*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty**MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866
CONSTIFREE* *(BARI IN BAKU WANI SIRRI NA WANNAN HADADDEN TEA DIN NAMU)*
*GASHI HADIN ITATUWA NE DA GANYENYAKI, GWANIN DADI IN KUNA SHA, ABUNDA DADIN* *SHINE BAYA TADA ULCER💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾*
*CONSTIFREE na abubuwa da dama kamar Haka....* 👇
🌹💃🏾 *Yana maganin Ciwon mara na al'ada ( menstrual pain)*
🌹💃🏾 *Yana wanko mara yayi maganin infection, natural detox ne*
🌹💃 *Yana maganin basir Mai tsoro*
🌹💃 *Yana magance constipation (kaje yin toilet ka kasa kayita fama bayan gida na damunka a ciki)*
🌹💃 *Yana taimakawa sosai wajen rage kiba da tumbi...💃💃💃*
💃🌹 *Yana taimakawa wajen magance duk wata matsala ta hanji cikin yardar Allah...*
💃🌹 *Constfree na magance duk wani datti na cikin ciki Koh mahaifa*
*(Misali wasu zakuga ance sunada blookage a ovaries nasu Wanda yake hanasu daukar ciki)*💃🌹 *Constfree nasa kyan fata ta zama gwanin burgewa....*
✔️ *Constifree ..na magance prob na Fabriod*
*Maza ku garzayoo domin mallakar naku💃🏻💃🏻💃🏻 Price 12k Muna Bada Rabi*
Mmn MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866
*🅿️06*
Alhaji Ladan Sharif Mai Auduga Shine asalin sunan mahaifin Asma'u. wanda haifaffen garin babban birnin jihar Jigawa ne wato jigawa Dutse. ya samo asalin laƙabin Mai Auduga ne sakamakon tun yana matashi yake manominta. ya gada ne shima a wajen mahaifinshi, dan da ita aka sanshi har kawo yanzu, domin itace rufin asirinshi, Alhaji Ladan baiyi karatun boko ba sai na addini, sai daga baya ne kana suka shiga makarantar yaƙi da jahici.
Mahaifinshi ya rasu sai mahaifiyarshi mai suna Hauwa'u wacce ake kira da Hajiya Iya, ya'yansu goma cur na da suka haifa kuma babu wanda ya koma duka suna nan da rayuwarsu. kai tsaye bazaka kirashi da mai kuɗi ba, amma za'a iya sakashi cikin sahun masu kuɗin dake zaune a unguwar Gida Sittin dake garin Dutse.
matarsa ta farko mai suna Mandiya wacce ake kira Ummah auren zumunci akai musu, Mandiya irin matan nan ne masifaffu, ga son abun duniya ga ƙyashi, ba laifi itama mahaifinta ya mutu ya bar musu tarin dukiya. shiyasa Hajiya ta matsa kan sai mahaifinta ya aurota domin Hajiya Iya itama akwai son harka da masu dashi.
Shekaransu biyar da aure har tayi haihuwa biyu 'yarta ta farko itace Aunty Ruƙayyah, sai mai bi mata Aunty Bilki, tun a lokacin yaso ƙaro aure. saboda yana ƙaunar Allah ya bashi ɗa namiji domin shine duka burinsa, sai Hajiya Iya ta hanashi, badan yaso ba ya bar maganar, kuma tun daga kan Aunty Bilki sai haihuwa ta tsayama Ummah cak bawai don ta gama ba sai don haka Allah ya tsara mata.
Zuwanshi Bauchi wajen harkan sana'rsu ta Auduga achan ya haɗu da mahaifiyar Asma'u wato Habiba, kuma tunda ya ganta ALLAH ya ɗora mai sonta baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nemi gidansu kuma ya gana da mariƙinta wato wan mahaifinta, domin lokacin Allah yayi ma mahaifinta rasuwa ba tare da jin ta bakin Habiba ba aka bada aurenta ga Alhaji Ladan. duk da ko da taji ba taji daɗi ba, amma bata nuna ba sai ta sadda kai tayi biyayyah ga iyayenta aka sanya ranar aure akayi biki aka ɗauketa daga Bauchi zuwa Dutse.
