Chapter 25

275 31 1
                                        

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

Ina masoya kayan ado da kwalliya, ina masoya dogayen riguna wato Egyptian Abayas masu kyau da saukin kudi..Ina yan kwalisa masu son kawata gidajensu da kayan kwalliya da gayu na zamani masu kyau, Aminci da karko a bisa kudi kalilan
*Maryam's Egypt Abaya* got you covered

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Join her grp via the link for breathtaking Abayas and beautiful home decors at affordable price.

            *🅿️25*

  Gefenta Abdalla ya Mirgina yana Maida Numfashi sama sama na Tsawon Minti goma, itako Asma'u tana Son Tashi Ta rufe jikinta ammh Takasa.
Abdallah ne ya Jawota Zuwa saman Jikinsa Tadawo Samanshi ya Kamata ya Kamkame kamar Wani Zai Kwaceta Kallonta yake Tana Runtse ido Lokaci Daya Hawaye Suna Zubomata, Wani Shaukinta ke Jansa ya yinda yaji kamar ana Sauke Mai Wasu kaya akanshi, yana jinsa Kuzarinsa na Dawowa yana Jin kamar an Sauke mai Wani Uban kaya mai Nauyi Aciikin Zuciyarsa Da jikinsa Gabadaya.
Harshe ya sanya yana Share Hawayen Ma'u yana Lashewa, Lokaci d'aya Kuma yana Kallonta yadda Ta Wani Narkemai kamar Wacce Ta Haihu, Hannu ya sanya yana Shafa kanta Zuwa bayanta Cikin Zuciyarsa yake Fadin"U are So Special Husna. kin Shayar Dani Ni'imar Da Ba Wata mace Data Taba Shayar Dani Duk na Dad'e da Wasila, Ada yana jin Dadin Mu'amala da Polina ammh daya Dandana Ma'u sai ya Raina Kansa dama Polinar gabadaya Ashe Inda ake Abu Dabam Shi Gabza kawai yakeci"
Da Wannan Tunanin ya kara matse Ma'u yana Fad'i afili.."Nagode My Husna. hakika kin Cika mace Tagari mai Farantama Mijinta Rai, kin Shayar Dani Madarar Dad'in da ba macen Data taba Shayar Dani. Husna karki Barni Don Allah Wlh sai yanzu Nake Kara Nadamar Abunda na aikata gareki dasu Mallam, don Allah kiyi Hukuri ki yafemin bada Sanina Komai ya Faru ba.."Yafad'a Yana Shafa Fuskarta Kafin ya sanya Hannu ya Jawo Blanket din Dake gefe ya Lulluba musu.
Itadai Ma'u batace Komai ba Saboda Taji Jiki, ganin batayi mgana bane yasa ya cigaba da Shafa Kanta Har Zuwa bayanta Cikin Salon Lallashi.
wanda Har Barci yafara Dibanta, ganin Haka sai ya Abdallah ya Lallaba ya Kwantar da Ita saman Katifa Shi Kuma ya Shiga Wanka,Yana Wankan Tsarki Ammh kamar yana Wanke Zuciyarsa Wani Nishadi yakeji Lokaci Daya Wani Shauki Da Soyyyar Asma'u na Shiga Cikin Ransa bayan yagama Wankan Tsarki ya Had'ama Asma'u Ruwa mai Zafi yana Fitowa Daga Tiolet din Kugunsa daure da Wani Karamin Towel Yana Zuwa yaye Bargon Datake Kudundune aciki ya Dagata Cak sai Tiolet.
Asma'u bata Farka ba Sai Da Tajita acikin Ruwan Zafi Kara Ta Saki Lokaci Daya Tana Bude Idanuwanta Da Suka Kumbura Saboda Kuka, Kokarin Tashi Take Saboda Wani irin Turirin Azaba Dake Fitowa ta Kasanta,Hannu ya saka ya Dannata Ciki Lokaci Daya Yana Shafa Kanta,kuka Asma'u Tafashe Dashi Tana Tsiyayan Hawaye.
