24

44 1 0
                                    

Ba shiri na farka ina ture hannun dake shafa ni "wayene" na fada a tsorace sakamakon bbu hasken tocin da na bari a kunne kamin nayi bacci

"Zaks ku bita a hankali kun san nima ina bukatar ta koh" na jiyo muryar ummi

Dariya naji daya daga cikin su yayi ya kara jawoni da karfin gaske,dayan kuma ya ware kafafuwana yana cillar da zanin dake jikina

Hankalina in yayi dubu toh ya tashi ganin suna kokarin fin karfina

Tun ina rokansu ina kuka har na koma hawaye kawai ina ambaton allah na ina ji ina gani maza biyu da koh ganin fuskar su banyi ba suka min fyade

Suna gamawa ma ummi ta dora nata ni dai tun da na suma ban sake gane inda kai na yake ba

Sai dana farka na gan ni a gadon asibiti,Ibrahim na gani ya shigo dauke da kofi sai bakin leda

Xama yayi kan farar kujerar robar dake gefen gadon "sannu maryam ya jikin"

Bace komai ba sai kallon sa da nake "tashi ki daure ki sha rabonki da abinci yau kwana hudu kenan"

Kwana hudu yana nufin ina a suma kwana hudu sai yau na farka toh meke faruwa ne

"Kar ki ba kan ki wahalar tunani don ba xai taimakeki ba ki samu ki ci kiyi wanka sai muyi magana kinji" magana yake amma Sam yaki ya hada ido dani

Yunwar nakeji don haka na mike xauna na jingina da pilo ya mika min kofin da ledar biredi

Duk da bai min dadi abaki amma haka na daure na shanye na mika masa kofin

Nurse ya kiramin ta taimakamin na shiga bayi nayi wanka na fito ledar kayana da ban san wanda ya kawo min ba na bude na dau wata doguwar riga na sa na saka hijabi na xauna

Shuru har awa guda bbu Ibrahim kuma bbu wanda ya kara shigomin sai bayan sallar azahar Ibrahim ya shigo

Xama yayi ya kara min ya jiki kan ya soma magana "ina ne garinku maryam? koh kina da wanda xamu kira ya xo ya tafi da ke"

"Ban gane ba Ibrahim make faruwa ne,ina su ummi da mazan da suka,,,,," kuka ne yaci karfina na kasa karasa maganata

"Ki bar batun nan maryam su ummi sun gudu ke ma allah ne yayi xaki rayu don sai bayan kwana biyu aka gano ki a dakin kwance"

Kuka na fashe dashi"wllh fyade suka min Ibrahim su su uku"

"Bbu shaida bbu kuma halin da hukumar makaranta xata taimaka maki sakamakon ba a hostel waton karkashin su kk xama ba kiyi hkri ki koma gida in kinyi jinya sai ki dawo makaranta "

Kirkixa masa kai ta somayi"babana bai xai amsheni ba Ibrahim daman can ba da yawunsa na taho ba balle ynxu wllh kasheni xaiyi"

"Kar kice haka kowa da kaddarar sa fa maryam"

"Baka san babana bane wllh bama xan yi gigin komawa ba ahakan dai"

Shuru yayi kan can yace dani "toh wa xamu kira"

"Sai dai inna fati ita ce dai nasan xata saurare ni "

Sai danayi sati aka sallameni na koma dakin da bbu komai ciki ynxu sai kayana shima mai gidan yace dana kwashe xai xuba sababbin yan haya ne

Littafin da na adana nmbr inna fatu na dauka na ba wa Ibrahim nmbr don a kira ta bugu biyu ta daga ban iya na mata bayani ba sai Ibrahim wanda bai boye mata komai ba

Can naji yayi shuru yana ta saurarenta har ta gama kan naji yace "ina wuni baba" sai kuma ya kuma jima bai kara magana ba

"Xan sake kira baba kati na ya kare xan sa sai na kuma kiranka" shine abinda Ibrahim ya fada yana kallona

Kuka na somayi "kiyi shuru ni xanji da komai kinji maryam bara na je na dawo" bai jira cewata ba ya fice

