarshi Zata Sakamai Kudi,Nan Suka yanke Kiran yana Ta Zubamata godiya.
Asma'u ko Tunda Ta Shiga Cikin Motar Bata Dago Kanta ba Tun bayan Dataji Muryan Abdallah agefenta, Kanta na Kasa Tana Wasa Da gefen Hijabinta Shiko Abdallah Idanuwansa Suna kanta Ji yake Kamar ya Jata Jikinsa ya Ciremata kaya yafara aiki ammh Sai ya Barsa ya Danne Abunda Ke Damunshi Cikin Muryan Kasala da Barci ya Furta"Kina lafiya...?tunda Baki iya gaisuwa ba."
Asma'u Taji Kunya Muryanta Na Rawa Tace"Yi...yi Hakuri ina Kwana..? Bai amsa ba Illah kallonta dayake yi Kafin yace"Kin makaro sai da Na Roka..."Yafad'a yana Fitar da Iska Daga Bakinsa,Rausayar Dakai Asma'u Tayi Kafin tace"Allah ya baka Hakuri." Kansa ya Jinginar Cikin Kujeran Motan yana kallonta Cikin Wani Yanayi kafin yace"No ya Wuce,..."Yafada yana lunshe Ido Cike Da kasala.
Sun kusa Minti goma ba Wanda yayi ma Wani mgana, Shi yana Aikin Kallonta da Kuma lumshe Ido Ita Kuma Kanta na Kasa,ammh Fargaba ta Cika mata Zuciya Tana Ciikin Wannan Halin ne bata da Kwanan Amin Taji Tattausan Zaratan Hannunshi Cikin Hannunta,Wanda Take Wasa Da gefen Hijabinta Dashi.
Yam! Taji Lokaci Daya Jikinta ya Dauki Ruwa Cikin Fitan Hayyaci Ta Dago Tana kallonshi Inda Shima ya sakarmata Ido Wad'anda Suka Chanza Launi Zuwa Jawur.
Cikin Wani Salo yayi Lum da Idanuwan nashi Kamar me maye,da Hanzari Asma'u ta Janye Idanuwanta Jikinta Na Rawa, shiko Duk yana lura da yanayinta ganin yadda Ta Firgitane yasa ya Hada yatsunsu Waje Daya Ya Matsewa Har Sai da Asma'u Taji Zafi Ta Saki yar Kara Tana Kallonshi Abun Mamaki Idanuwansa Suna Lumshe kamar mai barci fuskarsa Take Kare ma Kallo mai Cike Da Zati Da Haiba sai Sajensa Wanda Ke karamai kyau da Haiba Afuska Yayi Rama Duk da Ba Wani Kallon Sosai Tamai agidan Hajiya ba.
Tunanin ta ya Katse ne ,Sanda Taji Ya kira Sunanta Cikin Muryan Amo Da Muradi mai Girma.." ASMA'UL HUSNAH!!!!..." Yafad'a yana Jan Sunan nata,Wanda Sai da Jikinta ya amsa,Cikin Wani yanayi Ta Dago Tana Kallonshi Idanuwanta Sun kawo Ruwa Saboda Yanayin Datake Ji acikin Jikinta.
Kurama Juna ido Sukayi Cikin Fitan hayyaci Kowane Naso yagano Wani Abu Acikin idanuwan Dan'uwanshi, Asma'u Taji Bazata iya jurema kallon Ba Ta Janye Idanuwanta Tana Kara Bin Hannuwansu Dake Sarke da kallo, Abdallah ya Lumshe ido kafin ya Bude yana Fadin"Husna Wani Taimako nazo Nema awajenki Duk da nasan Laifina bakai ki kalleni ba ammh ammh Kiyi Hakuri ki Saurareni Domin Bayanke Babu Wanda Zai Iya Fitar Dani Daga Halin Dani ke Ciki." Yafad'a cikin Muryan kasala Daga Karshe Muryansa Ta Shake Kamar me Mura
Asma'u bata da Wata Natsuwa Tayi Jarumtar Cewa"Bakomai ka Sanar dani Allah ya sa Ina da Abun Taimaka maka kamar yadda Ka Fad'a.."Mirmishi ya saki kafin yace"Kina dashi Husna. Ke nake so  Ma'ana Hakkina Nazo karba Awajenki Amtsayina na Mijiki ."Yafad'a Cikin muryan Amo Da Haiba.