  
Yana Shafa Kitson 2steps din Dake Kanta yana kallon Fuskarta yake Fadin"Shiii...Sry My Husna Yi hakuri Kinji...,nine ko..? Toh Bazan Kara ba,Ki zauna Saboda Ruwan Zafin ya Shigeki yadda zaki Ji Dadin Jikin ki Ok.."Idanuwanta Cike da Kwallah Ta Gyada Kai kafin tace"Kabarni I Will help my Self." Tafad'a Tana Turo Baki, Sha'awa Ta bashi Sai da ya Duka ya Sumbaci Lebenta kafin yace"Ok...Na manta Da Babbar Likita nake Tare Kin iya Wanka Tsarki..? Ya Tambayeta kai Tsaye .
Da Mamaki Ta Dago tana Kallonshi Kafin Ta makamai Harara Dariya yayi yana Rufe Baki kafin yace"Srry...Afito lafiya.  ko kuma in kin gama let me Know sai nazo na Daukoki.." yafad'a yana Ficewa Daga Tiolet Din Tabi bayanshi da Kallon Mamaki Lokaci Daya Tana Sakin Mirmishi, Tuna Yadda Abdallah Agidansu Dakyar yake Mgana ammh Daga jiya Zuwa yau Bakinsa ya Bude.
Sai da ta gasa kanta Sosai Domin Tasan Amfanin Hakan kafin Ta Yi Wankan Tsarki Ta Fito Tana Tafiya ahankali Saboda Yadda Takejin Zafi Daga kasanta.
Ta sameshi ya Sanya Kayan Jikinshi yana Zaune Gefen Gado da waya ahanunshi kamar Tata, Yana ganin Ta Fito ya Mike Da Hanzari ya Tarota ya Dagata Cak sai kan gado,duk Zulle Zulle Asma'u Shi ya shafamata Mai ya Kuma Maidata mata kayan Jikinta Ya Tsaya yana Kallonta  kafin yace"U look so Fine Acikin kayan Asibtin nan.."Yafad'a yana Shafa Hannunta Dake cikin Nashi, bata yi mgana ba Kanta na kasa Tana kurama Hannuwasu Dake Sarke ido.
Cikin Wata irin Murya yace"Kin yo Alwala...? Sallar Zamuyi Domin Kinga Har pass 1." Yafad'a yana Nuna mata Agogon Fatan Dake Daure A Tsiyayan Hannunsa.
gyada kai Tayi alamar eh baiyi mgana ba ya Sauko Daga Kan gadon ya Jawota da Hannu Ta Sauko Shi ya ja musu Jam'in sallar Har Suka idar, Farin ciki ya Cika Ran Abdallah ya Juyo yana Kallonta cikin Wani yanayi  Yake Fadin"Husna Ban Dace Dake ba.."
Yafad'a Fuskarsa na Chanzawa Dago Da kanta Ma'u Tayi kafin Tace"Kamar ya fa..? Tafada Cike da mamakin kalamansa Aranta Tana Fadin Nice Ban Dace Dakai ba,Domin Kafini Komai kai ba ajina bane.."Ya Katse Mata Tunani da Matsowa gabanta ya Kama Hannayenta Duka Biyun yana Fadin"Haka kurum Naji Husna Ina son gayamiki Wasu Sirrinka na, mun zama Daya Dani Dake,kuma Zuciyata Ta Aminta ta Zauna Dake Na Har Abada. zaki Iya zama da Wanda Yake Sabama Allah bayan Kuma yasan Hakan Babu Kyau..?
Yafad'a yana Kallonta Ido Cikin Ido Asma'u Ta Rausayar Dakai Kafin Tace"Sab'o kuma. ....? Tafada Tana Kallonshi cikin Raunin Murya Abdallah yace"Eh Sab'o Husna. Zaki Iya Zama da Mazinaci Irina Wanda yake Zina da Arniya Wacce Bata da Addini..?yafad'a Yana Jin kunyar kansa ammh Duka Idanuwansa na Kan Ma'un wacce Ta Zaro Ido gabanta Na Fadi Bakinta na Rawa Tace"Zi...zina kuma...?