To cut d story short
Ibrahim yace da babana shi ya yarda xai aureni babana kuma ya ce muje can mu karata amma kar na kuskura na dawo inda yake har mutanen garin mu su sanda abinda na aikata

Acewar shi ai daman barikin naje ba karatu ba,,bangaren yan uwan Ibrahim ma basu amince ba acewar su ba asan kowa nawa ba kuma ace yar boko ai kawai bariki na fito

Dani da Ibrahim mu ga wulakanci da tozarci amma duk da hakan Ibrahim ya dage sai ya aureni duk da yan uwansa basu amince dani ba

Don iyayen sa sun rasu tun yana dan saurayi,shi yayi komai da kansa ya aje ni a dakinsa na zauren gidan

Anan nayi rayuwa wanda bbu dadi amma bbu halin fita har muka koma kaduna da xama na haifi fareeda da nanah

Shiyasa ban yarda ba da xuwa wani gari karatu ba don ban yarda da tarbiyar dana ma yarana ba aa don ban san da wa'inda xasu hadu ba kamar ni dasu ummi da kuma Ibrahim

"Mama mama mama"cewar nanah "ya ya " mama ta amsa tana dawowa daga dogon tunanin data fada

"Nace xan bi su adda gidan mami anjima xan dawo "

"Toh ki dawo da wuri kin san ba ayi abincin dare ba koh"

"Tom xan dawo " ta fada ta na dauko hijabinta

"Mama sai gobe xan dawo mami tace na kwana anan"

"Ai da gskyar ta kuma ma ni ban yarda da wannan yawace yawa cen ba ki xauna gu daya"

Fareeda bata kuma cewa komai ba har nanah ta fito suka bar gidan

Deen
Tun yana sa ran ganin kiran salman amma shuru kk ji har la'asar sai daya fito daga sallah ya kira layin shi amma akashe

Rai abace ya katse wayar gashi bai son kiran gida ya tamabaya in sun iso don kar su yi zargin wani abu

Motarsa ya shiga ya wuce kasuwa don haduwa da ahmad.

Sai dare ya samu layin salman yana dagawa ya haushi da fada "ke baka da hankali har ynxu koh in ce ka kirani in kun isa amma don iskanci ka kashe waya"

"Kayi hkri yaya wallhi wayar ce ta dauke ina isa gida kuma na sa caji na dauka ma koh anty ta kiraka ne kunyi waya shiyasa ban ma sake niman ka ba" salman ya masa bayani
Bai kuma cewa komai ba ya aje wayar sa,ransa na kuna ya na kuma kara tsara irin hukuncin da xai wa fareeda

Nadia
Ba laifi ta canxa ba kamar da ba tun da taji abin ya koma gasa tsakanin ta da fareeda take duk abinda xata iya ta ci gasar waton deen kenan

Bata fita sai in a tare xasu fita,boutique din ta bari hannun babbar yarinyar ta ta shagon sai dai aturo mata recond da alert

Daman can tana da cameras a boutique din,,,wani sa 'in kuma deen da kan shi ke kai ta dan duba in komai lfy sai su dawo tare

Fareeda
Har aka soma azumin Ramadan amma shuru koh text din deen bata gani ba balle kira

Ta danyi kiba ta kara haske ga wani sheki da kyalli da skin dinta ke yi

Sosai mami da anty amarya suke lura da ita sakamakon alamomin mai ciki da take nunawa

Gashi kamar gara,haka xalika bata son kamshi sai bacci

Kullum sai yayi waya da su mami da anty amarya amma basu taba masa zancen cikin ba

wani sa'in ma tana kusa sai dai taji suna waya har sun kammala amma shuru baxai ce abata waya ba koh ya tambayi yaya take

Tun bai damunta har ya xo yana damunta,ga wani mugun kewarsa da bukatar sa da takeji

Wani sa'in cikin dare sai ta sha kukan ta ta gaji don ma ana azumi kuma da kuma zirga zirgan siyayyen bikin khady da xa ayi bayan sallah shi ke dan dauke mata hankali

Mommah ❤️
Like comment and share
Thank you

BIYAYYATA Where stories live. Discover now