*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you coveredhttps://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.
*🅿️26*Karfe 7:30 pm na Dare Suka Isa Bauchi Lokacin har an sallame Sallar mangariba Hon Emeka ya zuba akofar makeken get din gidansu Abdallah Da Gudu megadi yazo ya wangale musu get din Suka Sulala Ciki.
Asma'u wacce ke Kwance Bisa Kirjin Abdallah Tun Barowarsu Dutse Ya Dan Fara Shafa Fuskarta Yana Fadin"Husna...mun iso.."Dakyar Ta Bude ido Jin Mota Ta Tsaya ne yasa Tace"Mun iso ne yaya Abdallah...?
Kai ya Daga Mata Kafin yace"Yes sarkin Barci Mai kuka Tana Barci Kuma." Yafad'a Da Sigan Zolaya Tura Baki Tayi kafin Ta Balle Murfin Motan Ta Fito Tana Rike Da Jakarta Shima Abdallah Fitowa yayi Megadi Daya Fahimci Abdallah ne Da Gudu ya Kariso yana Gaisheshi Ya Amsa Fuskar ba Walwala kamar ba yanzu yake Mirmishi ba.
Asma'u bata Tsaya ba Ta Nufi Cikin Gida Tana Tafiya Ahankali Saboda Rauninta Domin Kowa Tayi Tafiya da Sauri Sai Taji Zafi.
Sallama Ta Doka A babban Falon Gidan Wanda Babu Kowa sai Karan Talabijin,Shashen Mallam Ta Kalla Taji Shima Karan Talabijin Din Daga Barayinsa Ta Fara Taku Zuwa Shashen Hajiya sai ga Maman Fati Ta Fito Daga Shashenta Zata Shashen Falo Sukayi Kicibis Da Ma'u.
Cike da Mamaki Take Kallonta Kafin Tace"Ma'u...? Asma'u kanta Na kasa Tace"Na"am Mama...!"
Baki Maman Fati Ta Kama kafin Tace"Na Shiga Uku Daga Ina Kike Da Wannan Daren..? Kuma baki Kira waya Kince Kina Tafe ba..? Mirmishi Asma'u Tayi Kafin Tace"Bani kadai bane Mama Tare Muke da ya Abdallah yana Waje."'Ido Maman Fati Ta Zaro Cikin Mamaki Kafin Tace"Wani Yaya Abdallah..? Ko Baffa kike Nufi..? Kai Asma'u ta d'aga Zata sake Mgana Kenan Sai ga Abdallah ya Sawo kanshi Falon bayan ya Umarci Megadi daya Sauki Emeka adakinshi Kafin Zuwa gobe.
Maman Fati Da Mamaki da al'ajabi Suka Mamayeta kasa Mgana Tayi Banda Kallon Ma'u lokaci Daya Tana Kallon Abdallah Kamar Wacce Ta Warke Makanta, Mirmishi Abdallah yayi yana Karisawa Kusa Da Ma'u Ramkwafa yayi yana Fadin"Mama..."Sai Kuma Rauni ya Shigeshi yayi Shuru idanuwansa na Chanza Launi Ai sai Maman Fati Rikoshi Ta saki Murya Tana Fadin"Hajiya Mallam Ku Fito Kuga ikon Allah Kuzo Kugani Kai Allah Abun Godiya..."Take Fad'a Tana Shafa Fuskar Abdallah..
Hajiya Dake Zaune Cikin Falonta Tana kan Darduma bayan Ta iddar da Sallar mangariba Tana Addu'o' kamar amafarki Taji Muryan Maman Fati Tana Kiran Sunanta Dana Mallam,Da Hanzari Ta Mike Ko Hijabin Jikinta bata Cire ba Ta Fito Da Gudu
Hakama Mallam da Sauri ya Fito yana gyara Zaman gilashin Idonshi Domin Lokacin yana Karatu ne Haka su Fati ds Mahmud Dake Daki Suna Homework Suma Suka Firfito Sai Dai Duka Tambayoyin Su Hajiya ya Makale ne Lokacin da Suka Ci Karo Da Abdallah da Ma'u.