Kai ya Gyada Mata yana Kara damke Hannayenta Cikin Wata murya mai Cike Da Rauni Da Nadama yacigaba da Fadin"Ke kadai kikasan da Wannan Sirrin,Basan yaushe na Koma Haka ba Husna..? bansani ba abu daya na sani Shine Abaya ba Haka nake ba, Ko kinsan Harta Matata Wasila Kafin Muyi Aure Sai da Muka Fara aikata Zina..? Ayanzu kam Hawayen Asma'u Sun Fara Zubowa Cikin Firgici Take Kallon Abdallah kafin tace"Duk meyasa Toh...kafi kowa sanin Illah Zina bayan Haka Kuma Haramun ce Allah yahanamu Kusantarta..".
Jinjina kai Abdallah yayi kafin yace"I know Husna ammh bansan meke Damuna ba Husna na Baki lbrina..? Na baki lbrin Irin bakin Cikin Dana Sanya iyayena kina Son ji..? Don Allah Ko bakison Ji ki Tsaya ki Saurare ni Ko Don kila Kema ki Gano ina Mtaalar take.. "Bata Samu Zarafin Mgana ba Abdallah ya Fara bata lbrinshi Tundaga Matakin yarinta makrantar, Girmanshi Haduwarshi Da Wasila yadda akayi Aurensu.
Haduwarshi Da polina Rayuwar Aurensu. komai Babu Abunda ya Boyemata kafin ya gama gaban Hijabin Ma'u ya Jike da Hawayen Tsausayin Rayuwar Abdallah,haka Shima Hawayen yake yana Fadin"Kema kin Tsauyamin ko Husna..? Plz Help me ki sanar dani in kinsan Meke Damuna, Husna Tun Ranar Dana Fara Ganinki Kika samu Matsugunni Araina Ina yawan Tunaki Domin Kingama Cika Dukkan Ra'ayi na Awajen ya mace. Sai kuma iyayena sukayi Tunanin Min gata Wajen aura min ke..? Ammah  sai na Watsa musu kasa ido Duk da Tarin Hakurin Da Suke Dashi akaina, Husna Karki ce Zaki barni Saboda Munanan Dabi'una I Swear Soyayarki Ta Cika Kirjina Tun Ranar Dana Fara Ganinki Adakin Hajiya, Bangane  bane sai yau Da Kika Taimake ni da Kyakyawan Dabi'unki Plz Husna Karki ce Zaki Barni am begging u Don Allah Ki Zauna Dani Ki Tallafeni...." Asma'u Ta katseshi Da Fadawa Jikinsa Tana Kuka Take Fadin
"Allah Ne ya Jarabceka Domin ya gwada imaninka yaya Abdallah Insha Allahu Komai Zai Wuce Kuma Allah Zai yafeka maka Duka Laifinka Haka Su Hajiya, Bazan Barka ba Insha Allahu Zan Zauna Dakai Cikin Kowani yanayi.."Tafad'a Tana Kuka Sosai Kamkameta Abdallah yayi yana Sakin ajiyar Zuciya Lokaci Daya yana Tusa kanshi awuyanta Sun Dade Ahaka kafin ya Dagota yana Share Mata Hawaye yana Fadin"Kuka..? Is ok Stop craying kinji Tunda Kince bazaki barni ba Soon Anty Tin Will be alrigt in sha Allahu"
Yafad'a yana jan Kumatunta,Shagwabe Fuska tayi Kafin tace"Kaima Kadaina Kukan Toh.."Mirmishi ya saki kafin yace"Me...? Kuka nake ai bansani ba.."Yafad'a Cike da Zolaya Hannu tasanya Tana Sharemai Kwallah Shiko yana Ta Kallonta Cike Da Sha'awa Hannunta ya Riko yana Fadin"Lokaci ya Tafi My Husna We Hv to go,Yau zaki tare agidan Mijinki No more Zaman gidanku yanzu ko...?
Da Mamaki Asma'u Ta kalleshi kafin tace"yau kuma...? Kai ya gyada mata Kafin yace"Yes..ko bazaki bini ba..? Shuru tayi kafin tace"Ina Zan Koma... ? Na zata gidanmu Zaka maidani..."Hancinta yaja kafin yace"Kinji ki Da Wata mgana,Gidanki zan Wuce Dake parthercourt ko Baki so..?"Ido Ta Zaro Batayi mgana ba.