Da Sauri Asma'u Ta Kalleshi Tana Waro ido Cikin Fitan Hayyaci Tace"Kaina Kuma...? Tafad'a Hawayen Dake Idonta Suka Zubo mata, Matse Hannunta yayi kafin ya marairaice yana Fadin"Plz Husna Don't Say No, Don Allah ki Ceceni kimin Rai Wlh In ban Kasance dake ba Yau Zan iya Mutuwa.."Yafad'a Muryansa Tayi Sanyi kamar yayi Kuka, Lokaci Daya yana Dora Hanunta Bisa Kirjinsa da Ke Bugawa Da Karfi
Ganin Taki mgana yasa yayi Kasa Acikin Motan yana Riko Duka Hannuwanta Yana Fadin"Plz My Husna...Don Allah Don Darajan iyayenki Nasan Ke Yarinyace Mai Tarbiya Wlh baki Dace Dani Ba Allah ya Dubeni Ba Don Halina ba yabani ke, ki kalleni ban Rasa Komai na Fannin Jin Dadin Rayuwa ba Husna buh nasan kin sani bana iya Ma iyayena biyayyah, suna Bukata ta suna Son kasancewa Tare Dani ammh Na kasa yimusu Abunda Sukeso Bansan Dalili ba Husna Tell me plz Tell me me ya kamata na yi ?"Yafad'a Lokaci Daya Hawayen Dake Cikin Idanuwansa Suka Zubo.
Asma'u Tagama Rudewa da Rokon Da Abdallah yakemata akan Abunda yake Mallakinshi ne, Kalamasa na Karshe Sun Sakata kara jin Zubowar Hawayenta Cikin Fitan Hayyaci Ta Durkushe gabansa Tana Fadin"Is ok. don Allah kadaina Kuka meyasa kake Rokona Akan Abunda yake Mallakinka,?Na Amince Kayi Duk yadda Ka keso Dani Har Abada Bazan Zama mai Gardama agareka ba" Ta karishe Cikin Kuka.
Abdallah Da yayi Sagale yana bin Asma'u da Kallo Jin Ta Amince yasa Ya Kaimata Wani Wawan Rumguma daya Kusa Dauke Numfashin Ma'u Fadi yake "Tanque Husna.. Allah yayi Miki albarka.."Lafewa Tayi ajikinsa Tana Jin Bakon yanayi Da ita ajikinsa ya dago ya Zauna kan kujera kafin ya Zaro Wayar sa ya kira Emeka, jin Oga yace ya Taho yasa yazo Da Gudu ya Shiga Bangaren Direba Abdallah na Rumgume Da ita yace ma Emeka.."Plz in kaga wani Hotel anan hanya ka sanar dani..!
Da Hanzari Emeka yace"As uWish Sir..."Daga Haka Ya Tada Motar Suka Fara Tafiya Asma'u na Kwance Bisa Kirjin Abdallah Tana Shakan kamshin Turarensa Shiko ya Matseta gam yana Shafa Kanta Zuwa bayanta Cikin Yanayin Sauke Numfashi Kamar Wanda yayi Gudun Tsere.
Basu yi Tafiya mai Nisa ba Emeka yaci karo da Wani Hotel mai Suna three Star Hotel cikin girmamawa ya Tsaya yana Sanarma Da Abdallah shikuma yace Su Shiga Ciki, suna Shiga Ciki saboda yadda yake Rage Zafi da Jikin Asma'u kuma baisan Katse Kansa sai ya bama Emeka Atm dinsa yace ya Shiga Ciki yayi Musu Buking din Daki,Nan da nan ko ya amsa ya Shiga Ciki Da Hanzari Cikin Minti goma sai gashi ya Fito Ya kwankwasa Glass din Motar Inda suke Ciki, Bude Kofar Abdallah ya yi lokaci d'aya ya na Zuro Kafarsa Asma'u na Jikinsa tana kokarin Kwacewa yana kara  Riketa Da Ita ya Fito Rike Da Ita Kafin ya Karbin Key din Dakin Had'e da Atm dinsa a Hannun Emeka.
