*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty**ina gaida Maryam Jumare sannu da aiki, Fatan alheri zuwa Sisinah Aisha muhammad Alto, jinjina gareki Surayya dee(kawata) tare da Masoyana na nesa da na kusa da suka karbi labarin nan a karo na biyu Nagode kwarai Allah ya saka da Alheri sai mun sake had'uwa da ku acikin sabuwar Tafiyar in sha Allahu*
Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you coveredhttps://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.
*Karshe.*
Ta na komawa ta fara Shirin Komawa parthercourt Wanda Hajiya Ta ce Tare Da Baba Sa'a Zata koma Kuma batare Da Rakiyar Kowa ba, Haka ko akayi Ba ta Tafi da Wasu kaya ba sai Akwati Daya Wanda ta asaka Kayan su Aina aciki Da Abubuwan da Zata Nema.
Mamman yakai su Airport nida Baba Sa'a Wacce zata Dinga Taimakamata da Rainon Su Aina,Suka Hau Jirgi bayan Ta Kira Abdallah ta Sanar dashi, Farinciki ya Cikashi Yace da Zarar Jirginsu ya Sauka Ta Kirashi Zai Turo Emeka yazo ya Daukesu Shi yana Office aiki yamai Yawa,Haka ko akayi Jirginsu na Sauka Ta Kira Abdallah Ta sanar Dashi Shi kuma Ya Tura musu Emeka yazo ya Daukesu Zuwa Gida Ita da Baba sa'a Wacce Ke Rike da Aina Ita Kuma Ma'u Tana Rike da Aima Ahannunta.
Lokacin da Megadi ya Wangale musu get din Gidan Asma'u Taji mamakin ganin Sauye Sauye Acikin Gidan Kama da Karin Wasu Motoci Dake Cikin Tamfol da Kuma Fulawars masu kyau da Tsari da'aka Shuka bayan Tafiyarta har Sun Fito.
Abun yabama Ma'u sha'awa Acikin Ranta Tana yaba Komai na Abdallah Yadda yake Dabam Acikin Maza Haka Komai Nashi Yake Daman Irin So Special din nan
Lokacin da Emeka ya Daidaita Zaman Motan A parking space Ya Zagayo yazo ya bude musu Suka Fito Ita da Baba Sa'a, da Hanzari Emeka ya Bude Booth ya Dauko Akwatin Ma'u ya Nufi babban Shashen Gida ma'ana Inda Wasila Tayi Mulkinta.
Galala Ma'u Ke Binshi da Kallo Kafin Tayi Mgana Wayar Abdallah ya Shigo wayarta Tana Dagawa Kafin Tayi mgana Taji yace"Wlcm back Home my Sugarlip. Karki ce Komai my Dear sai inda na Dawo Ok.."Gyada kai Tayi Tana Mirmishi kafin Tace"Ok Babe..."Daga Haka Suka yanke Kiran.
Tana Cema Baba sa'a Suje Haka Suka bi bayan Emeka har Zuwa Shashen Inda Ma'u Ta sake Bakin Ganin Kamar an sake Komai na Cikin Flat din Ko'ina yana kalli ban Sha"awa Ashe Tun bayan Tafiyarta yasa Aka Fita da Komai Na barayin Aka Kona Don yace bai yarda Da Kayan ba, Aka sake Sabon Fenti na yarari da Zamani Akayi Feshi Saboda Shifa Har yanzu kyankyamin Wajen yake ammh Saboda yafi Girma Kuma Shi Yana Dauke da Upstairs ne Kuma Shi Abdallah yana Kaunar Rayuwa A Upstairs.
Har Emeka yaFice Ma'u na Bin Ko'ina da Kallo Cike da Sha'awa Wasu Kayattatun Kujeru ne Suka Kawata Falon Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ma'u Tazauna Tana Fadin Masha Allah bayan Ta Umarci Baba data Zauna. Aina ta bata Ta Fara Zagaya Duka Dakunan Shaahen Ko'ina An chanzamai Komai Tsab kamar Mutum bai Taba Rayuwa awajen ba, Daya Daga Cikin Bedroom din Dake kasa Ma'u Ta sauki Baba sa'a Ita Kuma Ta Haura sama Bedroom da aka sakama Master Bedroom Ta Bude Ta Shiga Sai Da Ta Kusa Shidewa Komai na Ra"ayinta aka saka White And pick Wow.. Haka kawai Ma'u Ke Furtawa Komai kayanta na Jere Acikin Dakin Abun sai Wanda Yagani sai Wani Dake Kusa Dashi Wanda Shi Kayan Dakin Black and White ne Kayan Abdallah ne Aciki alamun nan Ne Nashi,Akwatinta Taja Cike da Murna ta Shiga Dashi.