Lokacin da Alhaji Ladan yajema Hajiya Iya da maganar Habiba bataso ba, amma ganin shi ya dage ne yasa ta amince, amma bayan taja kunnansa kada ya sake ya wulaƙanta Mandiya wato Ummah, ya kuma mata alƙawarin hakan ba zata taɓa faruwa ba, tunda Ummah taji za'a auro Habiba shikenan hankalinta ya tashi ta fito da kishinta muraranta, har aka kawo Habiba gidan nan Ummah na cikin masifa da Alhaji Ladan, kawai baya biye mata ne, saboda yadda ta samu ɗaurin gindi a wajen Hajiya Iya.
Da farko zamansu ya fara daɗi saboda Habiba mace ce mai tsananin hakuri da kawaici, koda Ummah tayi mata wani abu bata tankata. kuma tunda ta lura Hajiya Iya na nuna bambamci tsakaninta da Ummah tafi sonta akan ta, bata damu ba ta watsar da komai ta rumgumi mijinta hannu bibbiyu, watan Habiba biyu da zuwa gidan ciki ya ɓulla a jikinta, murna wajen Alhaji Ladan ba'a magana yana ta addu'ar Allah yasa wannan karon ya samu namiji, tunda Ummah taji haka shikenan hankalinta yaƙi kwanciya ta dinga shiga tana fita domin tayi alwashin bazata taɓa bari Habiba tazo daga baya ta haifi ɗa namji a gidan ba.
Ko ita kanta Hajiya Iya bata ƙaunar taga Habiba ta haifama Ladan ɗa namiji a gidan, ita ko Habiba ba tasan wainar da suke toyawa ba, illah ta maida kanta ga kula da kanta da abunda ke cikinta, da kuma kai kukanta ga Allah. don ita mace ce mai yawan ibada, haka dai har cikinta ya kai wata tara, rana tsaka ta tashi da naƙuda Alhaji Ladan ya kwasheta shi da su Hajiya Iya zuwa wani private Hospital inda aka shigar da ita labour room.
Ko awa ɗaya ba'ayi ba sai ga wata nurse ta fito da dariyarta tana faɗin Habiba ta sauka, cike da tsantsar farin ciki Alhaji Ladan ke faɗin Ma sha Allah, Hajiya Iya ko da Ummah haɗa baki sukayi wajen tambayar me Habiban ta haifa cikin fara'a nurse ɗin ke sanar dasu ta samu ɗiya mace, washe baki sukayi suna hamdala a tare, shiko Alhaji Ladan yaji mamakin abunda sukayi amma sai bai kawo komai a ransa ba, duk da bai samu abunda yakeso ba, bai nuna damuwarsa ba.
sai washegari aka sallami Habiba suka dawo gida aka shiga kiran dangi ana sanar dasu labarin haihuwar.
Ranar bakwai na zagayowa akayi suna inda yarinya taci sunan *Asma'ul Husna..* Alhaji Ladan yayi bajinta sosai a haihuwar Asma'u wanda baima Hajiya Iya daɗi ba sam, haka dai suka ɓoye abunda ke ransu basu nuna ba, amma tsanar da sukema Habiba sun kasa boyeta, haka dai take zaune dasu tana haƙuri tunda mijinta bai chanza mata ba. tana cigaba da rainon 'yarta Asma'u.
Asma'u nada shekara biyu da haihuwa, Ummah ta sake haihuwa kuma itama mace ta haifa, aka sa mata suna Fa'iza bayan Fa'iza ta ƙarayin Rabi'atu lokacin Asma'u nada wajen shekara bakwai kenan a duniya, har an sakata a makaranta inda su Aunty Bilki ke zuwa wato *Dutse Capital School*.
lokacin ne kuma Hajiya Iya ta matsama Alhaji Ladan akan tana so ya ƙara aure bai so ba gaskiya domin shi bashi da ra'ayin auren mata fiye da biyu, amma Hajiya Iya taga yana mata wasa da kanta ta nemo mai auren Mama wato Salamatu kenan itama 'yar Dutse ce, Mama mace ce mai halin ko in kula bata shiga abunda babu ruwanta, kuma mace ce da bata bayyana abunda ke cikin zuciyarta akan fuskarta, baka isa ka gane ina ta dosa ba.