Ganin Abunda Tayi ne yasa yace"Kin Tsorata ne..? Bakison nan..? Toh Zaki Bauchi..? Ido Ta sakarmai kafin tace"Eh ammh Banyi sallama da Kowa ba Abbana baisani ba.."Mikewa yayi yasa Hannu yana Dagota yace"baki da Mtsala da Wannan yanzu Zamu biya Namai bayani Daganan sai ki Dauko Abunda Zaki Bukata d Rest kuma Sai kiyi musu Ta waya.."Rau Da Ido Asma'u tayi bata samu Zarafin mgana ba Ya Dauko Jakarta ya Mika mata,Tare da Wayarta yana Fadin"U hv Some miss clls..."Karba Tayi Shikuma ya Riko Hannunta Suka Fito Daga Dakin. dama already da hijabi ajikinta wanda Tayi sallah dashi , Dakin ya sakama key ya Kulle ganin yadda Take Tafiya ne Yasa Ya Dauketa cak ya Sauko Kasa Da Ita bai Direta ko'ina ba sai abakin Reception Kunya ya Kamata ga Mutane nata Kallonsu Sunne kanta Tayi kan Kirjinsa Key din ya mika musu Kafin su Fice yana Rumgume Da Ita.
Emeka dake Cikin Mota yasha barci Har yatashi basu Fito yafita yaje Ya Siya abinci yaci Ya Dawo Motar Kenan Yaga Fitowarsu Da hanzari ya Fito Daga Mota yazo ya Bude musu Gidan baya Suka Shiga kafin ya Rufe ya koma bangaren Direba yaShiga yaja Suka bar Haraban Hotel din.
Asma'u ke tama Abdallah Kwatance Shi kuma yana Gayama Emeka Don bai yarda Tamai bayani Da Kanta ba,Cikin Ikon Allah Sai gasu akofar get din gidansu Inda Suka Iske Abba Tsaye Shida Baban Aisha Suna mgana da alama Tun bayan Fitowarasu Masallaci ne Suke Tsaye Awajen,gaban Ma'u ya Fadi Cikin Rawan Murya Ta Kalli Abdallah kafin tace"Na Shiga uku  ga Abba chan."
Tafad'a Alamun Tsoro Sun bayyaana Gareta Kallon Su Abba Yyi kafin yayi Mirmishi yana Fadin"Toh Shine me..? Mijin ki ne Fa Bawani Chan Dabam ba,Let go ni zan Fita namishi bayani.."Yafad'a kai Tsaye yana Rikota Hannunta lokaci Daya Ya Bude Murfin Motan Ya Fito Tare Da Asma'u Wanda Caraf Suka Hada Ido da Abba Da Baban Aisha Domin Tun Sanda Motar Ta Tsaya Akofar gidan Taja Hankalinsu.
Jikin Asma'u na Rawa Ta Fizge Hannunta tayi gaba Ammh Sai me Zafi ya Tsirga mata Daga Kasaanta na Kokarinta Na Had'e Kafafunta ,cikin Sanyi Jiki Ta Kasala Ta Karisa gasu Abba Abdallah na biye Da Ita abaya yana Mirmishi Saboda ganin yadda Take Tafiya.
Rankwafa Tayi Tana gaida Su Abba,Baban Aisha ne ya amsa yana Kallonta kafin Abba yace"Ke  Asma'u Motar wa kika Fito yanzu..? Waye wannan..? Kafin Asma'u tasamu Bakin Mgana Abdallah Dake Bayanta yace"Nine Abba.."Yafada Cikin Alamun Jin Kunya Lokaci Daya Yana Durkusawa Abba na Kallonsa Da Mamaki yace"Kai ne Wa..? da'n Saurayi Ban Ganeka ba..  ?
Asma'u ko ganin Abdallah ya Kwaceta yasa Ta Fada gida da Sauri Tana sakin ajiyar Zuciya.
