Chapter 14

249 26 0
                                        

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku zumar kiba zumar kiba zumace wadda zatasaka kiba cikin kwana 7 dayardar Allah zumar kiba zumace mai inganci wadda aka hadata da magun gunan gargajiya,Bugu da qari har nafdac ta amince da lafiyar zumarmu ta bamu BACH NO hjy indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kasha zuma saika chanza 08167453086

          *🅿️14*

BAUCHI

      Misalin karfe 4:30pm na yammah, Proof.Muhmud Abdallah Azare Yana Zaune Acikin D'aya Daga Cikin Manyan Kujerun Falonshi.
Wani Littafin Azkar ne a hannunshi Yana karantawa Yana Sanye da Wata Jallabiya Doguwa Mai Ruwan Toka Harda Wata Hula Mai Kama Da Tabani Kaji Hadisi.
Idanuwansa Sanye Da Wani Siririn Glass Wanda Ke taimaka masa Wajen kara masa karfin gani wajen Karatu
Gefe Daya Kuma Kira'a ne ke Tashi Acikin Katon Talabijin Din Daya yima Falon kwanya tashar Manara TV ne Suka Sanya Karatun Alqur'ni mai girma Cikin Suratul Ankabut da kira'ar munshawi.
Hajiya Tayi Sallama Ta Shigo Falon Cikin Kulawa ya Amsa Mata Sallaman Yana Kokarin gyara Zamanshi Lokaci Daya Yana Kallonta Kusa Dashi Ta Zauna Tana Fadin"Barka Da Hutuwa Mallam.."Bai Dago ba sai ya Ida Karatun Dayake kafin ya Janye idanuwansa Lokaci Daya Yana Rufe Azkar din Dake Hannunsa.
 
Dubansa yakai Kan Hajiya kafin ya Saki Mirmishi Yana Fadin"Yauwa Hajiya, Hajiya Uwar Abdallah bawan Allah.."Ya Fad'a Da Sigan Zolaya, Mirmishi Ta Saki Tana Fadin"Kai Mallam Baka rabo Da Zolaya yau Kuma kirari Akejin yi ne"
Mirmishi ya Saki Kafin yace"Eh Mana Wato Hajara Kowa yagama Lura dake In Ana Son ganin Hakoranki awaje toh Ayi Miki Zencen Abdallah, Ciwo ya Kare ko Tunda yanzu Baffan n kula da Uwarsa Dakyau Dakyau.."Yafad'a Yana Yar Dariya.
Kunya Takama Hajiya ta D'an Dara Tana Rike Baki, Dariya Mallam Ke Mata Cike Da Farinciki yace"Kina Rike Baki,ko nayi Karya Tsakaninki ga Allah Zaki Fad'a?
Bakinta a washe Tace"Ni bance kayi Karya ba Mallam ammh.."Dakatar Da ita yayi Yana Fadin"A'a bar Mganar Maman Nafisa Tunda Dai Kin San Gaskiya."Yafada Yana Kallonta Lokaci Daya Yana Mata Dariya.
Gyara Zama Hajiya Tayi kafin Tace"Mallam wajenka Nazo Fa.."karkato Da Hankalinsa yayi Kanta Bayan ya saka Hannu ya rage Karan Karatun Da Remote din Dake kusa Dashi, sannan ya Maido da Hankalinsa Kanta Yana Fadin"Ina jinki Hajiya Allah sa Lafiya.."
Muskutawa Hajiya Tayi kafin Tace"Wani Tunani nayi Game Da Baffa Mallam.."Da Mamaki ya Kalleta kafin ya Maimata Sunan da Sigar Tambayan"Baffa Kuma..? Cike Da kwarin Gwiwa tace"Eh Mallam,Duk da yanzu Hankalinshi ya Dawo Jikinsa ya Fahimci Mune iyayensa na har Abada Wanda Bai da kamarmu, Addu'armu Bata Fadi kasa Banza ba Mallam Tunda yanzu Zaka ga Duk Safiya sai Baffa ya Kira mu Yana Tambayanmu lafiyanmu, Wanda Abaya bamu Samu wannan Damar ba"
Ta Dakata tana Sauke Numfashi.
Mallam na Kallonta ya Kad'a Yana Fadin"Ina jinki hajara.."Cigaba da Mgana Tayi da Cewa"Shine na Zauna Nayi Tunanin Mai Zai Hana mu Samu Wani Abunda Zai Dawomana Da D'anmu gabadaya garemu Wanda Ko baizo Donmu ba Zai Zo Don Abunda Zamu Masa.."A Natse Mallam Ke Binta Da Kallo Kafin yace"Ban Tari Numfashinki ba Hajara Menene Wannan Abun Wanda Abdallah Ko bai zo Donmu ba Zai Zo Don Shi..?"Cike da Kwarin Gwiwa Hajiya Tace" *MATA*..."