Da yake ita bamai shiga harkan kowa bane, shiyasa Ummah bata mata abunda takema Habiba. itama watanta tara ta haifo 'yarta mace wacce taci sunan Kursum bayan kursum tayi Fati bayan Fati tayi Maryam itace ta ƙarshe da yake haihuwan nata kusa kusa takeyi. itama dai bata haifi ɗa namijin ba, shiyasa Ummah abun yayi mata daɗi sosai domin bata ƙaunar ita bata haifi namiji ba wata tazo daga baya tace zata haifa.
A lokacin zama yaƙi daɗi tsakanin Habiba da Ummah wacce ta kasa haƙuri har ta fara tanka mata, ganin haka yasa Ummah ta fara fitowa da makirci kala-kala tana haɗama Habiba a wajen Hajiya Iya da Alhaji Ladan na wai tana ware Asma'u dasu Fa'iza bata barinta tana shiga cikin ƴan'uwanta. abunda ya sa saida Alhaji Ladan ya tanka bayan ya tsawata ma Habiba, bayan wannan anyi wasu abubuwa da dama waɗanda suka wuce misali, har ranar dai akayi na ƙarshe wanda yayi sanadiyar rabuwar auren Habiba gaba ɗaya wanda Ummah ta mareta akan ta bangajeta bata sani ba, shine kawai ta daga hannu ta kifa mata mari, ganin haka yasa itama Habiba ta daga nata hannun ta sharara mata mari, kawai sai Ummah ta zube ƙasa tana kwarara uban ihun Habiba ta daketa, koda Hajiya Iya da Mama suka fito nan suka iske Ummah kwance Habiba na gabanta tana kallon ikon Allah.
Wannan dalilin yasa Hajiya Iya ta zabgama Habiba mari kuma ta saka Alhaji Ladan bayan ya dawo ya saki Habiba hukuncin da har abada yake nadamar aikatashi ranshi bai so ba, don yana son matarshi. amma haka ya rubuta mata saki ɗaya ya bata, Habiba tayi kuka amma ta barma Allah komai, tun a daren ta kira Bauchi ta sanar dasu su kuma washegari tun safe sai ga matar kawu Inna Jummai sun iso Dutse da katuwar motarsu ta kwashe kaya, aka kwashe kayanta tsaf, lokacin da Habiba taga tabbas tafiya zatayi sai hankalinta ya tashi na yarda zata bar rayuwar Asma'u a hannun muguwar kishiya, Mama kuma bata shiga shirginta saboda ita halinta kenan baka gane wani hali take ciki da kai.
Hajiya Iya da kanta ta amshi Asma'u ahannun Habiba wacce ke kuka itama Asma'u na kuka wacce lokacin Asma'u nada shekaru 12 a duniya tana da wayau sosai lokacin tasan zafin rabuwa da uwa, tana ji tana gani aka kwashe kayan mamanta tas, kuma suka shiga mota suka koma Bauchi, ranar wuni tayi kuka haka Hajiya Iya ta sa bulala ta zaneta tas, wai karta damu mutane da kukan banza, ko Alhaji Ladan daya dawo yaga an kwashe kayan Habiba abun bai mai daɗi ba amma bashi da yanda zaiyi, dole ya ɗau haƙuri.
Tun daga lokacin rayuwar Asma'u ta shiga garari da ƙunci, domin kamar yadda Ummah ta tsani Habiba haka ta maida akalar tsanarta akan Asma'u wacce take ganin bambamci ƙiri ƙiri ana nuna mata da ya'yan Ummah, kamar ba gidansu ɗaya ba, Mama kuwa bata da wata matsala da ita, sai dai bata shiga shirginta kuma bata hanata ta shigo ɗakinta har kwana tanayi a wajenta suyi wasa ita da ƙannenta amma kuma bata isa don tayi ma ya'yanta wani abu ta haɗa da ita ba, ina babu ruwan kowa da ita sai dai idan Alhaji Ladan ne ya dawo wajenshi kaɗai take samun salama, Hajiya Iya ko ɗakinta ta shiga yanzu zata koreta tana zaginta ita da uwarta.