Shiko Abdallah kansa ya Shafa da ba Hula Duk Kunyar Kananun kayan Jikinsa Sun kamashi Cikin Kamala yace"Abdallah ne Abba.."Yafad'a yana Sunkuyar Dakai,Abba da Baban Aisha Suka Kalli juna kafin Abba ya kara Kallon Abdallah Dakyau kafin ya ganeshi Domin Ranar Daurin Aure Kawai Yataba ganinshi Shima Cikin manyan kayane Sabanin na yau cikin Kananan kaya.

Abba ne yace"Oh Ko Abdallah na Bauchi Mijin Asma'un..? Kan Abdallah na kasa Yace"Eh nine Abba Na sameku Lafiya..? Abba Da Baban Aisha Suka amsa da Lafiya lau kafin Abba yace"masha Allah sannu Shekaran Jiya kuwa Muke Zencen ka Da Mahaifinka ya Jikin naka..? Cikin Muryan Kamala Abdallah yace"Na Warware Abba.."Abba yace"Masha Allah Abu yayi kyau.."yafada Muryansa Na Nuna Jin Dadin dayake Ciki.
Abdallah yace"Abba Dama..Dama nazo Tafiya da Husna na ne Zata tare agidan Mijinta, kuma Abba ayi Hakuri da Abunda ya Faru abaya...Allah yaasa banyi Laifi ba.."Abba yace"Ko Daya Wlh Ai Daman metake Jira An Daura sai Tarewa agidan Mijinta Shine Martaban Kowacce Mace Babu Komai Ko Mallam Wada.."Babansu Aisha yace"Hakane Kam..Dama ai Shi Yafi Chanchanta daya Zo ya Dauki Matarshi Tunda Dai ga yadda Abubuwa Suka Faru.."Abba yace "Toh bari na Shiga Cikin Gida na Sanar da Iyayenta yanzu Zata Fito ku  Tafi Kaji.."
Abdallah yace"Toh Abba kafin ya Mike Tsaye Da Hanzari Abba ya Fada Gidan,yana kwalama Su Umma Kira,Asma'u ko Tana Shiga Tsakar Gidansu Taci Karo da Umma, ta gaisheta ammh sai Bata amsa bata Takoma Tana Binta Da Kallon Mamakin ganin Da Ma'u tayi Umma na Kallonta Daga sama Har kaasa,sai Ta Targu Tafara Kokarin Hada Tafiyarta ammh Duk Da Haka sai Da Umma Ta Fahimci Wani Abu salallami Tafara ma'u bata Kulata ba Ta Bude Dakinta Ta Fad'a.
Jin Salatin Umma ya Fito da Mama da Anty Amarya harda Ma Hajiya iya Suna Tambayanta Lafiya..? Karkace Baki Umma Tayi Tana Fadin"Nida yarinyarnan ne Asma'u ne, Tun Jiya da yammah Ta Fita gidan sai yanzu Take Shigowa da Uwar Ranar Nan Abunda Yabani Tsoro Da Ita gani Nayi Tana Tafiya Kafarta agwale Kamar Wacce Namiji yayi ma aika aika.."Hajiya Iya Ta Tabe Baki Tana Fadin"Toh ai Ba Abun mamaki bane, an saba Gantali Wlh Banyi mamaki ba Wani Namiji Takaima Kanta Domin Ke ko An Dade agida.."
Anty Amarya ce Ta Dafe Kirji Tana Fadin "Haba Umma Wannan Wata Irin Mgana ce,Kin Fi kowa sanin Asma'u Wannan ba Halinta bane ko Abaya balle ayanzu Datake Matsayin Matar Aure..."Wani kallo Umma Ta Jefamata,Asma'u ko na Ciki Tana Ji Mirmishi kadai Tayi Tana Dauke Hawayen Fuskarta kayanta Take Hadawa Dama Duka akwatinta Abba yace akawo Mata Dakinta,So Abubuwanta masu  muhimmanci take Diba Tana Sakawa Acikin Akwatinta na Gida Cikin Wannan Halin Ne Taji Muryan Abba ya Shigo.
