27

46 3 0
                                    

ya tsaya shi bai yi gaba kuma shi bai yi baya ba "xanje tadi ne" ya bata amsa wuni malolon bakin ciki taji turnike makogaronta wanda sai da tayi ta kyar ta iya hadiye ta "tadi fa kace me hakan ke nufi" tafada tana kallon fuskar sa

Kauda fuskar sa yayi ya kuma ce da ita"yanda kk ji haka ne " "haka ma kace ace all dis months baka nimeni ba kuma ace daga xuwan ka kace min tadi xakaje ka kyau,,,," bata ida maganar ta ba ya katseta da fadin"look am running late I don't hv time for dis" bai jira cewarta ba ya wuce ya shiga motar sa ya bar layin

Ta jima anan bakin kofar atsaye kan ta share hawayen da suke ta mata barazanar fitowa tun sanda ya soma mata magana

Taci sa'ar bbu kowa falon sai sa ta wuce dakin su direct khady na xaune tana cin abinci "ga abincin ki nan kixo ki ci"

Koh inda take bata kalla ba"na koshi" ta haye kan gado tayi kwanciyarta

Khady bata kuma bi ta kanta ba taci gaba da cin abincin ta

Deen
Bakaramin tada masa da hankali tayi ba da ya ganta she looked different gaba daya ta canxa tayi alittle bit chubby ynxu sai haske da glowing da ta kara

Her smell everything felt different wani irin kamshin dake fita daga gareta yasa yaji haushin ta me taje yi awaje awannan lokacin ace kuma shi dayake mijinta ma ta gigitashi

Ina ga yan waje da suka gama ganinta kuma suka jiyo kamshin ta

Gaba daya kishin ta ya rufe masa ido har ya manta da wata xancen bata da lfy yasa ya mai da mata da tadi xaije

Fareeda
Bata san ta inda kishin sa ke bullowa ba amma ji take kamar yanda ake kunna fanfo haka aka kunna mata shi

Kwance take amma ta kasa bacci tunanin ynxu ya na xaune da wata kenan cikin motarsa tana kalleshi tsaf tana kuma sauraron daddaden kalamansa da muryarsa tun tana yi har bacci barawo ya sace ta 😑 😆

Washe gari tun da gari ya waye yan uwa na nesa da kusa suke ta shiga da fice a gidan masu girki na yi kowa nata hada hada don yau dinner xa ayi

Haka amarya khady da tawaganta suma ba a barsu a baya ba sun cika dakin su khady fam har bbu space

Ita koh amarya tafito wanka xata sa kaya su wuce studio kiki's glam ✨️ don kwalliya

"Dan allah ummi kar ku manta fa ku samin flat shoe don wllh inna gaji da high heel din nan cireta xan" cewar khady tana sanya t-shirt saman xanin data daura

"Ke kuwa ai xaki bata wankan wani flat shoe kuma" cewar ummi

"Ni dai kawai ki samin ajaka" "toh naji"
Kwankwasa kofar akayi aka bude kofar "ga abincin karin ku can an kammala kuxo ku dauka" cewar samira yarinyar kawar mami

Suka amsa da toh kan ta fice daya daga cikin yan matan dakin ta mike ta bi bayanta dan dauko abincin

Fareeda
Kwata² bbu abinda ke mata dadi tun daren jiyan tana kwance can kuriyar gadon ta dunkule gu daya duk hiran da ake a dakin tana ji amma fa bata cewa uffam

Deen
Xaune suke acikin falon boys quarters din dake gidan ahmad da abokanan su ana hira ana cin abinci

Ahmad ne ya fito  dakin ya samu wurin kan kujera ya xauna "ango kasha kamshi ya akayi ne" cewar wani abokinsu faisal

Ajiyar xuciya ahmad yayi kan yace "wllh sha'anin mata da wuya take nan fa hafsa ta nuna min farin cikin ta tare da min fatan alkhairi amma ynxu haka ace anata kirana wai tana can tana ta faman kuka"

Dariya hafiz da faisal sukayi banda deen da ke xauna kan cafet ya na latsa wayarsa abdul yace "ai haka suke kishin nan dai bai barin su wllh"

"Ni dai shawarana kabita ahankali don koh ba komai u guys hv been true alot 2geda kuma sonka ne ya jawo hakan" cewar faisal

BIYAYYATA Where stories live. Discover now