Chapter 19

199 22 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KO DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI SAIWOWIN SANYI*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABARU*
*AKWAI SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI SAIWOWIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

        *🅿️19*

Su Anty Nafisa Ruwa kad'ai Suka Sha kafin su Umarci Su Anty Amarya dasu Ammi da Anty Bilki dasu kariso Kusa Nan Suka Fara Bude Akwatuna,Masha Allah kadai Ammi da Anty Amarya Ke Fad'i.
A yayinda su Anty Bilki da Anty Rukayyah Suka jige da Gumin Hassada Da Mamaki, Akwatuna Dozen Cike Da kayan Arziki Abun sai Wanda yagani,Daga karshe Anty Safina Ta Bude jakarta ta Ciro I.V Da Kuma Kudi Dubu 100 cash ta Mikama Aisha Tana Fadin"Ga katin gayyatanku da Kuma Kudin Hidimar Amarya inji ango, yace Amai Afuwa bai kawo Da Wuri ba,Bai samu Dama bane,yanzu Haka sai ana gobe Daurin Aure Zai Taho.."Washe baki A'isha tayi Ta karba Tama kasa mgana,Fa'iza ce ke sakin Guda Lokacin da Ammi Suke kara Daga kayan.
Abun Mamaki Harda Mama acikin masu Daga kayan Suna Yabawa Ita da Su Anty Amarya,Umma ko na Kofar Dakinta Tana Kallon Abun Mamaki,Babu Inda Jikinta baya Rawa,Saboda ganin yadda Allah ya Maida Asma'u lokaci Daya.
Hajiya iya ko Na gefe tana Wurga ido Tare da Jinjina ma Wanan Uban Dukiya Da'aka Narkoma Asma'u.
Aranta Tana Fadin lalle Wannan Mijin Na Ma'u Da Danginsa Duka Sun Taki arziki,Kaya fa sunyi Abun sai son Barka Anty Amarya Tayi Guda kamar hancinta Zai Fita Saboda Murna,Dakyar Su Anty Safina Suka ci abinci bayan Sungama Sallah Shima Din Sai da Ammi ta matsa musu,suna gamawa around 2 Sukayi Haraman Tafiya 20k Ammi ta Dauko Suka Basu Ammh Faufau Sukaki karba,Ganin Sun ki karba ne Aka Sanya Musu Toyen Toyen da'aka yi musu amota Suka Tafi Dashi bayan Su Jadadda gaisuwansu zuwa ga Asma'u Amarya bayan Sun Fito ne Su Anty Amarya Sun Rakosu Suke Shaida musu Gobe Mota zatazo ta kwashi kaya da kuma yan Danki,Abun yayi ma su Ammi Dadi Sosai,ko bayan Tafiyarsu ma Makotane ke Ta Shigowa ganin kaya Itako Anty Amarya bata gajiya da Bude ma Mutane cike Da Farinciki.
Umma dai da ya'yanta Daki Suka Sulale Zuciyarsu Cike Da Bakinciki Ayayinda Fa'iza da A'isha Suka karbi Key din Dakin Ma'u suka Shiga Suka Zauna Suna Hira gefe daga suna kallon Rantsatsun katinan bikin Asma'u Su kansu Duniya Ne.
Abba ya Riga Asma'u Dawowa koda ya Dawo Dama Tuni Anty Amarya ta Sanya an kwashe akwatunan an Shiga Dasu Falonsa yana Shiga Dasu yaci Karo,Koda ya Samu Lbrin Kayan Auren Asma'u ne Fuskarshi ya cika da Annuri da Farinciki yayi ta Sakama Asma'u albarka yana Fadin Wani Jinkirin Alheri ne,Asma'u bata Shigo gida ba Sai Shida da Wani Abu Na yammah lokacin Wasu masallatan Har Su Fara Kiran Sallar Mangariba
Tayi Mamakin ganin A'isha Da Fa'iza Ammh Mamakinta ya Shanye Lokacin da A'isha Ta Mika mata Katinan bikin da Kudin Hannunta tare Da Sanar da ita dazu Su Anty Safina Suka Tafi Sun Kawo Mata lefe
Cike da Mamaki ta Waro ido Lokaci Daya Tana Bin Sunanta Dana Abdallah Dake Jere jikin katin da Kallo,Kudin da A'isha ta bata tasake bi da kallo Tana mamakin yadda Abubuwa Suke Zuwarmata Batare Data yi Tsammani ba.
Bata samu gwanin Lefen Nata ba,Sai da Su A'isha suka Tafi bayan Ta Ce ta karbi Kudin ta Ijiyesu awajenta,Batayi gardama ba Ta karba.
Da Farkoma Harda katinan Ma'u taso Ta bata taki Karba Duka 50 ta Diba ta Barma Asma'u 50 din Saboda Rabon Yan Asibitinnsu da yan Gida,Fahad ne yazo ya Dauki A'isha bayan Sun Tsaida Mganar kan gobe Ma'un Zata zo gidansu A'isha Su Tattauna Tunda aikin Dare Gareta goben.