Da Mamaki Su Umma Ke Kallon Abba Kafin Suyi mgana yace"Halima  Da Mandiya ku Taimakama Asma'u Ta Hada Kayanta ku Fito Da Akwatunan Nata Yau dai Allah ya Nufa ga Mijinta chan Awaje yazo Tafiya Da Ita.."Umma Ta Zaro Ido Kafin Tace"Mijinta kuma...? hajiya Iya ko cewa Tayi.."Mijinta..? au dama Bai Saketa ba..?Abba ya Kalleta yana Fadin"Wata irin mgana ne Haka Iya..."Kyabe Baki Tayi batayi mgana ba Anty Amarya Kuwa Cike Da Farinciki ta Shige Dakin Asma'u Tana Kiran Sunanshi Abba Ko juyawa yayi yana Fadin"Ke Asma'u ki Hanzarta Don Kar ki barshi Jira.."ya Fice
Umma Da Taji Jiri na Dibanta Mama ce Ta Koma Daki, Umma ki Tana Tsaye kamar An Dasata Agaban Idanuwanta Anty Amarya Keta Fito Da Kwatunan Asma'u,sai gashi Sun Fito Tare Ma'u Ta Chanza kaya Zuwa Wata Bakar Abaya Eypet a baya  ta yane gyalen Rigan Akanta Tana Rataye da Wata Bakar Jakarta wayarta na Hannunta Har kasa Ta Duka Tana Fadin"Umma,Hajiya zan Tafi.."Umma kallonta Take Cike Da Bakim Ciki Takasa Mgana Hajiya iya ko Tabe Baki Tayi Tana Fadin"Umh....toh Allah yasa Kada bayan An Tafi Kuma adawo" Asma'u Tayi mirmishin Tace "Karki Damu Iya Insha Allahu Tafiyan Kenan Da Yardan Allah Nayi bankwana da Zaman Gidanmu sai dai Nazo na Wani Dan Lokaci na Koma Na Tafi.."Tafada Tana Mikewa Mama ce Ta Fito sanye Da Mayafi Tana Fadin"Allah Sarki Ma'u komai nada Lokaci.."Tafada Tana Karisawa Gareta Ta Riko Hannunta,Sai ga Ammi Ta Shigo Da Murnata ta Rumgume Asma'u Tana Mata guda a Kunne,Anty Amarya Dake Tsaye Ta Sanyo Hijabi Tafara Jidan Akwatuna Tana Fadin"Mama Ku Dauko Don Allah Mu Fita Dashi Waje."Tafad'a Tana Ficewa
Tana Fita Megadi ya Amsheta,Ya Fita dashi Inda Abdallah ke Tsaye Gefen Mota Hannuwansa Duka Cikn Aljihun Wandonsa yaTsurama Kofar gidan Nasu Ido.
yana so yaga Ta Inda Husna Zata Bullo Su Abba ko na Gefe Tsaye,Ganin Megadi da Kwatuna Guda Biyu ya sanya Emeka Fitowa ya Bude Booth din Motar Megadi ya saka, komawa yayi Nan ya Hadu da Mama Ta Dauko ya Karbeta Shi ya Kwaso Sauran Duka Emeka na Karba yana Sakawa Cikin Booth.
Ammi da Anty Amarya da Mama Suka Fito da Asma'u Wacce Taji Tana Kuka Tarasa Kona Farin Ciki ne ko akasin Haka,Umma Kuwa Saboda Bakin Hassada Da Kyashi Sai gata Ta Fito Domin Gani Take kamar karyane ba Gaskiya bane,Abdallah ya Gaishe Dasu Ammi suka Amsamai Cikin Sakin Fuaka Kafin ya matsa Su Saka Ma'u Cikin Motan Suna Fatan Allah ya kaisu Lafiya.
Abdallah har Wajensu Abba Ya koma yayi Musu sallama Kafin Ya Komo ya Shiga baya Inda Asma'u ke Zaune Tana Kuka Har Emeka yaja Mota Su Ammi na Daga Musu Hannu Cike Da Murna Har Suka Fice Daga Layin.
Umma na baya Sanda Motar Su Abdallah Tabar Wajen,Saboda Bakin ciki Wajen Juyawa Ta Shiga Gida Sai da Ta Had'a Goshinta da Get tsabar Bata gani Saboda Bala'in Bakin Ciki da Hassada

*Janafty*

ZAMAN GIDANMU.Where stories live. Discover now