Asma'u sai Lokacin Ta Fahimci A Inda take,gaban tane ya Fadi Acikin Ranta Taji Wani Iri,Shikenan Ita Kuma Nata kimar Atiti Za'a Karbeshi Atitin ma cikin Hotel.
kawai Sai Taji Hawaye Sun Kawo Mata Tunanin Ta yakatse ne Sanda Abdallah yaja Hannunta yana Fad'ama Emeka.."Wait me Here." Kai Emeka ya Gyada kafin ya Koma Cikin Mota ya zauna yana Hange Abdallah da Asma'u Sun Shige Cikin Hotel din.

******
Wasila Kuwa batasan Abunda Ke Faruwa ba, don bata Dawo Daga Inda Taje ba Sai Dare,Wajen Shakatawa Taje kafin Taje Wani Restaurant Taci abinci Tayoma Abdallah Take away, sai Kuma Ta biya Wani Katon Kati Ta Siyo musu Chaculate da Sauran Tarkacen Ciye Ciye.
Koda Ta Shigo agajiya Take, Wanka Kadai Tayi Ganin bataga Abdallah ba Sai Bata Damu ba, Atunaninta yaji Sauki jikinsa ne Ya Fita Yasha Iska Tasan Zai Dawo Ba Dadewa zai yi ba. A daddafe ta Rama Duka Sallolinta na Ranar Domin Remix take Kamar yadda Takoyama Abdallah ko yacemata bari Yayi sallah Lokaci Yayi Sai Tace"A'a ya bari Su koma gida, Ahaka zasu yi  ta Gantali Sai Dare bayan Sun Koma Gida Su Ramka Lokaci Daya.
Tana idar Da Sallolin Ta Sanya kayan barci Ta Haye gado,sakamakon agajiye Take Shiyasa Bata Dade Ba Wani Nannauyan barci Ya Tafi Da Ita, ba ita ta Farka ba Sai Da Gari ya Waye,Wasila Taji mamakin Rashin ganin Abdallah Kwance Kusa Da Ita sai Tayi Tunanin kodai ya Dawo yana Tiolet,sai dai me Saukowanta Daga kan gadon da ledan Data yimai Take away Taci karo.
lokaci Daya Kuma Zuciyarta ta Shiga Tsinkewa A Tamanin Ta Nufi Tiolet Ta Tura Wayam Babu Abdallah.
Wasila Ta Rude Ta Dawo Daki Da Hanzari Ta Lalubi Wayarta Ta latso Nombar Abdallah ammh Kuma akasheta Tajita Zuciyarta Ta Shiga Gudu Nan da Nan Ta Shiga Had'a Zufa,Attachement Din Kanta Taja Tana Tambayanta Kanta.."Abdallah Where are u...? Take Fada Tana Daga wata Shegiyar Rigar barcin Dake Jikinta mai kama Da Kafin ka Tsirara.
  Ganin bata da Amsa ne yasa Ta Koma gefen gado Ta Zauna Tana Kara Kiran wayar Abdallah ammh akashe Zuciyarta Tafara bata Wani Tunanin Kodai Abdallah ya Dawo Cikin Hayyacinsa aikin Datayi Akanshi ya Lalace ya Gudu ya barta.."Jin Wannan Tunanin yasa Ta Mike Jikinta na Rawa Ta Nufi karamar Jakarta Dake Side Drower Inda passport dinsu yake,Jikinta Har Rawa Yake Wajen Zazzage Jakar,Abunda ya Kusa Hautsina ya'yan hanjin Wasila Ganin Datayi Babu pasport din Abdallah Sai Nata Kuma Babu Katin Cire Kudi na Asusun Bankinshi na First bank..
Fahimatar Haka da Wasila Tayi yasa Ta Dora Hannu akai Tana Fadin"Is not True...never it can be happen..."Take Fad'a Cikin Tashin Hankali,bata Tsaya Neman Abunda Zata Suturta jikinta ba Ta  Fice Daga Dakin Kamar Zata Kifa reception Taje Tana tambayan Wai Da Yaushe Abdallah ya Fice,da Taga basu gane ba ,sai ta Shiga Cikin Wayarta Ta Nemo Hoton Abdallah nan ma Ido Suka sakamata Don basu gane Me Take Nufi ba,Wasila kamar Ta Zare Haka take bin Turawan Wajen Tana Nuna musu Hoton Abdallah kamar Zararriya ganin babu Mafita yasa Ta Koma Cikin dakin Nasu Ta Sanya Wata Doguwar Riga Ta Zari Jakarta da pasport dinta ta Fice Daga Hotel din don yanzu Hakika Zuciyarta Tagama yarda Da Aikinsu ya Lalace Abdallah yakoma Nageria bada Saninta ba.
