Chapter 28

231 23 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you covered

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.

               *🅿️28*

Da misalin ƙarfe 2pm na rana Suka sauka a filin jirgi na Portharcourt  international Airpot, suna sauka  Abdallah ya kira Emeka yace Yazo ya Daukesu,Ba gaddama Emeka yazo ya Daukesu yana Faman Washe baki Domin yaji Dadin Dawowar ogan nasa
Basu Dauki Lokaci ba Suka Iso Kofar Tamgamemen get d'in Gidan Abdallah Ma'u sake baki Tayi Tana Kallon Gidan da Anguwan Gabadaya ko'ina Tsit kamar Babu Mutane sai dai Kowani Gida yana Kamgame da Katon get kamar ba Mutane Aciki Hon Emeka ya Zuba Megadi yazo ya Wangale musu get Emeka ya Sulala Da Motar ya Daidaita Mata Zama aparking Space.
Asma'u ya Mika ma Hannu Takama Suka Fito Daga Motar bayan Emeka ya Bude musu Kofar Motar  Megadi ganin Abdallah yasa ya Rugo yana Mai Barka da Zuwa Hannu kadai ya Dagamai batare Dayayi mgana ba yana Karema Haraban Gidan Nashi Kallo Cikin Wani yanayi Wanda Yakasa Fassarashi Kallonsa ya Koma Kan Ma'u Wacce Take Wurga idanuwanta Acikin Farfajiyar gidan,Hannunta Dake Cikin Nashi ya Matse Kana tasaki ajiyar Zuciya tawaigo Tana Kallonshi gira ya Dagamata yana Fad'in"Perfect ko..."?
Mirmishi Ta saki kafin Ta gyad'a kai Da ido ya Nuna mata Wani Flat mai kyau Dake Gefe yana Fadin"Ga Shashenki kallah ki gani..."Daga ido Tayi Tana Kallon Katon Flat din Mirmishin Jin Dadi Ta saki kafin tace"Wow. So Nice Yaya Abdallah..."Dariya ta bashi ya Rumgumota yana Fadin"do u like it hmm..? Kai ta Gyadamai ta na Sunne kai kan Kirjinsa  tana Fadin"yana da kyau infact ma Gidan Gabadaya ya hadu kana da gida mai kyau." Kiss ya sakarmata Akumatu kafin yace"Ok Let go in First..."Yafad'a yana Riko hannunta lokaci Daya Suna Nufar Sashen da Zai sadasu Da Babban Falon gidan.
Akwatinta Emeka ya Fito Dashi Abdallah Da Hannu, yama Emeka mgana Da Hanzari ya Dauka Zuwa bakin Shashen Daya Fi ko'ina Ahad'uwa agidan.
Wasila na Zaune A kasan Cafet din Dake Falon Ta Zabga Tagumi In ka ganta bazaka ganeta ba Saboda yadda Takoma Ta Rame Ta Kwarzane kamar Wacce ake diba Ana miya, Tana sanye da Wata Doguwar Riga Mai Sharashara,Rayuwa ta Juyama Wasila baya Ammh Duk da Haka batasan Annabi ya Faku ba, Babu Mota balle Ta Koma Gidan Boka Kudin Dake Hannunta tagama Kashesu Duka Babban Tashin Hankalinta ga Store Abude ammh Bata iya sarrafa Komai ba Banda Ruwa Babu Abunda Take sama Cikinta ga Momcy Bata samunta awaya balle Ta sanar da Ita Halin Data ke ciki, Duk da Ko Tasan Itama Momcy Tana Chan Cikin Wani Hali ammh Bata damu  ba Indai Zata Samu Damar Kowama Wajen Sabon Bokanta na Maiduguri Ta Sanar Daahi Haryanzu Fa Shuru Abdallah baizo Gareta ba.
Babban Tashin Hankalinta Ciwon Hafsat Domin yanzu Abun Yayi Tsanani Dakyar Take Numfashi Rayuwa na Reto balle Jamila da Ciki ya Ramar Da Ita ba kudi balle Ta kaisu Asibitin Kullum basu da aiki sai Kuka, Ammh baisa Wasila Ta Saduba ba Sai ma Karfin Gwiwan da Wata Zuciyarta Ke Sanar da Ita Cewa Soon Abdallah Zai Zo Gareta.
Dama  already  gidan Abdallah yana Dauke da 2 flat ne cikin gidan, ɗayan filat ɗin yafi kyau da tsaruwa da komai da komai a ciki, sukan ɗan shiga shida Wasila su ɗan shaƙata wani Lokacin Ammh Wanda Suke Ciki yafi Girma Dat Why Suke Zaune anan,makullin ɓangaren yana hannunta, TuntuniTun Lokacin Data Ke Jan Ragamar Rayuwarsa.