Tun daga lokacin Asma'u ta fara janye jikinta, lokacin ne kuma Allah ya haɗata da AISHA WADA wacce suka taso daga Jigawa suka dawo Dutse mahaifinta ma'aikacin Civil Defences ne, sai kuma akayi sa'a aka sanya Aisha a makarantarsu Asma'u kuma aji ɗaya, tunda ga lokacin shikenan shaƙuwa da ƙawance suka ƙullu tsakanin Aisha da Asma'u wanda ɗaya bai taɓa iya wuni in bai ga ɗaya ba, dalilin haka ne ma Aisha ta matsa sai da aka sata a makarantar Islamiyan su Asma'u, saboda su riƙa zuwa tare, suna dawowa tare.
Mahaifiyar Aisha wacce suke kira da Ammi har gidansu Asma'u ta shiga suka gaisa dasu Hajiya Iya saboda dalilin ƙawancen Aisha da Asma'un, amma tunda su Ummah sukaji ance Asma'u kowacce ta shiga taɓe baki haka Ammi ta dawo gida jikinta a sanyaye, sai a lokacin take tambayar Asma'u ina mamanta take? tace bata nan ta kwashe kayanta ta koma Bauchi tsausayinta ya kama Ammi sosai, tun daga nan tayi alƙawarin kula da Asma'u inda ta haɗasu ita da Aisha tana kula dasu komai zata siya biyu take siya, hakama mahaifin Aisha shima komai zai ma Aisha bata karɓa sai an siyama Asma'u, dalilin hakama har zumunci ya ƙullu tsakanin Alhaji Wada da Alhaji Ladan.
Tun da Ummah ta ƙyalla ido taga rayuwar Asma'u ta fara in ganta tana samun kula da gata wani lokacin ma ba a gidan take kwana ba, wani ƙarin baƙin ciki ma Asma'u gifted ce, domin Allah ya bata kwanya sosai na ƙoƙari ko lokacin da ta gama primary sch ɗinta haka ta amshi kyaututtuka ba adadi, wanda ko su Aunty Bilki dake gabanta basu karɓa ba, ita da Aisha su sukayi ta karɓan kowani kyauta abun sai wanda ya gani, haƙiƙa abun yayiwa Abba daɗi kuma tun daga lokacin yayi alƙawarin zai iya kashe min ko nawane don inyi karatu, in karanci fannin lafiya.
Tun bayan tafiyar Mamana bata ƙara zuwa ba, sai dai ta kanyo min saƙo ta hannu Ammi in ta samu mai zuwa ko ta turo direba dashi, wannan ƙoƙarin nawa shike ƙara wutar tsanata a zuciyar 'yan gidanmu duk cikin ya'yan Ummah mutum daya ce muke shiri da ita Fa'iza domin ita yarinyace mai fara'a da son yan'uwa kuma gata sakona amma kuma muna jituwa sosai, su Maryam ko sama sama suma basu cika shiga harkata ba, nima sai nake baya baya dasu, in ka ganni ina dariya nida rabin raina ne Aisha wacce ta zama tamkar yar'uwa ta jini agareni.
Anan Dutse Capital School ɗin muka ɗora Jss1 ɗinmu nida Aisha hakama sauran 'yan gidanmu don nan mukeyi gaba dayanmu, muna Jss3 Abbanmu ya ƙara aure ya auro Halima wato Aunty Amarya wacce ta zama tamkar uwata agidan, don Aunty Amarya macece mai kirki da kawaici. tunda tazo gidan nan ta kamani ta riƙe hannu bibbiyu bata taɓa ƙyamata ko nuna min bambamci ba, shiyasa nima nake bata girmanta, kuma hatta da Abbanmu yana jin daɗin haka domin duk abunda ke faruwa yana sane bashi da yanda zaiyi ne kawai saboda Ummah ta samu ɗaurin gindin Hajiya Iya.