Sai dai me Wasila na Zuwa Airport din Jahar Ta tarar da Wani Tashin Hankali Domin An Rufe kowani iyakokin Kasar Na paris Da Kuma Duk Wani Filin Sauka Da Tashi na Jirage Saboda Wata Rigima da'aka Tashi Da Ita Asafiyar Ranar,Babu Shiga Babu Fita,Hannu Wasila Ta Dora akai Tana kwarara ihu. Toh Dayake Gari ne na,Turawa babu Ruwan Kowa Fa Da Kowa yadda kukasan Ba aganta ba Wanda yabi Ta kanta balle ya Tsaya Kallonta.
Haka taja Siraran kafafunta Ta Koma Masauki Tana Sharban Kuka,Tana kuma Cike Da Fargaban Gargad'in Boka na Kada Tabari Abdallah ya Kusanci Wannan Matar Tashi.
  Tana Komawa Ta Shiga Kiran Nombar wayar Momcy ammh Wani Ikon Allah Taki Shiga Tayi Tayi Ammh Ina Waya Taki zuwa, ta maida akalan Kiran kan Wayoyin Su Jamila Da Hafsat nan ma Shuru Kakeji Saboda Tashin Hankali Harsu samuel Ta kira Bata samu Abu kamar Tsafi Daga karshe Jifa da Wayar Wasila Tayi Ta Kwanta akasa Tana Ihu Da Kuka Fadi Take"Na Shiga Uku Ni Wasila...Ya Allah kasa Kada Abdallah ya Kusanci Tsinanniyar yarinyarnan..."Take Fad'a Tana Sharbe Kuka Kamar Wanda akace Uwarta Da Ubanta Sun Mutu cikin Lokaci Kadan kamaninta ya Chanza Saboda Tashin Hankali Da Fargaba.

******

Abdallah na Rike Da Hannun Asma'u Wacce Ke Binshi cike Da Tsoro da Fargaba Har Dakin Da Emeka ya kama musu mai Lambar 123 yana sama ne So Sai da Suka Hau Benan Wajen,Suna Zuwa Kofar Dakin Abdallah ya Zura Makulli ya Bude Suka Shiga Ciki ya Maida Kofar ya Kulle Harda Makulli ya Juyo yana,kallonta Lokaci Daya yana Sakarmata Mirmishi.
Kafin ya sanya Hannu ya Jawota Jikinsa yana Kamkameta Lokaci Daya Kuma yana Tafiya da ita Zuwa Gadon Dake Dakin Hotel din .
Asma'u ko ba Inda Jikinta baya Rawa balle Da taji ya Zaunar Da ita gefen Gadon yana Rumgume Da Ita Lokaci Daya Kuma yana Kokarin zare Mata Hijabin Jikinta Hade Da Jakar Hsnnunta, Bata da yarda Zatayi Tana Ji Tana Gani ya Ciremata Hijabin Da Jakar ya Ijiyesu Gefe Da Wani mayen Kallo Ya bita Cikin Fitan Hayyaci Kirjinta ya Tura ma Ido kafin ya Zura Hannu Saman Wuyanta ya Zare Mata karamin Farin Hijabin Dake Jikinta,Ajiyar Ma'u Ta Sauke Jin Yadda Kallon Abdallah ke Bin Kowani Sassa Na Jikinta.
Jikin Asma'u ba Inda bai Rawa Ganin yadda Abdallah ya Rude yana Rud'ata da Zazzafan Romance, bakinta kuwa kamar Zai cinye Saboda Tsotsa,Yadda yake tsotson ne Had'e da Fargaba ya kamata batasan Sadda Ta Saki Jikinta Ba Har Sai da Taji Abdallah ya Zare Farar Rigar Dake Jikinta.
Daga Lokacin bazata iya dora komai ba Domin bata cikin hayyacinta abu daya ta sani yau din Abadallah ya maidata ita cikakkiyar matar aure.



*Janafty*

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now