Dakin Baba Sa'a Tashiga Ta Karbi Su Aina ta basu Nono kafin Tafada Kichen Ta Iske Komai na Bukatar Girki Akwai Shiyasa nan da nan Ta Kunna gas Ta Fara Kokarin Dora Dinner Saboda Abdallah Cikin Lokaci sai gashi Tagama Sakwara da Miyar Agushi Sai Ferfesun Ganda da Kuma Lemon kankana Data Hadamai da Kunun aya ,dama already Su Ta farayi Tasanyasu A frigde kafin Tagama Girkin Yayi Sanyi Illai Kuwa Cikin Lokaci Tagama Jera komai Bisa kayatacen Danning Din Dake Falon,Ta Haura sama ta Shiga Wanka agurguje Ganin Har Bakwai TaWuce Lokacin sallar mangariba yayi .
Ta dad'e Abayin Tana Wanke Kanta kafin Ta Fito Manta ta Shafa Olive Duk bata Damu da Makeup ba yau Tayi bayan Ta Shafa Hoda ta sanya Jambaki kalan Kayan Jikinta Wani Material ne,Shara Shara Mai Santsi Kuma Mai kalan pick da Blue ne Kuma gashi da Mannewa ajiki Duk sai ya lafe mata Duka Cikar Kirjinta Dana Kugunta Suka Fito Bata Sanya Dankwali ba sai Ta gyara gashinta Ta Fakashi Ta baya bayan Ta Shafamai Tana kyalli Tana cikin Fesa Humrarta ne Wanda Aisha ta Bata Taji Karan Hon din Mota Lokaci daya Kuma da Bude Get. Mirmishi ta saki kafin Tayi Hanzari Tagama Shafa Turaran Aduka Lunguna da Sakon Jikinta,Ta Fice Daga Dakin Daidai Lokacin Shi Kuma Abdallah ya Shigo Falon da Sallama Fuskarshi na bayyana Fara'a Jin Falon ya Hade da Kamshin Abinci Dana Turaran Wuta da Baba sa'a Ta Kunnah.
Tundaga Nesa ya sakarma Ma'u Ido Itakuma Cike da yanga Take Saukowa Daga Step din Daya bayan Daya kasa Jure jiranta yayi Da Sassafar ya isa gareta ya Dagata Cak ya Sauko Da Ita Tsakiyar Falon Tana Dariya Direta yayi kafin ya Ware Mata Hannuwanshi Da Gudu Ta Fada Kirjinsa Atare Suka saki ajiyar Zuciya Lokaci Daya Suna kamkame Juna Kanshi ya Tusa Ajikin Wuyanta yana Fadin"I miss u my Sugarlip...."Tana Kara Shigewa Cikin Kirjinsa Tana Fadin"Miss u More Babe..."Sun Dade Suna Rumgume da Juna Kafin Su saki Juna Kowanne na Bin Dan'uwansa da Kallo Cike da So Da Kauna.
Hannunta ya Riko yana Fadin"Masha Allah My Sugarlip sai bayan Tafiyarki Nasan Sai Kina Gidan nan ya Cika complete Wlh da Bakina Ko'ina Empty buh ammh Kalli Daga Dawowarki Komai ya Dawo Daidai Tunda na Shigo nakejin Kamshi me Matata Ta Shiryamin ne..? Yafad'a yana Leken Kololin Dake Diniing Area.
Kunnanshi Ta kama tana Fadin"Sai kayi Wanka munyi sallah Tukunnah Nima Murna In Fito na Tarbeka bai barni nayi Sallah ba.."Mirmishi ya saki ya Jawota jikinsa yace"where is my kids...?Tace "Suna Wajen Baba sa'a Harma tayi musu Wanka ka bari ka natsa sai suzo su gaishe da Abbunsu ko.."Gyada kai yayi yana Fadin"Antything For my Madam.."Dariya tayi Tana Kama Hannunshi Suka Haura sama.
ESTÁS LEYENDO
ZAMAN GIDANMU.
AventuraLabarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.