Akwana a tashi bbu wuya agun allah gobe ake sallah kowa na ta shirye shirye masu dinki sun karbo,haka xalika masu kitso da lalle duk sun yi wasu kuma na kan yi amma banda fareeda
Wacce ke kwance tun safiya cikin bargo sakamakon zazzabin da take ji
Mami tayi tayi karya azumin don shan magani koh su tafi asibiti amma fir taki
Karshe dai tace toh tayi kwanciyarta adaki don samun hutu
Fareeda
Ita kadai tasan abinda ke damunta ba iya zazzabin bane har da kewar deen da take gashi tun da taxo bai taba kiranta baSai dai ya turawa salman kudi yace abata tun tana amsa har ta ce da salman kawai ya rinka aje mata in tana da bukata xata mai magana
Khady
Sosai take farin cikin don ta kagu ta kasance tare da yaya ahmad din ta,salon taje aka mata wankin kai da gyaran jiki sai sheki takeBatayi lalle ba sabida bikinta da za ayi nan da sati biyu
Deen
Kula iya kula yana samu yanxu gun nadia amma duk da hakan bai hana shi kewar fareeda baAllah allah yake bayan sallah da sati daya yayi ya je kaduna da sunan bikin khady yaxo dana amininshi ya ga fareeda
Washe gari ran sallah haka yayi ta zuba ido yaga koh khady xata sa hotunan fareeda a status da suka je sallar idi amma shuru
Sai na wasu mutanan daban take ta sawa haka ma salman da shi na su mami yasa sai anty amarya don abba baya gari sai na anty bilkisu da yaranta sai kuma nashi
Tsaki yayi ya cillar da wayar kan katifar da yake kwance ya dubi nadia da tayi kwalliyarta cikin shadda blue yasha aiki da stones
Ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi kyau sai kamshi take tana tattara plate din daya ci cin cin da samosa ya tashi
"Babe ina kk son muje yawon sallah"
Murmushi tayi"babe any where u want xan je" ta bashi amsa"Do u want to travel out sai kiyi holiday dinki ma"
Aje kayan tayi kan cafet ta dawo gefensa "da gske babe xaka bari"
"Why not " ya daga mata kai "jst tell me ina kk son xuwa aw book a flight "
"Ahhh babe am so happy I love u"tafada cikin farin ciki tare da rungumeshi
"Naji naji kar ki karya ni baki ban amsa ba"ya fada yana shafa bayanta
"Babe av always wanted to visit Italy "
"Then Italy it is " ya fada yana Jan wayar sa ya dan yi ayan latse latse na yan mintuna tana nan xaune tana kallonsa ya gama ya dago
"Get ready u r going to Italy tomorrow "
Kara rungumeshi tayi tana masa godiyaNace kada ki akayi baki sani ba 😆 🤣
Fareeda
Da kyar ta samu taje sallar idi nan ma data dawo sai kawai ta sauka gidan su nan ma still kwanciya tayi"Adda wai baki xuwa yawon sallah ne naga sai lebe wa kk yi kamar wata tsumma a randa" cewar nanah tana bude kulolin abincin da aka aiko dashi daga gidan su mami
Banxa fareeda tayi mata don ynxu ita magana ma ba son yinta take ba
"Toh ni dan allah ki aramin wayarki nayi hoto kyan nan sai an aje tarihinta "
"Kinji adda" ta kuma fada ganin fareedar bata da niyar kulata
"Ke wuce kar ki dami mutane baki ganin bata jin dadi ne kk xo kk wani isheta anan" cewar mama dake xaune tana cin abinci
"Ayya nifa waya fa kawai nace a aramin toh bara na je shagon ya usman na ari nashi" ta mike tana yafe gyalen ta kan daurin ture kaga tsiyar da tayi ta atamfar ta mai kyau dinkin riga da sket
"Ga wayar nan ki dauka ajakata ban san miye hadinki da usman ba wllh koh dai auren shi xakiyi" cewar fareeda murya da kyar