Mallam Kurama Abdallah ido Yayi yana Kallonsa Hakama Hajiya Maman Fati ne Take Fadin"Yanzu Naga Sun Shigo Wlh Shida Asma'u..."Tafada Tana Bayyanar da Murnanta, Hajiya Cike Da Hawaye a idanuwanta Ta Kurama Abdallah ido kafin Ta Kada kai Ta Juya Da Hanzari Abdallah ya Taka Zai Bita Mallam ya Dakatar Dashi Da Fadin"Kai Abdallah..."Waigo yayi Idanuwansa Sun Koma Jawur Ganin Mallam Tsaye yana Kallonsa yasa ya Tafi Da Gudu Garesa Ya Fada Jikinsa Lokaci Daya yana Kuka yake Fadin"Mallam in kuka ki Yafemin Wlh Zan Kara Lalacewa Rayuwata Zata Shiga garari Fiye Dana Baya, Yafiyarku agareni da Addu'anku Gareni Ita Ke Rike Dani har yanzu Mallam,Don Allah ku yafemin Bani da Masaniyar Abunda Yafaru.."Yafada yana Jin jijiyoyin kanshi na mikewa Bayansa Mallam yake Bubbugawa Alamuun Lallashi kafin yace"Karka damu Mu iyayenka ne Bazamu taba Gudunka ba, Mun yafemaka ko Itama Ta Yafemaka bacin Rai ne Karka Damu anjuma kadan Zata Sauko, naganka da Asma'u ina ka Daukota.."Dago Kanshi yayi kafin yace"Agidansu Mallam,Na Dauko Tane Ta tare Agidan Mijinta Domin na Nuna Muku na Chanza Na Fara Daawowa Abdallah na na bata.."Mirmishi Mallam ya Saki kafin yace"good News..Masha Allah,Allah ka Shiga Tsakani Nagari Da Mugu.."
Yafad'a yana Dafa Kafadan Abdallah kafin ya kalli Asma'u yana Fadin"Habiba duk kawaicin ne, Kinbarta a Tsaye..."Yafada yana yar Dariya da Sauri Asma'u Ta gaisheshi Maman Fati ko batayi mgana ba Ta Wuce kichen Tana Fadin"Bangane ba,ai gidan ba Bakonta bane.."Mirmishi Asma'u Tayi Kafin Ta Nufi Shashen Maman Fati Mallam da Abdallah Suka Bita Da Kallo.
Mallam ne ya Katse Abdallah Da Fadin"Kaje ka bama Mahaifiyarka Hakuri ka Sanar da Ita ga Ma'u ka Daukota nasani Zatayi Farinciki."Gyada kai Yayi kafin Cikin Sanyi Jiki ya Fara Taku Zuwa Shashen Hajiya,Mallam yabi Shi Da Kallo Har ya Shige Baya ya Koma yana Fadin"Alhamdulillah...."
Da sallama Abdallah ya Shiga Bedroom din Hajiya sai ya Sameta Zaune gefen Gado Tana Share Kwallah Karisowa yayi ya Durkushe agabanta yana Kallon ta Kafin ya Riko Da Duka Hannayenta yana Fadin"plz Hajiya Forgive me...Kina min Kuka So Kike in Shga Bala'in Fiye da Wanda Na Shiga abaya...? Kiyi Murna Abdallah ya Fara Dawowa Ainihin Abdallah Mahmud Azarensa Hajiya ga Ma'un ki chan Naje Har Gidansu na Daukota Gobe zamu Tare agidanmu Hajiya i promise u zan Rike Ma'u Da Amana inna Cutar Da Ita Daidai da Rana daya Allah ya Mata sakayyah.."Yafada Cikin Muryan Rauni..
Hajiya na Kuka Ta Mike Ta Dago Abdallah Ta Rumguneshi Tana Fadin"Ban taba Rikeka araina ba Baffa,Kullum Tsakani na Dakai Addu"a ne akan Allah ya Kwatoka Daga Hannun Wannan Shedaniyar Matar naka, Na yafemaka Naji Dadin Dauko Ma'u Dakayi Baffa Allah ya albarkaci Aurenku gobe da Safe sai Ku Koma Gidanku Tunda yanzu Dare Yayi.."Saboda Murna Baffa Baisan Sadda yayi ma hajiya kiss agefen Kumatu ba Keyarsa Ta Make Tana Dariya Shima Yar Dariyan yake kafin ya Fito da Wayarsa yana Kira Nombar Ma'u.
Asma'u Wacce Idar da Sallarta kenan Na la'asar din Data Kubcemusu da mangariba Tana Zaune Tana azkar Maman Fati na Gefe Tana gyara kayansu Fati ammh Rabin Hankalinta na Kan Ma'u Wacce Take Kallonta Cike Da Farinciki da Murna Rayuwar Ma'u yafara gyaruwa,wayar ma'u Tayi kara Wacce Ke Cikin Jakarta Jikinta asanyaye Ta Tashi Tana Tafiya ahankali Ta Isa Inda Jakarta yake Maman Fati na Binta da Kallon Mamaki ganin Ma'u na Gwale kafa kamar yar koyo.