Asma'u Na Digar Da hawaye Lokaci Data ga Lefenta Wanda aka Kashe Tarin Dukiyar wai Da Sunan Nata,Ada batama Tuanin Lefe ita kawai Allah ya Kawo Mata Miji koda Bai dashi ne,Ya Aurenta ya Rufamata Asiri sai ga Shi Allah ya Darajata ya kuma Daukaka Aurenta Fiye Da Kowacce Mace acikin Gidansu lalle Allah ne Abun Godiya.
Ranar Asma'u kwana tayi Sallah Tana Mika godiyar ta ga Allah Tare Da Addu'a Allah yasa Wannan karon Ta Tabbata Amaryar gaske bata bogi ba,Kamar yadda yake Faruwa Achan baya.
Tun Daren Anty Amarya Ta Sanar dasu Umma gobe za'a Bauchi jeran Asma'u Duk mai son Zuwa kofa abude Take,Umma Dai Ko Fitowa batayi ba, Mama ce Tace Zata,Anty Amarya tace Allah ya Kaimu.
Washegari kuwa Tun Wajen 10 direban Motar da Zata Dauki Kaya Suka Iso Shida Mamman Wanda zai Dauki Mutane,Lokacin Tuni Su Anty Amarya sun Shirya Harda mama. Motar kayan Ammi Ta Shiga Zuwa gidan A'isha aka kwaso kayanta na Chan gidan,harda Wanda take Siya Tana Tari da Kudin albashinta,tana Tarawa agidan  Aisha,Bayan sun Dawo Ammi ta Fito da Sauran Da kenan,Harda su kayan Gara komai buhu,Daga Umma wacce Hajiya iya tama Fada,Shine Ta Shirya Har Mama baki Suka sakii suna mamakin Duk Yaushe akayi Wannan Siyayyar,basu gama mamaki ba,Suka ga Ana Fito Da Botikai Na Roba manya Guda Goma Jerin kayan Fulawa Kenan,Mota sai da Ta cika Kafin Su Fara yin gaba.
Abba na Kofaar gida Lokacin Ranar Bai Fita ba Itako Ma'u Tun Safe Tana Gidan A'isha Ta Tafi da kayan aikinta Daga Chan Zata Wuce Asibiti
Mama da Umma sai Anty Amarya Da Ammi Suka Shiga Motar Mamman yaja suka bar Kofar gidan Namu Abba Namusu Fatan Adawo lafiya,Koda 2 tayi Suna gidan Asma'u Dake Gra Duk da Motar kayan ma Ta Ragasu isa,Nan suka iske Su Anty Safina da Anty Zainab Datazo jiya Sunzo musu da Abinci Da Kuma Maza Wadanda Zasu Kafa gadaje su kuma Sanya kujeru Tunda Abun na Kamfani ne, su Saji Da Shirya kayan kichen.
Sun Samu Tarbaa na Musamman,Sai Da Sukayi Sallah kafin Su ci abinci mai Rai Da Lafiya White Rice ne da Miyar Tumatar Wacce Taji kaji,Sai pepe meat,sai slat,Sai lemuka da Kuma zobo,Kowa yaba gidan Ma'u yake acikin Ransa.
Hatta da Umma ko Domin Kaf ya'yanta ba Wacce Ta Kama Kafar Ma'u,Har gwada ma Rabi'ah mijinta nada rufin Asiri,Suna gama cin Abinci Suka Mike Suka Fara aiki.
kitchen suka Fara Kimtsawa ko kafin Su gama An kafa gadaje da Kuma Kujerunta Farlo da Kuma Dinning Abun sai Wanda yagani kafin La'asar Sungama gyara Ko'ina nan fa Anty Amarya Dasu Anty Safina aka Shiga Zuba Video ta ko'ina Umma Ko na Gefe gaba-daya a muzance Take Saboda Abubuwn Da bata taba Zato ba,Mama ko Kusan ba'a gane meke Ranta Ammh tasaki jiki ba Kamar Umma ba
Daganan Kulle gidan Sukayi Mamman ya Kwashe su sai Gidan Proff. wannan Shine karon Farkon Haduwar Umma da Maman Fati Tun bayan Barinta gidan,Umma ta Jinjina ma Dukiya irinta proff.ta kuma Tabbatar Daga Habiba har yarta Sunyi gaba Sosai ganin irin Makeken Gidan da Maman Fati ke Ciki,Nan ma Sun samu Tarba na Musamman Hajiya Da Maman Fati Suna Ta ina Zasu Saka Dasu.
Umma da Mama Bin Maman Fati kawai Suke da Kallo gasu Mahmud da Fati Suna Ta Wasansu wanda kallo daya zaka Samu ka Fahimci yaran Suna Cikin jin Dadin Rayuwa Masha Allah.
