Chapter 22

224 23 1
                                        

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you covered

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.

      *🅿️22*

Wasila Dake Zaune Cikin Makeken Falonta Kafarta Daya kan Daya Tana ta Danne Dannen Waya Ko ajikinta gefenta Jamila ce Da Hafsat Suma Kowacce Na Kwance Ta Baje Tana latsa waya kamar amafarki Sukaji Muryan Abdallah Daga Waje yana Kwalama Wasila kira.
Zumbur wasila Ta Mike Ta fita Waje Da Sauri bayan Ta Wullar Da Wayar Hannunta akan kujera, Ganin Tafita Da Gudu ne yasa su Jamila Suma Suka Rufamata baya,domin Sunyi mamakin Yadda Wasila Ta Dawo Daga Bida Ranta fes kamar Babu Abunda Yafaru Nan ko Tasan Meta ta taka ne.
Tana Fita Suka Ci karo Da Abdallah yana Kokarin Shigowa Falon,cikin Wani Fitan Hayyaci Ya Rumgumeta lokaci d'aya yana Kamkameta kamar Wani Zai kwace Mishi Ita Fad'i Yake"Don't leave me my Noory I can Do Without u..."Yake Fad'a yana Tusa kanshi kan Dokin Wuyan Wasila Lokaci Daya yana Wani Lumshe Ido Kamar yaron goyen da ya jima bai ji Dumin mamansa ba.
Wasila Da taji Kamar Ansakata Acikin Aljanna Sabida Murna Da Farinciki Ammh Saboda Ta Gwada Abdallah da Kuma Kara Tabbatar da Tasirin Aikin Boka Dandugaji, sai Ta yi Saurin Kwace Jikinta Dakyar Tana Zubama Abdallah Harara, Cikin Fitan Hayyaci Yakara Nufarta Sai Tayi Azamar Matsawa baya Tana Fadin"Don't Touch me Abdallah I Hate u. ni zaka ci Amanata Ni Wasila Zaka yaudara? Ashe Aure iyayenka za su yi maka ammh Baka Sanar Dani ba kasa Kafa Katafi  ko? Fine Yanzu Takardata Zaka Bani Na gama Zama Dakai I Swear"
Tafad'a Tana Wani Jijjiga Jiki ammh Gefe na Zuciyarta Cike Da Jin Dadi, gefe Daya Kuma Tana kara Sarawa Ma Aikin Boka Dandugaji ganin Yadda Abdallah yataho Ko Takalmi bashi Akafarshi.
Jin Abun Wasila tace Ne yasa Abdallah Rudewa Cikin Wani yanayi Dayake Ji kamar Yayi Hauka ya Durkusama Wasila yana Kama Kafarta Cikin Wani Amo yake Fadin"Karki min Haka my Noory Wlh Ba Kowa agabana Sai ke, Bazan Iya Rayuwa da Wata mace ba bayan ke ba. Kece Farincikin Abdallah In kika Barni Wlh Mutuwa Zanyi plz Kiyi Hakuri Gani gabanki Kiyi min Duk Hukuncin Daya Dace Dani."Yafad'a lokaci d'aya Kawai Sai ga Hawaye Suna Kwarayoma Abdallah ba Wasila kad'ai ba Hatta Su Jamila sai da Suka Zaro Ido ganin Abdallsh Durkushe yana ma Wasila Kuka.
Su Emeka ko kamkame Juna Sukayi shi da Jesepe Abun ya basu Tsoro Balle josepen daya Daura Hannu akai yana Fadin"Jesus."
Wasila kamar Tana Yawo Acikin gajimare saboda Farinciki Cikin Wani Juya ido Tace"Hukunci Daya Zan yankema maka Umarni nake Baka ba Shawara ba, Katashi Mu Shiga Ciki na Shiryaka Yau Nakeso Mu bar kasar nan Dama already yau da Safe Na Tura Emeka yaje Airport yamana Buking din Jirgi ZuwAa paris kuma Na Riga na Kamamana Hotel mai kyau da Tsari Ta Webset dinsu, so Zamu Tafi Chan Muyi Hutun karshen Shekararmu achan I hop kaji ni ."Tafad'a Tana Wani Kallonsa Kasa kasa.
Jikin Abdallah na Rawa Yace"yes mah.."yafad'a yana Mikewa Da Hanzari Wasila Tatafi Ta Rumgumeshi, Tana Fadin Tayi Kewarshi Shima matseta yayi yaana Share Kwallah kamar Wani yaro karami Suna Kamkame Da Juna Suka Shige Cikin Falon, yayin da Hafsa da Jamila Suka bi juna Da Kallo kafin Su Saka Dariya Lokaci Daya Suna Tafawa.
kafin Kuma Su Daure Fuska ganinsu Emeka na Kallonsu Suma Cikin Takun yanga Suka Shige Ciki Suka bar Su Emeka da Bude Baki.
Cikin Abunda Baifi awa Daya ba Wasila da Abdallah Suka Gama Shirinsu, Wasila ce Tama Abdallah Komai Ta Kuma Had'amusu kayansu, ta Umarci Emeka da yazo Ya Kwasa zuwa Mota Duk da basu Dibi Wani kaya ba Sai Abubuwan Da Ke da muhimmanci Sauran kayan Sawan in Sunje Zasu Siya Komai
Zasu Tafi Wasila Ta Damka musu Hafsat Daya Daga Cikin Atm din Abdallah Tare Da Duka Makullan Mota Dana Gida, Harda Tarin Makudan Kudi Tace Yanzu Gida yazama Nasu Kafin Su Dawo So Suji Dadinsu Suma.
ihu Suka saka Suka Rumgumeta Suna Murna, Bayan Tayi Musu gargad'in kada Subar Wani Ahalin Abdallah ya Tako Mata gida.
Haka kuma ta Sanar Dasu Emeka da Megadi, Abdallah dai Na tsaye yadda Kukasan Rakumi da Akala Haka Wasila Ke Jan Ragamar Rayuwar Abdallah Tana Rike Da Hanunshi shiko yana Binta kamar Wani Dolo, Itako Tana Wani Taku Tana Yamutsa Fuska kamar Wata boss Haka Suka Shiga Mota Emeka ya Fice Dasu Daga Haraban Gidan Su jamila Na Daga musu Hannu cike da Murnan Gida yazama Nasu.
Suna Zuwa Airport Saura Minti Goma Jirginsu yatashi, Sai alokacin Wasila Ke Tambayan Abdallah Ina wayarsa yace Baisani ba,Ranta yamata Dadi Yadda Komai Zai Tafi kan Tsari Nan da nan Aka Fara Kiran Sunaye.
Har akazo kansu Ba Dadewa jirginsu ya Lula Sararin Samaniya Lokacin da Wasila Ta Kwantar Da kanta Jikin Abdallah Tana Mirmishin Mugunta Tace Afili..."Lokaci na Yafara Daga yanzu..."

ZAMAN GIDANMU.Où les histoires vivent. Découvrez maintenant