Daukar wayar tayi kan ta tabe bakinta "ni ina ni ina auren ya usman kin ganshi yanxu ne kuwa"
Duk da tana son jin toh ya yake ynxu amma bata tambaya ba "wllh baki ganshi ba ynxu ya xama alhaji har da mashin shagon ma an gyarata ynxu an xuba kaya"
Dan murmushi fareeda tayi"allah ya kara budi ya kuma bashi mata tagari" suka amsa da ameen har da mama
Fareeda bata koma gidan mami ba sai dare bayan sallar isha'i khady ta biyo mata
Washe gari wuraren karfe goma ya kai nadia airport xuna xaune xaman jiran agama boarding din ta
Ta kalleshi"meye sa baxamu je tare ba" "babe tafiyar nan taki ce ke daya it's a little bit of my appreciation to u game da duk kulawar da kk nuna min am greatful ynxu so nake ki je ki huta I promise next tare xamuyi vacation din"
Kafe shi tayi da idanunta "and ai kinsan bikin ahmad da khady nan da sati daya ne shiyasa I can't miss it "
Daga masa kai tayi "toh naji and congratulate dem 4 me inna dawo xanje na gaida su "
"Allah ya dawo min dake lfy my love uhmm" murmushi tayi ta mike "toh am going "
Shima mikewar yayi ya rakata har inda xata mika tickets dinta ta shiga jirgi sai daya ga tashin su kami ya bar airport din
Dayake yau biyun sallah basu je kasuwa ba gidan ahmad ya tafi horn yayi mai gadin ya bude masa ya shiga "barka da xuwa oga " cewar mai gadi
"Barka musa ya aikin dafatan anyi sallah lfy"
"Lfy lau oga" kudi sababbi ya mika masa ba shiri ya mika hannu yana washe baki ya amsa yana xuba godiya
Shi kuma deen ya shige ciki afalo ya sami ahmad din yana sanye da t-shirt da 3quater yana video a laptop dinsa
One sitter dake gefen inda ahmad din ya xauna shima ya xauna yana watsa masa harara "dear xan kiraki anjima ga yayanki ya shigo " cewar ahmad yana dariya
Sallama sukayi kan ya katse kiran "man ya daga ina haka"
Hararar shi deen yayi " kasan allah kar ka lalata mana yarinya "
"Lallai look who is talking kai da aka kawo maka yarinyar ai naga kallonta kk yi koh"
"Na dai fada ma ni yaushe xamu kd"
"Wllh ina son xuwa da wuri amma kamar ba xai yiwu ba so nake sai na gyara nan gaba daya ""Wai duka dama nan xaka dawo dasu"
"Toh ya xanyi hafsa ta dadde da son dawowa nan amma na ki kuma kaga baxai yiwu na dawo da ita nan ba amarya kuma a kd ba koh""Toh duk ka bar su anan mana "deen yafada cikin xolaya harara ahmad ya watsa masa har da jifansa da pillow "kai ai naga duk acan ka bar matan naka ai"
Dariya deen yayi "kai ni ba wannan ba don allah ka taimaka ka kira khady in tana tare da fareeda in ganta "
Kallonsa yayi "ban gane ba fareedar bata da waya ne "
"Tana dashi kiranta ne kawai baxanyi ba in baxaka kira ba toh kai ma shikenan " ya diba cin-cin ya kai bakinsa
"Allah dai ya shirye ka da wannan Jan ajin naka " ahmad ya ce yana kokarin kara kiran khady
Bugu biyu ta daga "baby yaya har ya tafi ne" cewar khady
"Ina fareeda ta jiyo muryar shi ba shiri ta jawo hijabi ta saka don riga da skit ne ajikinta sai dan kwalin data daura
"Uhmmm tana wanka ne bata fito ba "
Yana jin haka bai kuma cewa komai ba koma kan 3 seater ya yi kwanciyar sa shi kuma ahmad ya cigaba da soyayyar sa
Pls like comment and share
Don't 4get to tag d little star down der
Thank you
Mommah ❤️