Da Kallon Mamaki Mallam ya Bita kafin yace"Mata Kuma..? Taya ya Hajara..? Hajiya Ta Numfasa Tana Fadin"Ma'ana mu nema Masa Mata Daga barayinmu Mallam mu Aura Masa Koda bayaso. Kuma mu Ijiyeta Atare Damu Tilas Abdallah Zai Dinga waiwayan Gidan Ko ba don mu Kodon Matarsa Dake Tare Damu.."
Mallam yayi Shuru Yana Nazarin Mganar Hajiya Kafin ya Kara gyara Zaman glass din idonsa ya Cire ya ijiye Kan Hannun kujeran Dayake Kai yace"Banki Taki ba Hajara Ammh Wani Hanzari ba Gudu ba Wata Yarinyace kike ganin Zata Dace da Yanayin Abdallah,? Kar  ki Manta Shed'aniyar Matarsa Bata barsa Haka ba, Duk da Nasan Abdallah bazai Bijirema Umarninmu ba,ammh Fa kinsan yanayin Da'ake Ciki Hajara Azo Aneman ma yaron nan Aure ,Daga Baya Ya Gudu ya barmu Da Jin Kunya, in mu munyi Hakuri Mun Nuna Juriya mu Iyayen Baffa ne baza mu Taba kin D'anmu ba Ammh Matar fa? da Yan'uwanta ? Watarana fa Zasu Gaza Hakuri Har Zuciyoyi Suzo Su baci. shi nake Gudu Hajara Tuntuni Shiyasa Kika ga Ban  tab'a Kawo Shawaran mu Matsama Abdallah yakara Aure ba Tun Abunda ya Faru na Farko game da Aurensa da Matarsa da duke Tare yanzu"
Yafad'a Yana Sauke Numfashi, Hajiya Tace"Duk naji batunka Mallam kuma na yarda Dakai. ammah Da yardan Allah Muna Kai kukanmu gareshi Bazai karabama Wannan Shedaniyar Matar Tashi Dama Akanshi  ba, Mganar Yarinya Kuma kwantar Da Hankalinka ta Gida ce,Kuma Kaima Nasan Zaka Yaba da Zabina zakuma Ka yabama Hasashena Mallam.."Kai Tsaye yace"Wacece..?
Sai da Hajiya ta Murmusa kafin Tace"  *ASMA'U CE*.. "
Tafad'a Fuskarta na bayyanar Da Annuri, cike da Mamaki Mallam Ke Kallonta kafin yace"Wata Asma'un..? Kai Tsaye Tace"Asma'u Dai daka sani Mallam Yar Wajen Habiba..."Tsam Mallam yayi Yana Bin Hajiya da kallo ganin Haka yasa Hajiya Tayi Saurin Cewa"Don Allah Mallam karkace A'a Wlh kafin na Tare Ka Da Mganar sai Da nayi Addu:aa sosai Akan lamarin Kuma naji Zuciyata ta Natsu da Mganar  Mganar Gaskiya Asma'u yarinyace Burin kowani Namiji Mai kima ga Tarbiya ga Natsuwa ga Hankali Uwa Uba ga Addinina na Tabbatarmaka Alheri ne Matukar Baffa ya samu Dacen Samun Asma'u a matsayin Matarsa."Tafad'a Cike da Tabbatarwa.
Aiyar Zuciya Mallam ya Sauke Kafin yace"Hakane Duk Abunda Kika Fad'a Akan Asma'u Gaskiya ne, ni kaina Shaida ne Tunda Ga Mahaifiyarta Nan Muna tare Da ita Shekara da Shekaru Kuma bamu Taba samun Wata Mtsala ba sai Abunda ba'a rasa ba, ammj tsaya wani hanzari ba gudu ba Shin Hajara kina ganin Babu Matsala,ta bangaren Ita Asma'u.? Bangaren Habiba Dai Babu Shakka Nasan Ba Mtsala."..
Baki Hajiya Ta Washe kafin Tace"Babu Mtsala Sam Mallam Asma'u Yarinyar Kirki ce, Bazata ki Abunda Muka Zo Mata Dashi ba.  Yanzu Dai Kafara yin isthikara Akan all'amarin In kaima Zuciyarka Ta Natsu kamar Nawa sai Mu Tuntubi Habibar Duk Da Nasan Bazata ce Komai ba,sai Asan Abunyi Banaso Abun ya Dau dogon Lokaci.
Gyada Kai yayi Kafin yace"To Shikenan ba Mtsala Zanyi Zuwa Gobe ko Jibi Sai na Kira Habiban mu Tattauna Allah Ka Shigemana Gaba"
Hajiya Ta Karba Da Ameen kafin Su Cigaba Da Tattauna Mganar Hajiya Nata Kara Karfafa Mganar Don Dai Mallam ya Amince 100%.
ai ko Tayi Nasara Domin Shawaran Hajiya Ta Zauna Sosai Acikin Ransa.

ZAMAN GIDANMU.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora