*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku zumar kiba zumar kiba zumace wadda zatasaka kiba cikin kwana 7 dayardar Allah zumar kiba zumace mai inganci wadda aka hadata da magun gunan gargajiya,Bugu da qari har nafdac ta amince da lafiyar zumarmu ta bamu BACH NO hjy indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kasha zuma saika chanza 08167453086
*🅿️16*
Koda Su Anty Amarya Suka isa Tsakiyar Falon Abba Sun Iske Mama Da Hajiya Iya Tsaye Suna Bin Kayan Da Kallo Abba Na Gefe.
Baki Hajiya Iya Takama Tana Fadin"Wai Ladan Ko bakaji Dakyau bane, Wannan Kayan Duk na Asma'u ne."?
Ɗan Mirmishi Yayi Kafin yace"Tabbas Iya, Sadakin na Wajen Mallam Wada nace Ya Ijiye Awajensa Tukunnah, Dayake Lokacin Da Shi Mahaifin yaron ya Bukaci Sanya Lokacin Bikin Sai na Kirashi Awaya Sai Gashi ya Kariso.."
Anty Amarya ce ke Zagayen Kayan Tana Kara Sakin Gud'a Hajiya Iya ta Dago Tana Kallonta Cikin Takaichi Tace"Wlh In Kika Sake ma mutane Wannan Sakarci Zaki Fita Halima, Haba Kinbi Kin Damu Mutane Hala Asma'u ce Farkon Aurarwa Agidan nan..? Tafada Cike Da Zafin Rai Da Bakinciki.
Jin Haka yasa Anty Amarya Rufe Bakinta Tana Fadin"Allah Baki Hakuri Hajiya, Ba Yau Aka Fara Aurarwa ba. Ammh ni Wannan Shine Na Farko awajena Don Asma'u Tamkar ɗ'iyata nake Kallonta.."Tsaki Hajiya Iya taja Takaichin na cinta, Umma Tabi Da Kallo Wacce Ke Gefe Tana Bin Tulin Kayan Da'akace Na Saka Ranar Asma'u ne da Kallo Bakinciki kamar ta sakama Kayan Wuta Haka Takeji.
Mama Kuwa Tana Tsaye Ita kad'ai Tace"Allah ya Sanya Alheri.."Babu Wanda ya gane Abunda Ke Zuciyarta Hajiya iya ce Ta kalli Abba Tana Fadin"Anya Ladan Abunda ka yi ka kyauta kuwa..? Abba yace"Me Nayi Kuma iya..?
Tacigaba Da Fad'in"Toh na Wannan Uban Kayan Daka Karba, kana ganin bazamu Zama Abun Zund'e ba a fara yawo Damu Agari ace ka Saida Asma'u Kuna Ranar Aure Sati Biyu kamar Wata Kaza, Karka Manta Akwai Fa Shirye Shiryen fa Daza'a gudanar Sai nake Ganin kamar Lokacin Yayi Kusa.."Tafad'a Tana Kallonsa.
ɗan Mirmishi Yayi Kafin yace"Ko Daya iya, Karki Manta Itama Asma'u Tamkar ya Take Agaresu, Da Farko na Fara mgananar Kayan Sunyi yawa Sai Ya Rufemin Baki Da Fad'in Daga Yaron Wajen Nashi Har ma'u Duka ƴa'ƴansane So bayason Wani Korafi Zai Mata Abunda Yafi Hakama.."Jin Haka yasa Bakin Hajiya iya ya Mutu Anty Amarya Tace"Gaskiya ne Kam..Duka Nashi ne.."
Bakin Ciki ya Kusa Kashe Umma Ta Juya Ta Fice Daga Falon Cikinta na Juyawa ,Dakinta Ta Shige ta fad'a Tiolet Da Gudu Saboda Yadda Taji kamar Gudawar Ta Fara Zubomata.
Abba ne yacema Hajiya iya" Iya ko Za'a Kai Kayan Nan Ɗakinki ne.."Da Hanzari Tace"A'a barsu Anan.."Daga Haka Itama Ta Juya Ta Fice.
Abba ya Bisu Da Kallon Mamaki,karshenta Mama ne da Anty Amarya Suka Kama Kayan Da suka Shiga Dashi ɗayan Bedroom din Dake Shashen Abba.
Asma'u Ko Tana kwance Tana Barci Saboda Mganin Datasha Kamar Amafarki Takejin hayaniyar Su Baba lami kamar Harda Muryan Anty Amarya, Mikewa Tayi Tana Salati Lokaci Daya Taji zazzabin Dake Jikinta ya Sauka Hakama Ciwon Kan Nata,Saukowa Tayi Daga Kan Katifarta Ta Shiga Tiolet Tayi Wanka Tana Fitowa Ko Mai Bata Shafa ba Ta Zura Dogowar Rigarta Baka,Ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallar Azahar Domin Ta Duba Agogon Wayarta 1:30pm na Rana
Ta idar Da Sallan Kenan Sai ga Anty Amarya Ta Turo Kofar ɗakin Ta Shigo Ganinta Zaune ne yasa Ta Washe Baki Tana Fadin"A'a Amaryar Sati biyu kin Tashi..? Ya karfin Jikin naki Yanzu..? Mikewa Tayi Tana Kokarin Cire Hijabin Jikinta ba bama Mganar Anty Amarya Ta Farko Muhimmancin ba Shiyasa Tace"Da Sauki Anty Wlh Koda Nashi Naji Ni Sakayau.."Dariya Anty Amarya Ta Saka Tana karisawa Gareta Tana Fadin"Masha Allah Dama, Zazzabin Na Barin gidane ma'u Allah ya Amshi Addu'armu Ina Miki Murna Nan Da Sati Biyu Kinzama Amarya.."
Kuri Tayima Anty Amarya Da Ido Kafin Tace"Amarya Kuma Anty..,? Bangane Mganar ki ba.."?Tafad'a Cike Da Mamaki ,batasan Dalili ba Sai Dai Taji gabanta Na Fad'i Lokaci Daya Kuma Jikinta Ya fara yin Sanyi..."Baki Anty Amarya Tarike Kafin Tace"Ikon Allah, Kodai bakisan Meke Faruwa bane..?
Asma'u Tace"Meya Faru Anty Amarya Wlh Bansani ba..? Tafada Idanuwanta Na Fitowa Saboda Tsoro.
Kafad'unta Anty Amarya Ta Dafa kafin Tace"Kwantar Da Hankalinki Abun Alheri Ne ya Sameki Damu Gabadaya. Kuma Nayi Farincikin Jin Nice Ta Farkon Wacce Zan Sanar Dake Wannan Lbrin,Dazu Nan Mijin Mamarki Suka bar Nan Gidan.."Ido Asma'u Ta sakar mata Kafin tace"Mallam..? Anty Amarya Tace"Eh Mganar Bata da Yawa Atakaice yazo Mganar Nema ma ɗa'nsa Aurenki ne, Kuma har Babanki ya bashi Har An saka Rana Sati biyu, sun bada Sadaki Dubu Dari biyar Kudin gaisuwar iyaye Dubu dari biyu ga Kuma Uban Kayan Arziki Wai Kayan Saka Rana.
Gaskiya Asma'u kin yi Goshi Domin Naji ajikina Wannan Karon Allah ya Karbi Addu'anmu Zaki Zama Amarya.."
YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU.
AdventureLabarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.