Yana riƙe da hannun Asma'u suka shigo falon Wasila dake zaune ta rabga uban tagumi taji sallama kamar Daga sama Kuma Ta Tsinkayi muryan Abdallah mai Cike da Zati Wanda Ko Mutuwa Tayi Tatashi Bazata Taba Mantawa Da Ita ba.
miƙewa tayi da Sauri Tana Kallon Abdallah Dake gaba, Ma'u  na bayansa,Murza idonta take Tana So Ta Tabbata da gaske ne Ko Tunanin Data Sabayi ne na Taga Abdallah yazo Gareta. Still Shidin ne Tsaye yana Kallonta Cikin Wani yanayi Wanda Yakasa Fassarashi,da mugun gudu Wasila Ta Nufi Abdallah Tana Zuwa Sai Taci Burgi agabanshi, rirriƙeshi tayi tana Fadin "Dee ashe zaka dawo gareni...?" Ta Fad'a cikin Fitan Hayyaci tana Fadawa Jikinsa Lokaci Daya Tana  ƙara ƙanƙameshi, yatsina fuskarsa yayi ya ɓamɓareta daga jikinsa ya miƙa mata hannu yana Kallonta Cikin Bakin Ciki Da Takaichi  fuska a ɗaure yace "Bani makullin Second Flat dina..."
galala kawai ta tsaya baki buɗe tana kallonsa, a hasale ya daka mata tsawa yace "Nace ki ɗaukomin  makullin oder Side Ki bani Karki Batamin Lokaci..." yafad'a yana Watsa Mata Wani Mugun Kallo.
Ma'u Dake Gefe Tana Binsu da Kallo Expecially Wasila Wacce Tamata kama Da Arnan nan masu Tallah Abinci Abakin Tasha.
A hankali  wasila ta juya jiki a sanyaye tafara Haura Steps Tana Hawaye Jikinta ba Inda baya Rawa, taje ta ɗauko makullin ta bashi, ta buɗe baki zata fara mai magana kenan ya dakatar da ita, sai a lokacin hankalin Wasila ya kai kan Asma'u dake tsaye tana kallonta.
Wasila tana ganin Asma'u zuciyarta ta fara harbawa ta kalli idanunta lokaci ɗaya tsoronta ya shiga ranta, taji kawai tana shakkar kallon idon yarinyar.
tana tsaye yaja hannun Asma'u suka  Fita taga Ko Inda Take Bai Kara Kalla ba,hannu Wasila Ta Dora akai Tana Fadin"yesu.Meyake Faruwa ne..? Wacece Wannan Tare da My Dee...? Wata Zuciya Tace Matarshi mana"  Ihu Ta saka Tana Dukan Kanta Kamar Wata Mahaukaciya Kan Cafet din Ta malale Tana Fadin"Na Bani na lalace Ni Wasila...oh god Help me.."
Makulli Abdallah ya sanya ya buɗe Kayattacen Flat din, suka Shiga yana Rike Da Hannu Asma'u emeka Kuma na Bayansu Dauke da akwatinta, Ko'ina Neat Dai dai Kura kadan, 2 bedroom ne da Kichen Ammh Komai na Bukatar Rayuwa Akwai Acikin Shashen.
Santi Kawai Ma'u Keyi Abdallah na Mata Dariya Kwabewa Tayi Tafara gyara Falon Tana Fadin Abdallah ya sama musu Abinci Tana jin Yunwa, amsa mata yayi da Toh kafin yayi Kissing dinta agefen Kumatu ya Fice yana Kiran Emeka.
Da Hamzari Emeka ya Taho Kudi ya bashi bayan ya Bashi Umarnin yaje Restauranta yayo Musu Takeaway, Karba yayi Yana Fadin"Ok Sir...",Har Abdallah ya Juya sai Emeka ya Kira"Oga..."Waigowa Abdallah yayi yana Fadin"What...? Hannu ya Emeka yasaka a alijuhun Wandonsa ya Fiddo  Takarda Cikin Emvalop,Hade da Key din Gida Dana Mota ya Mikama Abdallah Kin karba yayi Fuska Ba Annuri yake Fadin"i said What is dis..? Kan Emeka na kasa Yace"Is From madam Polina..."Shuru Abdallah yayi yana Nanata Sunan Polina kafin ya Karbi Takardan Jikinsa yayi Sanyi Duk dama yana Da Niyyar Zuwa Wajenta Ya sanar da Ita Cewa yabar Sabon Allah Har Abada.
Maimakon ya Koma Cikin Falon sai yaja Karamar Farar Kujera ya Zauna akai yana Bude Emvalop din keys din Suka Fad'o da Mamaki yake Binsu da Kallo yadaga yana Dubawa Tabbas Wannan Key din Gidan da polina ke Ciki ne wannan Kuma Key din Motarta ne Mamaki ya Cikashi,Cikin Hanzari ya Farke Takardan ya Ci karo da Rubutun polina yafara Karantawa Abayyane..

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now