*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*GHT GIDAN KUDI🗣🗣🗣🗣🗣🗣 kuna Ina!!! Ga hanyar samu Mata da Maza 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻Shin kunsan kuna da damar shiga GHT company da kudinku kalilan. Wanda Zaku iya kyauta dashi, wanan jarin kune wanda zaku kafa kanku da yaranku. GHT company shine ya kamata ko wani mutum yayi rijister dashi zaku samu alkhairi sosai kuma zaku samu kyautan blender, TV plasma, Kettle, Generator, Kudi, Fita kasan waje, Mota, Gida har da Karatu zuwa kasar waje💃💃💃da dama a cikin arziki GHT da 4,500 dinku zaku shiga harkar da zaku ji dadin ta sosai kuma ku amfani da kayansu wajan nunawa Yan uwa da abokai yanda kayan mu yake aikinsa mazà ku garzayo da 4,500 dinku don shiga wannan Sanaa a dama daku.
KADA KU BARI WANNAN DAMAR TA WUCE KU
*Kadan daga bayanin bonus na GHT*
✅idan kukayi register mutum 1(daya)kuma aka samu cinikayya tsakanin sa da company GHT zata biyaku ₦16,558 kudin la'ada
✅idan kukayi register mutum biyu za'a biyaku ₦33,116
✅idan nakasan ku sukayi register mutum daya za biyaku ₦9,854 zuwa 10k
✅idan nakasan,nakasan ku sukayi register zakisamu ₦8,000 a ko wani mutum daya.
Wannan kadan daga cikin alfanun da zaku samu da ₦4,500 kenan.
Ko kunsan zaku iya samun millions of naira a watanni da company GHT😱
✍🏻idan bakuson kawo mutane, zaku siya kaya a sari ku siyar, ku samu riba.😃
Duk meson rijista yayi mani magana wa.me/+08066726866sai ayi processin masa yin Registration
*🅿️11*
Da karsashinsa ya Tura Kofar Dakin Hajiya ya Shiga da sallama. ammh ciki d'akin Shuru sai dai Wani Ni'imantattacen kamshi Turaren Wuta Daya Daki Hancinsa.
Lumshe ido yayi kafin ya Bud'e su Fes yana bin Dakin da kallo har idonshi ya Sauka kan Hajiya Dake kwance kan gado Tana barci.
Cikin Sanyi Jiki ya karisa gabanta yana Kare Mata kallo. gabansa ne ya Fad'i ganin irin Ramar da Hajiya Tayi Duk ta Zabge Ba wannan kibar Nata da Cikar Fuska mai Cike da karamci, Tsaye yayi yana kallonta idanuwansa Sun kala Sun kara ja,yana ji kamar ya Durkushe Bisa kafafunsa ya saka kuka.
Hajiya ko dake barci dayake Duk Nisan barci Hayaniya kad'an ko Mutum ya matso kusa da ita Zataji yanzu Zata Farka.
Ahankali ta Bude idanuwanta Da Suka Shige Saboda Barci, Abunda tagani yasata Saurin Maida idanuwanta ta Rintse kafin Wasu Siraran Hawaye Su Zubomata ta Gefen Fuska,gyara kwanciya tayi Kafin ta Murmusa tana Fadin"Har Sai Yaushe ne Baffa Zaka zo gareni? Akullum bani da wani mafarki sai na ganin ka tsaye agabana.."Take Fad'a idanuwanta na Runtse tana kuma Share Hawayen da Suka zubo ta gefen Kunnenta.
Jin Abunda Hajiya ke Fad'i ne yasa baisan Sadda ya Durkushe gaban Hajiya ba lokaci d'aya yana kamo Hannunta Cikin karaya Da Nadama ya Furta.."Gani Agabanki Hajiyata ki Bud'e idanuwanki Da gaske wannan Karon Baffanki ne agabanki ba Mafarki kike ba."
Jin Muryan Baffa da kuma Hannunta daya Riko yasa Hajiya Bud'e idanuwanta Fes akanshi,Kuramai ido tayi kafin ta wani Zabura Kamar Zata Fadi, sai gata ta Diro kasa da Mugun karfi har kafarta tana Turgud'e Yayi Saurin Rikota yana kallonta.
Kafad'unshi Ta damka tana Girgiza Shi Take Fadin"Da gaske Baffa na ne Agabana..? Abdallah kai ne kuwa Ko dai haryanzu Ban Farka daga mafarkin dana sabayi bane na Kazo gareni.?
Tafad'a Hawaye Suna kwaranyomata Kana Duka hannuwanta Biyu tana Shafa Fuskarshi. Shima kukan yake son Saki ammh kuma Idanuwansa Sun bushe Zuciyarsa ne kad'ai ke iya Fassara Halin Bakin Cikin Dayake Ciki
Ganin haka kawai yasa ya Fada Jikin Hajiya yana Sauke ajiyar Zuciya yana Fadin"Ni ne Hajiyata Abdallah ki ne. Don Allah ki yafemin bansan meya Sameni ba.."
Yafad'a yana Runtse Ido Saboda yarda Kansa yake Saramai, Ai da hanzari Hajiya ta Kamkame Shi tana Dariya Had'e da Kuka tana Fadin"Alhamdulliah Allah Mun gode Maka daka amsa addu'armu ka dawo mana da Abdallah garemu" Take Fad'a tana kamkame Dashi tana Dariya da Kuka lokaci d'aya.
Yau Hajiya Duk ta Cire wannan alkunya ta Dan Fari ta na murna Zuwan Abdallah.
Daidai Lokacin Maman Fati ta Shigo dakin Hankalinta tashe, Asma'u na Biye da ita abayanta,Ganin hajiya Rumgume da Wani Saurayi ta na kuka yasa Suka yi Turus.
Maman Fati bata samu Zarafin mgana ba Hajiya ta ankare Dasu,Da hanzari ta Saki Abdallah tana Riko Hannunshi take Fadin"Maman Fati mu gode ma Allah. yau dai ga Abdallah yazo garemu"
Sai alokacin Maman Fati taga Fuskarshi,Waro ido tayi kafin itama ta karisa tana Damko hannunshi take Fad'in"Hajiya Da gaske Abdallah nake gaani ko kuwa Idona Ke min Gizo.?
Tafad'a kai tsaye tana Shafa Fuskarshi Kai ya girgiza kafin kawai ya Durkushe gabanta yana Rike da Hannunta yace"Maman Fati Ku min aikin gafara ku yafemin Wlh bansan meya Sameni har nayi wannan Tsawon Lokacin banzo gareku ba."Yafad'a yana Sakin Nishi Sama sama.
YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU.
AdventureLabarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.