Tana Fitowa da Wayar Taga Nombar Da Abdallah ya Kirataane Da Safe Tana Dagawa Yace"Kizo Mamanki na Nemanki Husna..."Mirmishi Ta saki kafin Tace"Na idar da sallah ne ganin nan Zuwa.."Ok yace kafin Su yanke Kiran Tahowa Tayi Tana Duba wayar ahannunta nan Ta Tarar da Missd clls ba adadi na Aisha Harda Na Fahad sai na Ammi Dana Anty Amarya Mirmishi Tayi Domin Tana da Tabbacin Aisha Taji lbrin Komai, Kallon Maman Fati Tayi Bayan Ta Ijiye wayar akan madubin Dakin Take Fadin"Mama zani Shashen Hajiya mu gaisa.."gyada mata kai Maman Fati Tayi Ita kuma Ta Fara Taku Zata Fice Maman Fati Tace"Asma'u..."
Juyowa Tayi Tana Fadin"Na'am Mama..."Maman Fati Ta Hade Rai Tana Fadin"Zo nan..."Ba musu Ta Nufeta Lokaci Daya Tana Tsarguwa da Irin Kallon Da Maman Fati Ke binta dashi Kusa da Ita ta Durkusa ahankali Tana Cije baki, cikin Manyantaka Maman Fati tace"Meya sameki kike Tafiya kina gwale kafa..? Gaban Ma'u ya Fadi Ta Sadda kai Tana Wasa da gefen Hijabinta Sake Kallonta Maman Fati Tayi kafin Tace"Magana nake..? Nace meya sameki kike Tafiya ba Daidai ba..?
Tafad'a Tana kara Hade Fuska,Cikin In ina Asma'u ke fadin"Ba...bakomai...mama.."Tsura mata ido Maman Fati Tayi Duk Tasan Halin yarta ammh kasancewarta Uwa gareta Dole Ta Lura da Komai nata Cikin Dauriya tace"Abdallah yayi miki Wani Abu ne..? Kunya Takama Asma'u Ta sadda kai kafin Ta gyada Kanta,Dan Mirmishi Maman Fati Ta saki kafin Tace"Baki Shiga Ruwan Zafi bane..? Kanta na Kasa Tace"Na Shiga..."Rausayar dakai Tayi Tana Fadin"Ok Shikenan Tashi Kije Kidaawo Ina Jiranki.."Da Toh Ma'u Ta amsa kafin Ta Mike Ta Fice Daga dakin Maman Fati Na Binta da Kallon burgewa.
Tana Zuwa Hajiya Tatashi Ta Rmugumeta Cike Da Farinciki Falo Hajiya Taja Hanunta Suka Fito Ganin Abdallah na salla Adakin Hajiyar,Haka Hajiya tataasata da Godiya da Nasihu Tare Da Rokonta Alfarma Ta Dage Wajen Ganin Abdallah ya Daina wasa da Ibadarshi sunanan Zaune ya Fito ya Nufi Shashen Mallam,Sun Kusa Kai Wajen Awa Daya Suna Hira da Hajiya kan Ta Mata sallama Tatafi Shashen Mamanta bayan Ta sanar da Hajiya Zata Dawo.
Tana Zuwa Already Maman Fati Ta Riga Ta Hadamata Ruwa mai Zafi Tana Shigowa Tace Maza Ta Tube ta Shiga Tiolet ta sake Gasa kanta,Kunya na Cin Asma'u tamike Ta Shiga Tiolet din Kuma taji Dadin Ruwan Da Dade Tana Gasa Jikinta Kafin Tafito koda Ta Fito Maman Fati bata dakin Rigar Jikinta ta Maida Tunda Duka kayanta na Mota.
yunwa taji Tana ji Sai Ta Hada Tea tasha Kafin Ta kwanta Bata koma Shashen Hajiya ba ganin Dare yayi Maman Fati Kuma Tana shashen Mallam,cikin su Fati Da Mahmud Ta Shige bayan Tayi Addu'ar barci Ta Shafesu Wayarta Takashe sai gobe zata Kira Aisha Suyi mgana
Bata kara saka Abdallah a idonta ba Sai da Safe dataje gaida Mallam,Ido kawai ya sakarmata yana Kallonta Ita kuma sai Taji kunya Dakyar ta gaisheshi ya amsa yana kara sakarmata Ido kasa kasa.
wanka kad'ai Sukayi bayan sun Karya Su Mallan Suka Tarasu Suka yi musu Nasiha Sosai Kafin Su Umarce Mamman Daya Tukasu zuwa gidansu bayan Mallam yabama Abdallah Key din Gida.
sanin Baizo da kaya ba Sai ya Diba kayansa Dake Nan aka saka amota bayan Ankwashe Duka kayan Asma'u daga Motar Abdallah Zuwa na Mamman, kafin su Tafi sai da Abdallah ya sallami Emeka yace ya Koma porthercourt Shi Ba yanzu zai Dawo ba,bayan ya Kuma gargadeshi Da Karya Kuskura ya sanar da Wasila Inda yake,akwai Amana Sosai tsakaninshi Dashi ya Tabbatarmai Da Cewa Insha Allahu ba Wanda zai Fad'amawa

أنت تقرأ
ZAMAN GIDANMU.
مغامرةLabarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.