Haihuwar farko da Aunty Amarya tayi ta haifi namji murna wajen Abbanmu ba'a magana Ummah ko kamar tayi hauka saboda baƙin ciki, amma bata da yarda zatayi domin Allah ke badawa ba mutum ba, ranar suna yaci sunan Kakanmu Lukman suna kiranshi da Walid, hakama haihuwarta na biyu ta ƙara samun ɗa namiji wanda yaci sunan mahaifin Aunty Amarya Shehu suna kiranshi da Khalifa
Muna SS1 bikin su Aunty Bilki da Aunty Ruƙayyah ya taso wanda za'a haɗa rana ɗaya, wai feleƙe wajen Ummah ba'a magana ita mai ya'ya zasu yi aure ko ankon bikin ma Ammi ta mana nida Aisha, Abba kuma ya bamu kuɗi muka ƙara da kala ɗaya, nima na fito nayi sharr. duk da ba haka Ummah taso ba, akayi biki lafiya amare suka tare agidajensu duka anan cikin garin Dutse.
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'aje ba duk wani ƙunci na gidamu da nake fuskanta yanzu ya ragu ganin na girma na zama budurwa. duk wani kyau da cika da ake nema a wajen mace na gama mallakanshi ko mutanen uguwa na faɗa, duk gidanmu ba mai kyawuna, tun muna SS2 samari suka fara mana chaa nida Aisha duk inda mukaje muka dawo sai an biyoni musamman ma ni Asma'u haka Allah yayi ni da farin jinin samari, a kuma lokacin ne akayi mana walimar sauka nida Aisha a makarantar haddarmu, wannan saukan ta izama Ummah ƙara tsanata tana ganin a komai sai na fi ya'yanta da taji labarin Fa'iza taje sai da ta kamata tama ta dukan tsiya, a gidanmu Abbana ne kaɗai yaje sai Aunty Amarya ko Mama bata samu zuwa ba hakama su Maryam wai sun tafi gidan kakanninsu, kuma suna sane da ranar walimar.
Abunda yafi min daɗi shine zuwan Mamata walimar saukata wanda shine haɗuwata da ita ta farko tun bayan barinta gidanmu, a gidansu Aisha ta sauka nayi murna sosai da zuwanta haka muka rumgume juna muna murnar ganin juna mamata tana mamakin girmana da wayau na, ta kawo min kaya da abubuwa sosai harda kuɗi, tamana ɗinkuna nida rabin raina Aisha, sai awajen walima suka haɗu da Abba kuma sun gaisa cikin mutumci, anyi walima lafiya an watse bayan mun karɓi tarin kyauttuka. Washegari mamata ta koma Bauchi bayan ta sanar damu cewa ta kusa aure, nan muka buga ihu nida Aisha mukace wlh sai munje Bauchi, tana Dariya tace in lokacin yayi zata kira Ammi ta waya ta sanar da ita.
Duk tarin samarin dani keyi basa gabana, burina kawai shine nayi karatu, Aisha ce ma ke man faɗa ya kamata na fara kulasu don mun kusa yin Candy kuma gidanmu nasan Abba baya barin wata ta cigaban mai da karatu agida sai agidan mijinta toh da wannan shawarar nata na fara kula wani Najib anan ƙasan layinmu yake ma'aikaci ne a Mtn office, mun fara soyayyah dashi ina sonshi yana sona, har magana takai wajen Babansu Aisha shi kuma yama Abbana magana nan suka samu Najib suka mai maganar ya turo iyayenshi ayi magana, da na gama zana jarabawar fita ayi aurenmu. Najib ya amsa cikin murna amma sai me? Tunda ga lokacin Najib ya ɗauke ƙafa daga gidanmu ya daina kirana a wayar daya siyamin, tun ban damu ba har na damu na sanar da Aisha, muka kirasa a waya yana ɗauka sai tambayata yayi wacece..? Tunda mukaji haka sai jikin mu yayi sanyi sosai da al'amarin, tun muna ɓoyewa har muka sanar da Ammi itama taji ba daɗi amma sai ta bani haƙuri ta lallasheni ta kwantar min da hankali.