Salar La'asar Kad'ai Suka yi wannan Karon ba Mamman bane ya Koma dasu ba,Motar Haya aka Samo musu Suka Shiga Suka koma Dutse Cike da Labaran Abunda ya Faru A Bauchi Umma ko Tana Rawan baki Tana Bama Hajiya iya Lbrin irin Daular Da Ga Habiba ke ciki, Abun baima Hajiya iya Dadi ba Domin taso yarda Ta Fidda Habiban agidan Ladan To Rayuwarta ta lalace Sai dai Ta Manta Allah ne mai Komai Kuma Dama wani Hanin ga Allah baiwa.
Tun A ranar Umma ta Dinga kiran ya'yanta awaya tana Tsegunta musu Su Anty Bilki sun Jinjina lamarin Sosai
Anty Rukayyah ko Cewa Tayi ba girimgirin ba Tayi mai,Fa'iza ko ba wanda ke takanta Domin Ba Wanda ya Isa Yarabata da Asma'u Umma tayi Dukan da Fadanta Tun Suna yan'matanci kafin Su kawo yanzu,Rabi'ah ko tana Jigawa Ammh Tace sai Tazo tabama Idonta Abincin Wannan Daular da'akace an kawo ma Asma'u wacce Suke Tunanin Har Abada bata kai Wannan Matsayin ba.
Itako Asma'u Ranar Datayi night Duty Ranar ta Rabama Duka Abokan aikinta katin Daura Aurenta Harda manyansu Likitoci da Ma'aikatan Wajen da Suka Saba Kuma tayi Sallama Dasu, Domin gobe ne Daura Daure,Sunji babu Dadi Sister Bahijja da Suka Saba Harda Kuka.
Ita kanta Asma'un Ta koka ko Domin yadda Takeson Aikinta ammh Jin Dadinta Daya Da Hajiya ta Sanar da Ita Mallam yace Zai Mata Cucuku A maidata Babban Asibitinnsu na Bauchi,Daganan Bata koma gida ba,Gidan A'isha Ta Koma saboda nan Suke Tsara Komai Ita da Fa'iza Tunda ba Kawaye Gareta ba.
Anan gidan A'isha akayi musu kunshi mai Kyau ita da A'isha da Fa'iza,Abun sai wanda yagani,Sai da daddare Fahad ya kawsosu Dukkansu Harda A'isha ya kawosu Gidansu Ammi nan zasu Kwana,abinci kuma A'isha ta bayar ayi musu ne,Duk da Asma'u batayi Gayyaba A'isha tayi Saboda Ta Gayyato musu yan Makaranta su na Boko dana islamiyya kowa yaji Asmee Ladan Zatayi Aure Sai yayi murna Kuma yayi alƙawarin Zai zo Duk da Ko yawancinsu Sunyi Aure.
Anan Asma'u ta iske Dangin Mamarta Daga Bauchi Sunzo,Mota guda Fadawa jikin Goggo Jummai Tayi tana Murna Don Bata Zata Zuwansu ba.
Gidan Ammi Suka Sauka Suna ta Aikin wanke kayan Miya Domin anan Zasu Nasu bikin,Da Ta Shiga cikin Gida Kuwa Dangin Abbaa ne Da Su Umma da Mama,da ya'yansu kowacce tazo,cike Da Fara'a Take gaishesu, Ranar ma Sai da Hajiya iya ta yabamata Mgana wai Tana Amarya sai Shigen bakin yawo an saba Baza'a iya bari ba,Ita dai batace komai ba,Dakin Anty Amarya ta Shiga Ta dau Abunda Zata, dauka Tunda Tun Shekaran Jiya ta Kwashe Abubuwanta masu amfani Daga Dakinta Domin Hajiya iya Nata Bala'in Taki Kwashe kayanta Ko Zaman gidan Bai Isheta bane,Nan ta Fice Yan'uwa Su Anty Amarya nata Tsokanarta Suma Suna aikin ne,Tana komawa gidan Ammi Goggo Jummai  Tajata kurya Daki Ta Bata Kaza Akula wacce Tasha Hadin magani sai Wani Ruwan Tsumi jakarka Guda wai Kuma ta Shanyeshi Daga Dare Zuwa Safe,karba tayi Tana Tura baki Su A'isha Na mata Dariya.
Abba Kuwa Tun adaren yasa aka Share Farfajiyar gidan da Waje,Washegari Tun Safe Masu Canofi suka Zo Suka Kafa A ko'ina Saboda Rana Tunda Daurin Aure karfe 1pm ne na rana.
Shima Anashi barayin yayi Gayyah Sosai shima kati ne ya Buga yayi Ta Rabo kamar yadda yakeyi A ya'yansa na Baya.

ZAMAN GIDANMU.Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