Mommah's ❤️
Ke dabance
Loving maeelBiyayyata
1
"Ke kam wllh bansan ranar da xaki rage son bokon nan ba"cewar wata mata da baxata wuce shekara 45 ba amma jikin ta bai nuna hakan ba,fara ce sosai dog doguwa bata da jiki sosai xaune take akan tabarma ta kula gyada aleda don sana'ar ta kenan aduniya " mama wllh ina son karatu ba don komai ba sai don nayi ilimi na zama babbar likita " ta fada da dan murmushi a fuskar ta don har tana imagining kanta anan gaba ciki farar labcoat tana xaune a office dinta mai kyau "toh allah ya nuna min ranar mamana" mama ta bata amsa "amin"
Kaduna
"Hello" " amma wllh nadia baki da mutunci ace ni mai yara na fito tun daxu amma ke da baki are kowa ba kina can kwance kirjin miji kin barni axaune xaman jiranki" aka fada cikin way wayar " wllh ba haka bane kawata deen ne wllh ya tsaida ni kin san shi baya son mace tana rigashi fita daga gida,amma gani nan xan iso ynxu " ta fada tana mai Jan kofar entrance din falon ta sa mata key,parking space ta nufa ta ma motar ta key ta shiga mai gadi ya bude mata gate ta fice daga gidan.
Bata tsaya ko'ina ba sai wani babban shagon salon dake 7brothers plaza a kaduna wuri ne mai girma da kyau ba kowa ke ziyartar wurin ba sai masu kudi,sauka tayi daga motar ta dauki Jakarta mai tsada maroon Wanda ya shiga da shaddan style din bubu dake jikinta,gyalenta ma dan karami medium Wanda akafada ta yafashi sai bul bula kamshi take baxaka taba zaton matar aure ce sabida hatta gashin kanta bata boye ba wacce ta tufke shi tayi daurin zarah buhari akai,tafiya take a ahankali da high heel din dake kafarta Wanda daka gani xaka san da sabo sabida ita nadia takalmanta kenan only her house shoes ne flat,washe baki sakina tayi data hango kwarta tashigo shagon "my friend sannu da xuwa amma fa kin shanya ni" tafada ta mai tarar ta " sorry kawata amin afuwa" ta maida mata tare da janta kan kujera suka xauna bola ce yar aikinta ta karaso " madam welcome" "thank you bola hope everything is fine" " yes ma'a""Mutumina gobe fa nake son xuwa gida dubo Iyali na" ahmad ya fada yana diban abinci yakai bakin shi " ba munyi da kai sai next week ba? Why did you change ur mind" yafada ba tare da ya bude idanunsa ba " madam ce take missing dina tace in ban dawo ba gobe xata iya fada rashin lfy" ahmad ya fada yana dariya tabe baki yayi yace " allah ya kaimu " " da madam xaka je ne" baxan ya masa don ya san da gayya ya masa tambayar dariya ahmad yayi ya cigaba "wllh ni ma na kosa na koma gun aisha I miss her wllh not jst her food har da,," dan allah mu bar maganar nan wai kai baka da aiki sai surutu fadi ba a tambayeka ba" tintsirewa ahmad yayi da dariya yace" aa wllh dole na fadi ynda nake ji game da matata at least ni ina fada kai fa?" Yayi tambayar yana leka fuskar shi don tsokana mikewa yayi ya dau phone dinsa da key yayi waje ahmad nakiran shi yayi mai banxa motar shi ya shiga ya bar kasuwar koh nashi shagon bai kuma leka ba, ranshi ne ya kara baci da ya tuna shi matar tashi ma daban take bbu abinda ta iya sai yawo all d time ace yau weekend she can't stay at home da shi ba kara speed din motar yayi ranshi na kara kuna.
" mama mama mama ina kk" alama mama ta mata akan tana bayi amma bai hana fareeda cigaba da kiranta ba " ke ban son sakarci fa " mama ta bata amsa tana fito daga ban dakin rungumeta fareeda tayi tace " mama na samu wllh na samu admission din" " masha allah allah mun gode ma,ynxu mama na sai makarantan jami'a kenan"mama ta fada ta murnarta " ai kuwa dai mama " "wai murnar me ake ne haka ko dai aure xakiyi ne adda" cewar kanwarta nana data tashi daga bacci sabida hayaniyar fareeda Harara ta watsa mata kan tace " da yake ke shi ne agaban ki ba,toh admission nasamu yarinya" tabe baki nana tayi tace " admission toh auren fa" ta fada tana kallon mama " wllh mama ki mata magana nifa wllh ke ke hanani dukan ta " tafada kamar xatayi kuka ta shige daki mama ta juyo kan nana " baki da Kunya koh yayar taki kk raina haka koh" " mama xancen danayi ynxu na raini ne kuma" " na dai fada maki ban son rashin kunya tom" " naji allah ya bata hakuri" daga cikin daki fareeda ta amsa mata " ameen " mama ce ta shigo dakin ta xauna kan kujera ta dubi fareeda tace "toh yanxu sai me kenan xa ayi" washe baki tayi tace " mama registration xaje inyi sai na fara xuwa" " toh nawa ne kudin" " usman yace da komai da komai na rike 70k sabida har da kudin hostel" dan tunani mama tayi kan tace " mamana ban tunanin muna da wannan kudin fa sabida karatun likitancin ne akwai tsada" annurin fuskar ta bai gushe ba tace " mama ni ynxu xanje gun hajia muyi lissafin kudina duk mu hada ai ina ga xai isa insha allahu" jikin mama yayi sanyi tace " toh allah yasa" " ameen bara naje na fada mata don next week xan tafi" " ban gane ba xaki tafi ina" mama ta tambayeta tana mai kallon ta hadiye yawu fareeda tayi tace " mama na manta ban fada maki ba ai karatun ba anan garin bane" " bangane ba toh aina ne" shuru tayi bata ce komai ba " tambayarki fa nake kin min shuru" "Abuja ne mama" cewar nana ta shigo dakin ta zauna gefen mama don tasan akwai drama yau " Abuja, Abuja fa kk ce nana" " wllh kam mama " nana ta kara fadi tana mai kallon fareeda wacce banda harara da mugun kallo bbu abinda take jefen nana dashi " wai haka mamana" ta jiyo murya mama akanta " eh mama amma dan" " kE" mama ta mata tsawa Wanda duk sai da suka tsorata don rabon data yi haka tun suna yara " baki isa ba,ba kuma dani ba ban da aure bbu abinda xai fidda ku gabana" mama ta fada cikin baccin rai " mama ta shige daki.Hi guys
Nasan wasun ku sun karanta books dina abaya wasu kuma basu sanni ba,amma am very sure xaku so litafinan sosai please try and read,like,follow and repost 🙏 nagode
Mommah ❤️