Shikenan ƙarshen rabuwa na da Najib, lokacin bikin Mamata ya ƙarato ta kira waya ta sanar da Ammi ita kuma ta shirya mana tafiya bayan Babansu Aisha ya tambayarmun izini a wajen Abbana kuma ya barni, cike da farin ciki muka ɗaga Bauchi ni da Aisha da Ammi, mamata da danginta sunyi murna sosai da ganina. sai da mukayi kwana huɗu kana muka dawo saboda makaranta, Mamata tayi aure a gidan manyan mutane kai da gani basai an faɗa maka ba, ta auri wani Proffessor Abdallah Mahmud Azare wanda ke aiki a jami'ar ATBU BAUCHI, kowa sai taya Mamata murna yake domin ta dace da samun gwarzo miji wanda kowa ke yabonsa yana da mata ɗaya da ya'ya biyar mata huɗu namji ɗaya shine babba kuma da yake duka sun girma babu yara a cikinsu.
Ko a Bauchi da muka dawo sai da wani ya biyo ni mai suna Sagir, da farko banso na kulashi ba Aisha ce ta matsamin har na fara sauraran Sagir, shima dai kamar dai na Najib ɗin sanda aka mai maganar turo mgabatanshi shikenan alaƙarmu ta yanke, wannan karon abun ya dakeni don na shaƙu da Sagir fiye da Najib, amma rana tsaka ya barni ga magana ta gama yaɗa dangi har Bauchi mamata tana ta murnan zanyi aure akusa da ita.
Rabuwata da Sagir tasa sai da na kwanta ciwo Aisha da Ammi suka shiga damuwa sosai gashi muna gabda fara zana jarabawar fita ne, ganin na sa tunani araina ga kuma jarabawar dake gabana yasa na watsar da komai muka kama karatu nida Aisha inda muka zana jarabawarmu cikin aminci da nasara. ranar da mukayi Candy aranar Aisha ta haɗu da Fahad ni kuma Allah ya haɗani da wani Sulaiman ɗan Sanda ne.
Wannan ma karon na tuɓure nace bazan ƙara kula wani namiji ba, amma Aisha da Fahad suka riƙa tausata har na sassauto na fara kula Sulaiman, shi magana har tayi nisa domin ana tunanin rana ɗaya za'a mana aure da Aisha amma sai me, har danginshi sun kawo kuɗin nagani ina so. shima su Fahad sun kawo, sai kuma magana ta taɓarɓare, domin kwata-kwata Sulaiman ya ɗauke ƙafa ko na kirashi awaya baya ɗauka da manya suka kira waliyanshi sai suka ce ai yaro yace ya bar wannan maganar.
Labarin da ya sameni nayi kuka kamar zan zauce, tun daga lokacin sai dangin mamata suka fara zargin ko Ummah tamin wani abu ne duba da irin yarda bata ƙaunata muraran ta nuna, amma sai ban ɗauki abun da serious ba, na barma Allah komai, nan ko Ammi ta dage da nemamin taimako domin kariya, kuma duk abunda ke faruwa Ummah nada labari in muka haɗu ta dinga tintsira min dariya kenan, tun daga nan nasha jinin jikina da ita amma ban taɓa faɗama kowa ba na bar abun a cikin zuciyata.
An saka ranar auren Aisha da Fahad wanda ta dinga kuka tana faɗin ita ba zatayi aure ba sai tare dani, shikanshi Fahad ɗin yasan ƙaunarmu daga Allah take, ni ce abun na Aisha ya bani dariya yaushe ake haka ni Fahad ya kawoma ƙararta nako mata faɗa sosai sai dai kawai ta rungumeni tana kuka, duka duka wata goma aka sanya bikin Fahad da Aisha tun kuma daga lokacin muka fara shiryen shiryen biki.*Janafty*
YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU.
AdventureLabarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.